Skip to content

Chapter 1

Chapter 1

Abari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

© *Sumayyah Takori* Litinin babbar rana, ko bature yana tsoronki. Habibu ya yi shirin ofis cikin _suit_ din ma'aikatan bankin _Barclays_ , da jibgegiyar rigar sanyi, hand-socks da leg-socks, yana so zai fita aiki. ga yara sunyi shirin makaranta tsaf, misalin karfe bakwai daidai na safe. amma babu hanya, domin kuwa tashi sukayi suka tarar kankara ta rufe kofar gidan ruf, da tagogi bakidaya. Dina ma ta fito cikin nata shirin cikin kayanta na lauyoyin banki, tana ta korafi akan 'snow'. Dole Habibu ya fiddo waya ya kira ma'aikatan sare kankara, nan da nan suka zo cikin minti goma, suka bambare kankarar sannan suka samu hanya suka fita. Mairo ta fito daga dakinta ta yiwa sanyi mugun shiri, baka ganin komai nata sai shacin kayatacciyar fuskarta kai ka ce balarabiyar *Morocco* ce. Tasa yaran a gaba suka fito tana dauke da little Mairo, suka zo bakin hanya suka tsaya tana rike da hannayensu, tsayuwar minti biyar sukayi motar makarantar su ta iso ta sanya su ciki suka tafi, suna daga mata hannu itama tana daga musu. Kasancewar ita bata da karatu a yau sai ta kama hanya cikin nutsuwa ta koma gida. ( _Wannan shine tsarin rayuwar gidan Yaya Habibu a kullum. Duk wayewar gari kowa abinda yake yi kenan)._ Mairo na karantar Zamantakewar Dan adam (Sociology ) a jami'ar Michigan (Michigan State University) tun bayan dawowar ta gidan Yayanta Habibu. A yammacin ranar tana zaune a _study-room_ da farin gilashin karatu a idanunta tana nazarin littafin 'Haralarambus and Holborn ( _Sociology_ , _Themes and Perspectives_ ) domin wani assignment (aikin gida) mai matukar wuya da aka basu akan *hedonism* zasuyi _submitting_ a washegari. Aunty Dina ta murda kofar ta shigo fuskarta dauke da murmushi, sassanyan kamshin ta na turaren (yves saint laurent) shi ya fara bakuntar hancin Mairo kamar koyaushe, Dina mace ce mai darajja kamshi a jikinta ta dade da sanin wannan. Ta ja kujerar dake fuskantar Mairon ta zauna sannan tace "Mairo dan rakiya nake nema, London zan je gobe ko zan samu ki raka ni?"Mairo ta shiga girgiza kai da sauri "inada aiki mai yawa a makaranta goben, kuma zanyi submitting assignment dina, me zaki je kiyi?" Ta ce "kallon 'film-fare award' na wannan shekarar, gara in gani _vivid_ fiyeda a talabijin nafi gane komai. Tun wancan satin ake ta sanarwa za'ayi". Mairo bata san kallon Indian na Aunty Dina ya kai matsayin haka ba, da zata ni ki gari kasa-ya-kasa tun daga birnin Michigan har babban birnin Birtaniya don kawai ta ga GALA! Da sauri tace "sai kin dawo. Ni kam, bazan samu zuwa ba". Habibu da taya bera bari ya yankowa Dina tiket ta tashi a washegari, gidan ya saura sai su kadai. Tun safe Mairo na makaranta tana fama da ayyukan gaban ta itada kawarta Ir'eesh Tawheedah 'yar asalin kasar Somalia. Bata dawo gida ba sai yamma lis, ta tarar tuni Yaya Habibu ya riga ta dawowa. Zaune suke a falon shi shida yaran suna aikin makaranta yana nuna musu. Mairo tayi sallama ta shigo suka yi tsalle suka daneta suna yi mata "oyoyo". Yaya Habibu ya daga ido ya kalle ta yana mamaki cikin ransa wai wannan Mairo ce, MAIRON GURIN-GAWA, MAIRON-HURE! Abu daya ya tuno a wannsn lokacin yayi murmushi (goruba daga kan bishiya a kauyen GURIN-GAWA) ya ce "Mairo 'yan makaranta.... Mairon Dina. ... Mairon Yaya Habibu...!" Ta yi dariya har fararen jerarrun hakoranta suka fito. Kirarin da yake mata kenan idan ya so nishadi. Ta wuce dakinta rungume da jakarta don ta kimtsa. Bayan tayi sallar magriba tayi wanka ta canza kayan jikinta ta fito falon ta zauna tare dasu. Zuwa can Yaya Habibu ya fito daga dakinsa cikin shiri, sai kamshi yake. Ga dukkan alamu cikin sauri yake. Ya dube tayace "maza a shirya dinner, amma _African-Dish_ . Inada babban bako anjima kadan. Babban abokina Amiru zai sauka yanzunnan daga Washington D.C zan je filin jirgi na dauko shi". Yadda yake maganar cikin rawar jiki kadai zaka fahimci wannan bakon mai muhimmanci ne da matsayi na musamman a gareshi. Ba tun yau ba Mairo na jin sunan Amiru a bakin Yaya Habibu da Dina. Zata iya cewa rana bata fitowa ta fadi wani cikinsu bai ambaci Amiru ba. Ta amsa da ladabi "toh, sai kun iso". Yana fita ta mike ta nufi kicin, Lynder na goge-goge ta bata hanya ta wuce, ta bude _deep-freezer_ tana tunanin me zata dafa musu? Daga bisani zuciyarta ta tsaya akan tuwon shinkafa miyar danyar kubewa tunda dai suna da Okora (danyar kubewar gwangwani). Nan da nan ta dora sanwa, tayi amfani da _dried fish_ da _mushroom curry_ cikin miyar, duk kicin din sai ya dau kamshi. Sunada zobo, don haka ta tafasa shi ta tace, ta markada abarba ta hade da zobon da fulebo din abarba ta juye a _jug_ ta sanya a firji don ya yi dan sanyi ba tareda ta sanya sukari ba. Ba tun yau ba ta san Yaya Habibu da son Danwanke, kai shi duk wani abinci ma na Africa to ya bi bayan dan wake. Don haka nan da nan ta jika kanwa ta kwaba ta jejjefa cikin tafashashshen ruwan zafi, cikin dan lokaci ta kammala komai. ****** Ta kashe wayar ba tareda ta baiwa Nabilah amsa ba. Jikinta a sanyaye matuka, maganganun Nabilah kullum irin na Anty Dina ne, ko maiyasa? Alhalin basu san juna ba, basu taba ganin juna ba ko a hoto, balle tace sun hada baki ne suna _sharing idea_ don su kalubalanceta! Dai-dai lokacin taji shigowar Yaya Habibu da bakonsa. Da alama ba su biyu bane don tana jin muryoyin maza daban daban. Ta sake kudundunewa a cikin bargonta sama-sama take jiyo tashin muryarsu anata turanci kamar tashin duniya. Kira ya shigo wayarta, daga kwance ta mika hannu ta amsa a kasalance. Dina ce. Tace "yaya kuke Mairo? _Hope_ ba matsala, ina nan tahowa gobe insha Allah, mai zan sayo miki?" Mairo ta ce "munyi kewarki ne kawai Anty, duk gidan ba dadi da baki. Bana bukatar komai sai dawowar ki lafiya". "Nima haka Mairo, ji na nake kamar nayi shekara ban ganku ba. Me ya samu wayar Habib ne? Na kasa kama shi". Tace "yana falo, yayi baki ne". "Su waye?" Mairo ta ce "Na dai ji yace Amiru ne" Dina tace "wow! Amiru yau a gidanmu? Maza kaiwa Habib wayar inason magana da shi". Ta mike rike da wayar ta fita, shaf ta manta ko kanta bata rufe ba tsabar yadda Dina ta matsu tayi magana da mijin nata, a haka ta isa falon. Ta karasa kusa da Habibu ta mika masa wayar. Juyowar nan da zatayi sai idonta cikin na Amiru, wanda ke zaune gefen Habib cikin _Italian Suit_ bakake wul, ya sassautama wuyanshi ruwan tokar _tie_ dake jikinshi. Suka samu kansu cikin matsananciyar faduwar gaba a lokaci guda. Ga ita Mairo, kwarjini ne da kyawun Amirun ya haifar mata da faduwar gaban. Amma ga AMIRUN, bazan iya cewa ba! Habibu yace "Amiru *meet my beloved sister MAIRO* , da nake baka labari...". Yana mai kokarin saita lumsassun idanunsa akan Habibun, don kawar dasu daga nacewar da sukayi akan Mairon yace "itace Mairon??? Mairo zo mu gaisa....". Amiru dai Hausa yayi, amma wani _accent_ ne da Mairo bata taba

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66