Chapter 2
Chapter 2
jin mai gardinsa cikin kunnuwanta ba. Kamar yadda bata taba ganin mutum mai kyau da kwarjininsa ba, ilhamomin dake tare da shi bata taba haduwa da mai irin su ba! Wannan shine AMIRUN Yaya HABIBUN??? ( _The beginning of everything_ kenan) ***** Mairo data koma daki kwanciya tayi rigingine cikin nadama. Kai tsaye ka dubi kwayar idon mutum mai kima kamar Amiru, kace baka sonsa ai ya zama wulakanci da cin fuska. To amma ita a ganinta daidai tayi, don bata iya karya ko yaudara ba. Amma dai duk da haka ta san bata kyauta ba. Saidai a ganinta gara hakan, da dai tayi irin auren da zuciyarta ta raya mata akansa. Dina tayi sallama ta shigo tana fadin "tashi, abincin da kike gudu ne na biyo ki da shi. In dai Amiru ya dade da barin gidannan. Ta tashi ta zauna sosai ta karbi farantin ta soma ci. Dina na kallonta, can kuma tace "Mairo me kika ce da Amiru ne? Ya shigo cikin walwalarsa, ya fita a yanayin da bamu taba ganinsa a ciki ba. Ina laifin wanda ke son ka?". Ta cira kai daga cin abincin tamkar wadda aka katse wa gudun jini a cikin jikinta, sai kuma ta sunkuyar. Can kuma ta dago ta dube ta tace. "Yana magana ne kan wai yana so na, so kuma na aure, yana burin na zama uwar iyalinsa. Nikuma na gaya masa kai tsaye cewa "bana son sa!". Dina tayi murmushi, daga jin kalaman Mairo da yanayin maganarta kasan kuruciya na dawainiya da ita. Cikin sanyin murya tace "sabida me ba kya son nashi Mairo? Gashi kyakkyawa son kowa kin wanda bai samu ba, gashi da dimbin ilmi kamar Yaya Habibun da kike cewa yana burge ki. Yanada matarshi baturiya zallah amma ya tsallakota yazo yace ke Mairo yana son ki. Zai iya rabuwa da ita saboda ya aureki. Gashi da kirki ga addini, ke kuwa Mairo me kike nema a da namiji da ya wuce wannan?" Sai Mairo tasa kuka, ta kwantar da kai a cinyoyin Dina, ta shiga kuka mai tsuma zuciya. "Na kasa mance *Uncle Junaidu* ne Anty Dina! Na kasa mance dimbin alherin da yayimin a rayuwa. Shine tsanin duk wani matsayi da matakin dana ke kai a yau. Idan na auri wani ba shi ba na ci amanar sa.......!" Dina ta katseta "akwai hanyoyi da yawa da zaka sakawa mutum Alherin da yayi maka ba dole sai ta hanyar aure ba. Misali shine ki dinga bin shi da kyakkyawar addu'a ba tareda shi din ya sani ba. Wannan addu'ar Ubangiji yayi alkawarin karbar ta Mairo. Kada ki yi mamaki zuwa yanzu shi Junaidun ya samu wadda yake so ya aura ya manta da ke. Ni na kasa gane kan wannan soyayya da kike yiwa Junaid maras dalili. Kin ce bai taba cewa yana son ki ba! Kince ba kuyi alkawarin aure ba! Kince ya san gidan Baffa amma bai nemeki ba! To Mairo gaya min wace hujja gareki da zata tabbatar da cewa yana son ki? Bakisan akwai masu taimako sabida Allah ba? Ba don a aure su ko a saka musu da soyayya ba? Haba Mairo, kiyi tunani mana, kiyi amfani da hankalinki, ki so mai son ki a zahiri da badini. Kiyi aure saboda Allah da raya sunnar Ma'aiki amma ba don abinda zuciyarki ta afu a kai ba. Ina tabbatar miki Amiru in kin nutsu, kin bude zuciyarki a hankali zaki so shi wallahi har ma fiyeda son da kike ma Junaid. Iyakar soyayya ta gaskiya kin yiwa Junaid, ko baki aure shi ba Allah ya shaida! Yayi alkawarin sanya masoyan gaskiya da suka mutu ba tareda sun auri juna ba a gidan aljannah. Ina tunanin Junaid yayi abin nan ne da hausawa ke cewa ABARI YA HUCE SHI KE KAWO DA RABON WANI!" Ta dubi Dina da sauri har tsakiyar idanunta tace. "Idan hakane Aunty Dina, kema kin yarda Uncle Junaid yana so na, furtawa ne baiyi ba kamar yadda _Inna ta_ da Nabilah ke cewa???" Gyada kai Dina ta yi. "EH, yana son ki, amma ya bari YA HUCE! Don kuwa a zahiri babu wata mu'amala ta mutunci da tausayi tsakanin mace da namiji sai 'SOYAYYAH'. In ma mutuncin ne da farko, to daga baya rikidewa yake ya koma soyayya. ... Ke dinnan Mairo har wata soyayya kika sani ko halarci? Wallahi HALACCI kike yimawa ba soyayya ba. Amirun shi kike so da gaske; na gani a kwayar idon ki, na gani a gangar jikinki. Kina jin abubuwan da kike ji kan Amiru a Uncle Junaidun? Kina neman Junaid ya aureki ne don ya tallafi rayuwarki a wancan lokacin da kike neman matallafi ido rufe, amma ba don kinsan hakikanin me aure ya kunsa ba. Mairo kinaso ki ramawa Junaid halaccin da yayi miki ne ta hanyar 'aure' don da shi kika saba, ya sanki, kin san shi, a tunanin ki wannan shine karshen soyayya, to ba shi bane! Soyayyar aure daban take, Allah ke hada ta, kuma bata fassaruwa. Ita zuciya an halicce ta ne da son mai kyautata mata, wannan shine tsakaninki da Junaid ba soyayyar aure ba! Idan kuma mata sun fara zuwa neman aure ne to sai muyi shirin tafiya Kano, unguwar Galadanchi gidansu Uncle Junaidu, mu nemeshi mu kai kudin aure... mu gaya masa yadda kike son shi, har kina duban tsakiyar idanun masu son ki da aure na hakika kina gaya musu ba kya son su. ......sabida kawai kada ki ci amanar soyayyar shi da ya baki a makaranta. ......" . Ala dole ta murmusa, ta san _zambo_ ne Dina take mata. Duka wannan bata lokacin da yawan bakin da Dina ta share tana bayani, ba duka abinda tace ne Mairo ta yarda dasu ba. Ta dauki Dina a matsayin mai campaign ga AMEERU! Sabida shi ta sani, shine mai irin tsarin rayuwar su. Bata san komsi game da rayuwarta ta baya ba, batasan wanene Uncle Junaid a rayuwarta ba. Ita kudin Yaya Habibu ma tsoro yake bata balle na Amirun da ta ji suna cewa yana _World Bank_ karewar _Barclays_ . A karkashin inuwarsa rayuwar Habibu ta ginu bakidayanta. Shi ya maida Yaya Habibu ko me yake a yanzu. Ta yarda ta hakura da Uncle Junaidu sabida hujjoji kwarara da kowa yake gaya mata. Hatta Nabilah tace da ita "lokaci yayi da zata manta da Uncle Junaidu tayi aure". Ta dubi irin auren da ita tayi, amma daga baya ya zame mata ALHERI. Don yanzu ba abinda take so a duniya sama da Ismael kuma shima hakan har ga albarkar haihuwa. Ta sauke ajiyar zuciya ta koma ta kwanta bayan fitar Dina. Ta ja bargo har kanta ta kudunduna. Bacci take so ta yi amma ya ki zuwa. Al’amuran na neman tarwatsa mata kwakwalwa tareda wargaza mata tunani bakidaya. Tana so ta yarda da Dina, halaccin dake zuciyarta na karyata Dina. Amma abubuwan da ta zano ai duk haka suke; zata je neman auren Uncle Junaidu ne??? Ko kuwa haka zata kare a zaman jiran *tsammanin warabbuka* ??? Zata iya cigaba da zaman jiran ranar da uncle Junaid zai nemeta, ya bayyana mata soyayyarshi, ya bata uzurin da ya hana shi yin hakan a lokacin da ya dace daga nan har gaban
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66