Chapter 56
Chapter 56
zan auri mai so na. Daman kuma babu iddarshi a kaina”. Daddy ya sake jinjina kalamanta, yayi mata godiya ya sallameta ta fita ta koma wurin Amiru. Inda aka baro su shida Habibu. Daddy ya dubi Hajiya cikin wani irin fushi da ‘anger’ da bata taba gani daga gareshi ba. Fuskar shi tayi jawur abinki da bafulatani, jijiyoyin kansa sun fito rada-rada, idanunshi sun canza launi daga farare sol zuwa jajaye. Jikinshi na tsuma, tsigar jikinshi na tashi yace “A’isha! Hanan gaskiya ta fadi ko karya ne?” Ta juya kai cikin tsoro da tashin hankali, nadama da yin kaico da kai, don bata taba ganin shi cikin wannan halin ba. Tace “batayi karya ba anyi haka. Sai dai kuskure ne da ajizanci irin na kowanne dan adam. Na tuba Alhaji na bi Allah na bika. Sai dai komai ya faru ne da zuga da taimakon wadannan……….” Tana nuna Nina, Ni’ima da Khalisa. “Su suke karbo komi a Lagos wallahi ban taba zuwa ba. Don nasan zuwa wajen irin wadannan mutanen haramun ne. Na roke ka, kada ka bari Habibu yaji wannan magana don GIRMA NA ZAI FADI A IDANUN SA don ba iyakarta kenan ba…….” Cikin nishi Alh. Abdurrahman yace “sai kuma me?” Ta yarfe hawaye da majina tace “Na sanya shi ya janye hannun jarinsa daga bankinsu shida Habibu……duk takardun dukiyar shi suna hannu na yanzu, bari inje in dauko…”. Tana shirin mikewa ya daga mata hannu “bayan Nina, Ni’ima da Khalisa sai kuma wa?” tace “sai mutanen Gaya. Su suke cewa “juya” ce. Don haka ne na kulla auren shi da Hanan don ya samu ‘ya’ya kawai wallahi, amma ba don in raba shi da matarsa ba….. kai shaida ne akan cewa tsakani da Allah ina son Mairo”. Ya kalli Nina da Khalisa da suka yi tsuru-tsuru, jikinsu sai kyarma yake. Don sun gigice da ganin ‘tension’ din mahaifinsu mai son su da gudun bacin ransu, tareda kyautatawa rayuwarsu tun daga yarinta har girma. Rayyah tace “wallahi babu ruwana……” Sabah tace “wallahi babu hannu na…..” Mami tace. “ni Daddy da ba a kasar nake ba, wallahi bani da masaniyar komai…….”. Juyawa yayi gefensa ya fizgo wayar talbijin. Ya soma binsu yana tsula musu. Duka na tashin hankali. Da masu ruwan, da wadanda suka ce babu ruwan su. Yana hawaye yana tafkarsu, yace “Kun yi asara! Kun kashe auren mutumci da amana da soyayya ta gaskiya!! Bazan yi muku baki ba. Amma kuji tsoron hakki. Kuje duniya kadai ta isheku, tunda kuma mata ne kuma aure kuke kamar yadda Mairo ke zaman aure. Sannan abinda kuka yiwa Mairo, kuka sa aka yi mata, zai iya faruwa da kowaccenku. Dan uwanku kuma idan yana da hakkinku Allah zai fitar masa, muddin ya mutu bai yafe muku ba. Kuma sai kun maimaita wannan magana agaban Habibu, sai Habibu yaji wannan maganar. Ke kuma Hajiya ki tattara ya-naki-ya-naki ki tafi Gaya, sai na nemeki…….bana bukatar ganin ki a cikin gidana yanzu……”. Kowa a falon kuka yake, yana rokon gafara. Basu kara tsananta kukansu ba, saida suka ji wannan danyen hukuncin da Daddy ya zartas akan Hajiya. Suka rirrike kafafun shi suna bashi hakuri yace “ni baku yi min komai ba. Wadanda kuka yiwa su zaku nema gafara amma ba ni ba. Sannan bazan taba sanya baki Mairo ta dawo gidan dan uwanku ba. Tunda bakwa son ta. Ku aura mishi duk wadda kuke so tazo ta cika muku gida da ‘ya’ya. Ko ya mutu, ko yayi rai, na barwa ALLAH! Ku bace min da gani dabbobin banza. Hajiya ina kara gaya miki, kada in dawo in ganki cikin gida na….”. Ya yarda wayar ya fice, yana share hawayen da suka cika mishi ido. *** Wasa-wasa sai da Mairo ta kwashe watanni uku cur cikin wannan halin, a lokacin cikin jikinta ya fito sosai, domin ya shiga cikin watanni na biyar. Rannan daga ita sai Hajiyar Dutsinma a dakin, ta farka daga barci, ta kurawa silin ido, al'amuran suka soma dawo mata tar-tar. Ta tuna wai Amiru ya sake ta, ba tareda ta yi mishi laifin komi ba, alhalin suna tsaka da son junansu. Bayan ta mallaka mishi duk wata soyayyarta. Sannan ya auro Hanan, ba ta fita daga wannan bacin ran ba, ya dankara mata saki, ta tabbatar bisa tursasawar Hajiya ne, amma Amirun ba zai taba yi mata haka akan-kanshi ba, ko giyar wake ya sha. Tana mai sa ran bada jimawa ba za su dai-daita da mijinta ya maida ita ta zauna lafiya da Hajiya Aisha, tunda abin da Hajiyar ta kwallafa rai, har ta tsane ta a kanshi, ga shi Allah Ya bayar. Sai kuma ta tuno wai an fada mata ya kara kamuwa da ciwon zuciya irin wanda yayi a baya, aka samu rayuwarshi da kyar da taimakon ta. Gashi yanzu basa tare. Kai ita ji tayi ma kamar ance ya rasu! Daga bakin Hajiyar Dina da ba zai taba yi mata karya, ko zolaya ba. Ta soma kuka a hankali, kukan sabo, soyayya, kauna da kewa. A tsayin zamansu na shekaru takwas, bai taba bata mata ba, sai bisa kuskure. Soyayyar da ya wanzar da rayuwarshi a nuna mata, wani abu ne da ba zai taba kankaruwa daga zuciyarta ba. Tunda ya aure ta ya haramtawa kanshi sauran mata. Bai kara hada jiki da wata diya mace ba, bayan ita, har inda yau ke motsi. Har kuwa wadda ya aura da auren sunnah. Taji wannan a bakin Hanan ba a bakinsa ba. Duk da matakin rayuwa irin nashi, wannan bai shagaltar da shi daga rudin duniya ba. Ta tabbata ta yi babban rashin da har abada ba zata mayar da makwafinsa ba. Ta mika hannu ta shafi kasan mararta, inda babynshi ke kwance, yana wutsil-wutsil cikin koshin lafiya. Ta lumshe ido a hankali, hawaye masu dumi suna zirara ta gefen idonta suna shiga cikin kunnuwanta. Ba ta damu da ta share ba, haka zuciyarta ba ta daina kokawa ba. A wannan halin Habibu ya tarar da ita. Ya ja kujera ya zauna yana fuskantarta. Ya ce. "Mairo, Mairon Dina, Mairon Yaya Habibu..." Ga mamakinshi sai ta fado jikinshi tana kuka mai tsuma zuciya. Ta ce. "Yaya Habibu da gaske mun rasa AMEERU?" Ya ce "Mun rasa auren shi dai Mairo, da gaske mun rasa auren mai kaunarmu da gaskiya da amana. Amma Ameeru yana nan a raye. Duk wanda yace dake ya rasu, ya fada miki ne kawai don ya tayar da hankalinki. Ko kuma baki tsaya kin saurara dai-dai ba. Amma yana gida, kwance a dakin ki. Akan gadon ki. Kwanciyar shi ciwo da rabuwar auren ku ya barni da kewa, da katoton gibi a zuciyata. Wanda mayar da shi wani abu ne da ba zai taba yiyuwa ba. Don haka ki dage da yi mishi addu’a. Allah ya bashi lafiya cikin gaggawa. To lose a friend like him, will be the GREATEST lose of all losses. To lose a husband like him, is another GREAT loss. (rasa aboki kamar sa, ba karamar asara ba ce daga manyan asarori, kuma rasa miji kamar sa, shima babbar asara ce.) Sai dai mu cigaba da yi mishi addu'a. Allah ya bashi lafiya. Wannan ne kadai babbar sakayyar da zamu yi wa masoyi irinshi. Amma ba da son ranshi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66