Skip to content

Chapter 26

Chapter 26

Abari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

bana son kinbibi da son nuna iyawa, waye ba ya amai idan ya ci abin da ranshi bai so ba? Wuce da Allah ki ba ni waje, ke kuma ungo goro ki ci tashin zuciyar zai lafa". Mairo ta koma daki tana jinjina hali irin na Habiba. Karfe biyar na yamma ta ji karar motar Baffa tabbacin ya dawo. Sai da ta ba shi lokaci ya kimtsa sannan ta je dakinsa, ta same shi yana cin abinci ga Hajara da autarta Umma a gefe, ban da harararta ba abin da Hajara ke yi, amma ita ba ta kula ba, tsugunnawa ta yi har kasa ta gaida Baffan, ya amsa cikin walwala, ya ce "Yaya dai Mairo, babu wata matsala ince ko?" Kanta a kasa ta ce "Babu Baffa, ina so in je Galadanchi ne". Bai tambayi wajen wanda zata ba, ya dauko naira dari biyu a aljihunsa ya mika mata, ya ce "Ga shi ayi kudin mota, amma kada ki bari dare ya riske ki waje". Ta ce "Insha Allahu Baffa". Mairo tana tafe tana tunanin rigima irin tata, ya za a yi ta nemi gidansu Uncle alhalin ba tasan komi a kanshi ba? Ace ma ta sani, me zata je ta ce, kuma me zata je ta yi? Wata zuciyar ta ce "Gaida mahaifiyarsa kamar yadda yake gaida naki". Wannan tunani ne mai kyau. Ta fito daga Yakasai zuwa Bakin Rimi, ta tari tasi ta ce "Galadanchi". Ya bude mata kofa ta shiga. Ba a fi minti goma ba ya sauke ta a unguwar Galadanchi. Ta fito ta ba shi dari biyun Baffa ya ba ta canji, ta gangara dai-dai makarantar gidan Galadima ta tsaya nan tana rarraba ido, ta rasa wanda zata tambaya. Daga can gefe wajen masallaci dandazon matasa ne a zaune suna haramar shiga sallar magriba, ba zata iya shiga cikin wadannan samarin ba don haka ta ci gaba da tsayuwa cikin rashin sanin abin yi. Tana nan tsaye wani saurayi ya zo gittawa ta gabanta ta yi mishi sallama, ya juyo ya amsa, ta ce "Don Allah Yayana tambaya nake". Ya ce "Allah Ya sa na sani kanwata". Ta ce "Gidan su Junaid nake tambaya". Ya ce "Junaid? Ya ya sunan maigidan?" "Gaskiya ban sani ba". "Babba ne ko yaro ne?" "Babba ne, don zai girme ka". Ya yi dan tunani "Kwatanta min shi". Nan ta shiga kwatanta mishi, ya ce "Ke ko gidan Justice Atiku kike tambaya?" Kwarai ta taba jin sunan Chief Justice Atiku Galadanchi a bakin Kausar mai rasuwa, (Alkalin-alkalai) na Jihar Kano. Ta ce "Ina jin nan ne". Ya ce "Mu je na nuna miki". Abinka da karamar unguwa, kowa yasan kowa. Ya yi mata nuni da gida ginin manyan 'yan bokon da, mai malalen suminti, dakali biyu sun sa gidan a tsakiya, ko ina a share tas ko tsinke babu. Ta yi wa saurayin godiya ta sa kai zauren gidan. Ashe yadda wajen yake ba haka cikin gidan yake ba, cikin gidan gini ne sosai na zamani, mai ban al'ajabi, sabida yadda aka kwalmada karfe da rodi aka yi irin wannan ginin ba kasafai ake samun irinshi cikin Nijeriya ba. Ko'ina gilashi sai daukar ido yake hatta kofar shiga falon gidan ta gilashi ce. Ta tsaya a kofar falon tana sallama. Wata dattijuwa da alama mai aiki ce, ta fito tana mata kallon rashin sani. Mairo ta tsugunna ta gaishe ta, ta amsa, ta ce "Yammata wa kike nema?" Ta ce "Babar su Ilham". Ta bude mata kofar falon, ta ce "Zauna a nan, Hajiya tana zuwa yanzu". Ba ta zauna a kujerar ba, a kan wani tattausan kilishi da ke tsakiyar dakin ta zauna. Talabijin na ta aiki cikin tasoshin tauraron dan Adam. In banda kamshin turaren wuta na (Bakhour) ba abin da ke tashi a falon, gauraye da ni'imtaccen sanyin na'urar sanyaya daki duk da sanyin da ake fama da shi kuwa. Ta daga kai a hankali zuwa gabas maso kudu na dakin. Tangamemen hoton Uncle Junaidu ya yi mata sallama, yana murmushi. Wata matsananciyar faduwar gaba ta same ta, ta kura mishi ido ba ta ko kyaftawa. Dai-dai lokacin da ta ji muryar Hajiyar tana yi mata sallama. Ta daga kai ta kai dubanta ga mahaifiyar Uncle Junaidu. Nan ta ga inda Junaid ya debo kyau, tsurarsa. Mace ce ma'abociyar zati da kamala gami da gogayya cikin zuzzurfan ilmin boko. A idanunta farin gilashi ne (medicated). A kiyasce zata yi shekaru hamsin. Amma a idaniyarka ba zata fi shekaru talatin da biyar ba. Ta zauna a kujera fuska cike da annuri, Mairo ta duka tana gayas da ita. Ta amsa cikin murmushi ta ce, "Yammata daga ina? Ban gane ki ba". Itama Mairon sai ta rasa abin da zata ce. Wata zuciyar ta ce "Akul! Kika ce danta kika zo nema, wannan ba mutumcin diya mace ba ne. Kin zo ki gaishe ta ne sabida Allah, da kuma soyayyar danta da Allah Ya dasa miki. Amma ba don kamun kafar neman soyayyar ba". Hajiyar ta sa mata ido tana nazarinta, ta rasa inda ta san fuskar. Haka kawai Allah Ya sanya mata kaunar yarinyar a zuciyarta. Duk inda ake neman kyau da nutsuwa, haiba da kamala to wannan yarinyar ta zarce, ga shi da alamunta ilmi ya ratsata ta ko ina. Amma shirun da ta yi mata ya sanya ta diga mata ayar tambaya (kuestion mark?). Ta sake maimaita mata tambayarta "Yammata daga ina kike ban gane ki ba?" A sannan ne Mairo ta cira kai, wasu irin fararen idanu, gauraye da wani irin blue-blue suka haske Hajiyar, ta yi wa Allah sarkin halitta tazbihi, ta tsarkake Shi, ta tsarkake iko da iyawarSa. Cikin sassanyan sautinta ta ce "Na zo wurin Ilham ne". Ta ce "Ke kawarta ce halan? Don na ga kamar nasan fuskarki". Ta ce "Eh". A takaice. Ta ce "To amma kuwa na yi mamaki da ba ta kawo miki katin bikinta ba, an yi bikinta watanni uku da suka wuce. Suna zaune a Wales din kasar Ingila inda mijinta ke karatu". Mairo ta ce "Allah Sarki, Allah Ya yi ba zamu hadu ba". Ta sake juyawa ta dubi hoton Uncle. Ta sake juyowa ta dubi mahaifiyarsa, wata irin soyayya da kauna na sake mamayar zuciyarta. Ba ta ki ta zauna a nan tare da Hajiyar Junaidu ba, tana yi mata bauta, har karshen rayuwarta koda Junaid ba zai aure ta ba. Wannan ita ce kauna ta hakika, wadda ba a samunta a wannan zamanin. Da gaske Junaid ya yi mata nisan da ba tasan ranar da zata kamo shi ba. Tsigar jikinta ya tashi, ganinta ya dushe, wani duhu ya gilma mata ta daina ganin abin da ke gabanta na wucin gadi. Hajiyar ba ta lura ba, don a lokacin hankalinta ya tafi ga amsa kiran wayar da ya shigo mata yanzu-yanzu. Ta mike tana gyara lullubinta ayayinda ta fuskanci da Uncle Hajiyar ke magana. Hajiyar ta yi mata alama da hannu ta jirayeta. Sai da ta gama wayar ta ajiyeta akan centre table, ta ce da Mairo "dan jiraye ni ina zuwa". Ta koma matattakalar da ta fito, jim kadan ta dawo da leda mai tambarin shagon country mall ta mika mata. Mairo ta girgiza kai alamar ba zata karba ba, don

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66