Chapter 66
Chapter 66
watanni biyu dan Pretoria. Bayan sun dawo ta nemi chanjin wajen aiki zuwa jami’ar Abuja, ba da son ranta ba, sai don ta samu kasancewa full-time da mijin ta. Abin son ta. Uban ‘ya’yanta kuma abin kaunarta; Dan Abdurrahman Gaya. A shekarar ne kuma akayi bikin kaddamar da Amiru Abdurrahman matsayin gwamnan CBN, bayan gwamna mai ci a lokacin yayi ritaya. Ba don shekarun shi sun kai ba, sai don kwarewa da sanin makamar aiki da dimbin tagomashin cigaba da ya kawowa Central Bank of Nigeria a matsayinsa na tsohon ma’aikacin World Bank. Shima Uncle Junaidu ya samu ‘promotion’ zuwa ‘chancellor’ na jami’ar Bayero bakidaya. Zumunci da aminci bai taba yankewa tsakanin su ba. Shekara na zagayowa Mairo ta direwa Hajiyar Amiru wani saitin 'twins' din data zabi a bawa sunan (Ilham da Sagir) kannen Uncle, don bazata taba mantawa da kaunar da Ilham ta nuna mata ba. Uncle yaji dadi kwarai kuma ya kawo Ilham daga Wales don kawai taga takwararta. Farin cikin Hajiya Aisha abin ba a cewa komai. Dina ma ta sake samun Hurairah (Hure) bayan fidda rai. Amina ta samu Atiku, Ikhlas ma matar Uncle ta sake haihuwa. To haka Nabilah duka hayayyafa suke kamar kaji, sai mu ce Allah Ya raya, kuma Allah Ya kara dankon zumunci. MASHA ALLAHU LA-KUWWATA ILLA BILLAH... Maman Safah da Marwah ce....ke cewa. Sai mun hadu a sabon littafin YAKANAH cikin yardar Maiduka. Dandano Daga Yakanah Karfe goma sha dayan dare garin kano yayi tsit, sai iskar hunturu dake kadawa. Malam Ja’afar ya dauko tabarmar sa ya shigo cikin gida daga soron kofar gida. Zai gitta ta dakin Fati ya jiyo sheshshekar kukanta. Ya dakata, ya dago labulen yana kallonta. Tana zaune akan darduma ta kunshe fuskarta cikin hijabi sai kuka take. ya karashe shigowa cikin dakin yace “Fadimatu kukan me kike yi? A razane ta cira kai ta dube shi idanunta jawur sun yi luhu-luhu alamar tayi kuka har ta gode Allah. Malam Ja’afar ya zauna a wata ‘yar kujera dake dakin yana fuskantar diyarsa. Ta share idonta da hankici, ta ja shashsheka kafin tace “Baba babu komai” ya jima yana kallonta sannan yayi murmushi yace “kina tuhumar mu dayi miki auren da baki so, auren mijin ‘yar uwar ki. Ki yi hakuri, alheri muke nufin ku da shi, ba zaki gane ba sai nan gaba. Idan kun gano gatan da muka yiwa rayuwarku” Fati tayi shiru tana sauraron babansu. Taga wannan itace damarta ta karshe. Daga gobe za’a zarga mata igiyoyin wanda baya sonta. Ta kai kanta kasa tana kuka sosai tace “ku yi min alfarma Baba. Baba baka taba sa ni in yi wani abu na shallake maganarka ba. Amma a wannan karon ina so ka dubi hujjoji na. Baba. Dr Sulaiman baya so na, baba Dr. Sulaiman yafi karfi na. bani da ilimin da zan jera da shi a matsayin matarsa. Baba sulaiman bazai taba son wata ba bayan son da yake yiwa yaya Hadiza. Baba kune baku sani ba, amma Dr. sulaiman ya tsaneni ban san laifin da nayi masa ba. Ban taba gaishe shi ya amsa ba, haka bai taba kallona a matsayini jinin Hadiza ba balle yayi la’akari da wannan ya kaunace ni. In dai don ‘ya’yanshi ne, ai nima ‘ya’yana ne…zan cigaba da rike su ba sai na zama matarsa ba……” Ya ce “Amma zaki zama matar wani ko? Kuma babu wanda zai aureki da zugar ‘ya’yan yayar ki. naji hujjojin ki Fati, amma nima ina so in tambayeki “wane abu ne Hadiza take da shi wanda ya kaita ga matakin zama matar Babban likita irin Sulaiman???? Tana ‘yar talakawa kamar ki??? Mu biyo Fati da Babanta a littafin YAKANAH yana zuwa bada jimawa ba!!!! __________-_TAKORI
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66