Skip to content

Chapter 41

Chapter 41

Abari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,211 words 0 views Progress saved
Download Book

su ce ta fita ba. Daga likitocin sai dattijon sai Habibu, wanda idanunshi suka kada suka yi jajur, zaka iya hango tsabar tashin hankalin da ke kwance cikinsu. Don ma yana dauriya ne, amma da fashewa zai yi da kuka. Cikin gaggawa kowannensu ke ba shi taimakon da zai iya. Masu jona abin janyo numfashi na yi, masu auna bugun zuciya na yi, da ya ja wata doguwar ajiyar zuciya su dukka suka kalli juna suka girgiza kai, sannan suka ci gaba da aikinsu cikin kwarewa da sanin makamar aiki. Kafin su cire 'odygen' din su yi wa Habibu da dattijon alamar su biyo su ofishinsu. Fitarsu ke da wuya leburori suka shiga dakin suka soma tsaftace wajen. Har zuwa wannan lokacin dattijuwar nan ba ta daina sallah ba. Ba ta daina kai goshinta gaban mahaliccinta ba, domin ta yi imanin Shi kadai ne zai tashi kafadar danta, amma ba wadannan tarkacen nasaran ba. A can ofishin Dr. Fredrick Engles (consultant) na bangaren zuciya, bayani yake musu dalla-dalla na bugun zuciyar ba-zata da 'patient' dinsu ya samu, wanda ya yi mugun yi wa zuciyarshi illa farat daya. Ciwon zuciya na lokaci daya ya yi mishi mugun kaye, wanda idan ba a yi gaggawar magance mishi damuwarshi ba, daga yanzu zuwa kowanne lokaci komai zai iya faruwa. Ya kare da tambayarsu, shin ko sun san hakikanin abin da ke damun mara lafiyan? Domin su sunyi-sunyi ya fada musu, amma ya ki cewa komai. A nan ne dattijon ya soma yi wa babban likitan bayanin duk abin da Amirun ya fada mishi ranar da ya dawo, kafin ciwon ya ci karfinshi. Wato kanwar Habibu yake so, ita kuma ta ce ba zata aure shi ba. Habibu kuma ya dubi likitan ya ce "Ni kuma na yi alkawarin zan aurawa Amiru Mairo, ko da a gobe ne, idan hakan shi ne zai zamo FANSA ga lafiyarshi. Ko da kuwa ace wannan shi ne abu na KARSHE da zan gabatar a rayuwata". Dattijon ya ce, "A'a Habibu, ba za a yi haka ba, a bi-ta a hankali, domin dai da na kowa ne, ban yarda a tursasata bisa abin da ba ta so ba". Dr. Fredrick ya ce "Yanzu ina yarinyar?" Habibu ya ce "Tana waje, sun zo tun dazu. Sai dai ba tasan abin da ke faruwa ba. Da kyar ma idan tasan Amirun ne kwance a gadon asibiti". Likitan ya ce "A kirawo ta". Habibu ya fita, jim kadan suka shigo tare da Mairo, duk da ranta a bace yake, amma ba zaka karanci hakan a fuskarta ba. Ta nemi kujera gefen Habibu ta zauna, kanta a sunkuye, Dr. Fredrick ya yiwa su Habibu alamar su fita, yana mai ci gaba da rubuce-rubucensa cikin 'file'. Ofishin ya rage daga shi sai Mairo, har zuwa lokacin bai gama rubutun da yake yi ba. Daga bisani ya dago, ta karkashin farin gilashinsa yake kare mata kallo. Cikin ranshi ya ce, Dole maza su kwanta ciwo. Ya yi gyaran murya, sannan ya yi murmushi, ya ce "Maryam". Ta dago a hankali ta dube shi cikin fararen idanunta ba tare da ta ce dashi komai ba. Ya mike zuwa dan karamin firij da ke gefenshi ya fiddo gorar ruwan (Faro) ya bincire murfin ya sha, ya maida robar. Maimakon ya koma mazauninshi, sai ya ja kujerar da ke fuskantarta ya zauna. Ya sake yin murmushi kafin ya sake kiran sunanta. Wannan karon kam ta amsa, ta ce "Na'am". Ya ce "Sunana Dr. Fredrick, ni ne likitan da ke kula da lafiyar iyalin ABDURRAHMAN GAYA. Ina so ki ba mu hadin kai mu ceto rai, wanda ke cikin halin ha'u'la'i akan soyayyarki. Shin za mu samu wannan taimakon Mairo?" Cikin murya mai sanyi ta ce "Ni Doctor?" Ya ce "Ke fa Maryam". "Ta ya ya zan taimaka?" "Ta hanyar tayamu jinya, har sai ya samu lafiyarshi, domin a halin yanzu ba ya bukatar komai Maryam, sai soyayyarki, sannan ne mu ma za mu samu namu aikin ya yi kyau. Mai zai hana ki yarda ki auri mai sonki Maryam? Har ya ke neman rasa kyakkyawar rayuwarshi a dalilinki?" Cike da matsanancin mamaki ta ce "wai wanene?" Yayi murmushi ya ce "Taso mu je". Dr. Fredrick ne a gaba, Mairo na biye da shi. Ya tura kofar dakin dazu ya shiga, ita ma ta sa kai. Dakin babu kowa, sai mara lafiyan, wanda ke barci sadidan. Sai dai fa da ganin irin barcin da yake yi kasan ba na Allah da Annabi ba ne, na karfin allurai ne. Ba karamin bugawa zuciyarta ta yi ba (kamar wancan lokacin da ta fara ganinsa) a lokacin da ta sake yin arba, da dan Abdurrahman Gaya. Sai dai fa wannan Amirun ya sha ban-ban da wanda ta gani satittikan da suka gabata, ma'abocin kuzari da koshin lafiya, hadi da wasu nasibobi da ba duk maza Allah Ya mallakawa ba. Wannan Amirun ya rame fiye da tunaninta, sannan ga dukkan alamu ba karamin jin jiki yake yi ba. Ta tsaya jikin gadon kawai ba ta ce komai ba, sai dai zaka iya karantar karyewar da zuciyarta ta yi, hadi da tausayi tsantsa, da shi ma ya bayyana bisa kyakkyawar fuskarta. Tambaya ta ke cikin ranta, ita kuwa wace ce da Amiru zai kwanta ciwo a dalilinta? Kamar an ce da shi bude idonka, a hankali ya ke bude idonshi a kanta. To ita ma din kallonshi ta ke, sai ya dauka ko mafarki ne da gizon da ta ke mishi dare da rana, don haka ya dauke kanshi daga kanta, don bai gasgata idanunshi ba. Ya mayar da su kan Dr. Fredrick, wanda ke ta murmushi. Shi kam al'ummar Hausa suna ba shi mamaki akan soyayya, shi wallahi har duniya ta nade, bai ga macen da zata kwantar da shi a gadon asibiti ba. Balle mutun irin Amiru, dan gata gaba da baya, wanda duk irin macen da yake so a duniya zai iya aura. Ganin abinnasu yake kamar irin a fina-finan India. Ya kama hannun Amirun yana murmushi, ya ce "Kana da bakuwa fa? Wadda tayo tattaki tun daga U.S domin ta duba jikin ka!" Bai juya ya kara kallon Mairon ba, wadda ganinta ya kara haifar mishi da faduwar gaba. Kirjinshi in banda bugawa ba abin da yakeyi. Zuwa yanzu ya yarda ita din ce, ba gizo idanun shi ke mishi ba. Likita ya kama hannun Mairo ya dora mishi kan kirjinshi, dai-dai santar zuciyarshi. Tana jin yadda zuciyarshi ke bugawa fat-fat-fat! Amma don karfin hali bai fasa magana ba cikin nishi. "Ba wajena ta zo ba, ta biyo bayan Yayanta ne". Mace mai rauni da saurin karaya, sai ta soma kuka. Tun fil'azal Mairo mace ce mai tausayi, abin kuka bai da wuya a gurinta, bare an ce a dalilinta ne Amir ya kamu da ciwon zuciya. Wato wannan ne dalilin Habibu na yanke mata karatunta, Allah sarki Yaya Habibu, a da har ta kullace shi tayi fushi dashi mai tsanani. Ban da abinsu ita wace ce? Da kasancewarta tare da shi zai sa ya samu sauki? Likita ya daga mata gira, ya rausayar da kai, ta gane yana lallaminta ne ta rarrashi Amiru. Ta janye hannunta daga kirjinshi, cikin sassanyar murya ta ce "Ni na fada maka cewa

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66