Chapter 35
Chapter 35
lumshe ido ya bude su dukka a kanta "Amma mai yasa Mairo? Komi yana da dalili, kamar ni, na so ki ne sabida wasu abubuwa guda uku, wadanda bazan iya gaya miki ba. To ke mene ne naki dalilin?" Ta so ta ce da shi "Sabida ina da wanda nake so". Sai ta tuno alkawarin da ta daukarwa Yaya Habibu, na barin soyayyar Junaid da mantawa da al'amarinshi. Don haka sai ta ce. "Sabida wasu dalilan nima, da bazan iya gaya maka ba!!". Sun dauki mintina uku shiru, babu wanda ya sake cewa da dan uwansa uffan. Kamin ya dauke ido daga kanta, ya ce. "Ni kuma na yarda ki aure ni ko da ba kya sona…!!!". Ta ce "Ba zan yi hakan ba, idan na yi hakan na yaudare ka, na ci amanar kaunar da nake yi wa Uncle Junaidu……....!!!" Ta yi saurin kai hannu ta toshe bakinta da karfi, ba ta san yaushe furucin ya subuto daga zuciyarta ba, ga shi an ce 'magana zarar bunu' ta riga ta fita. Sai ya kauce da zafin nama ya ba ta hanya sabida wani masifaffen KISHI da ya taho ya tokare masa a kirji. Ai tana samun hanya ta arce. Da kyar ya iya dago matattun kafafunsa bayan mintina goma sha biyar, ya nufo falon inda ya tarar da Raymond da Habibu akan tebur suna cin abinci, Dina na tsakiyar falon tana canza channel a talabijin. Abincin da bai ci ba ke nan, ya zauna cikin doguwar kujera fuskarshi babu walwala, ya ce. "Raymond idan ka gama sai mu wuce". Habibu ya juyo ya dube shi yana nazarinsa, ya ce "Ba zaka ci abincin ba? Mairo ce ta girka maka..........." Ya dago idanuwanshi da suka canza launi luuuu! Yana kallon Habibu a kankance, ya ce "Ba zan iya ba!!". Dina ta ce "Haba don Allah Amiru? Ba ka ga wahalar da ta sha wajen girkin nan ba? Idan ba ka ci ba bazata ji dadi ba". Bai san lokacin da ya ce "Ba don ni ta girka ba, don Yayanta ne". Daga haka ya mike ba tare da ya iya hada ido da kowa ba. Ya sake ce da Raymond, "If you finish, meet me outside….". Shima Habibu sai ya ajiye cokalin don jikinshi ya yi sanyi, don bai taba ganin Amirun cikin kwatankwacin irin wannan halin ba. Don haka ya mike ya bi shi wajen ya dafa kafadunshi da ya juya baya. Ya ce. "Mai ya faru ne?" Ya kalle shi kawai bai amsa ba, tambayar duniyar nan Habibu ya yi, amma ya ce "Babu komai". Don ba burinshi ba ne a takurawa Mairo ta aure shi. So na hakika ya ke nema, ba da tallafin wani ba. Mairo da ta koma daki kwanciya ta yi, rigingine cikin nadama. Kai tsaye ka dubi kwayar idon mutum mai kima kamar Amiru da ya ce yana sonka, ka ce ba ka son shi, ya zama wulakanci da cin fuska. To amma ita a ganinta dai-dai ta yi, don ba ta iya karya da yaudara ba. Amma dai duk da haka ta san ba ta kyauta ba, sai dai a ganinta gara hakan, da ta yi irin auren da zuciyarta ta raya mata. Dina ta yi sallama ta shigo, dauke da faranti tana cewa "Kin yi barci ne?" Ta girgiza mata kai, alamar "A'ah". Ta ce "To tashi, abincin da kike gudu ne na biyoki da shi". Ta tashi ta zauna sosai, ta karbi farantin ta soma ci, Dinan na kallonta. Can kuma ta ce "Mairo mai kika ce da Amiru ne? Ya shigo cikin walwalarsa, ya fita cikin yanayin da bamu taba ganinsa a ciki ba. Ina laifin wanda ke son ka?" Ta cira kai ta dube ta, sai kuma ta sunkuyar. Can kuma ta dago ta dube ta, ta ce "Yana magana ne akan wai yana sona, ni kuma na gaya mishi cewa, bana son shi!" Dina ta yi murmushi. Daga jin kalaman Mairo, da yanayin maganarta kasan kuruciya ke dawainiya da ita. Ta ce "Sabida mai ba kya sonshi Mairo? Ga shi kyakkyawa, son kowa, kin wanda ya rasa. Ga shi da ilimi kamar Yaya Habibun da kike cewa yana burge ki. Yana da mata Baturiya, amma ya tsallakota ya zo ya ce yana sonki. Zai iya rabuwa da ita sabida ya aure ki. Ga shi da kirki, ga addini. Ke kuwa mai kike nema a da namiji da ya wuce wannan?" Sai Mairo ta sa kuka. Ta kwantar da kai a cinyoyin Dina, tana kuka mai tsuma zuciya. "Na kasa mance Uncle Junaidu ne Aunty Dina. Na kasa mance dumbin alherin da ya yi min a rayuwa. Shi ne tsanin duk wani matsayi da matakin da nake kai a yau. Idan na auri wani ba shi ba, na ci amanarsa…...." Dina ta katse ta "Akwai hanyoyi da yawa da zaka saka wa mutum alherin da ya yi maka ba dole sai ta hanyar aure ba. Misali shi ne, ka dinga binshi da kyakkyawar addu'a ba tare da shi din ya sani ba. Wannan addu'ar Allah Ya yi alkawarin karbarta. Kada ki yi mamakin zuwa yanzu shi Junaidun ya samu wata da yake so ya aura. Ni na kasa gane kan wannan soyayyar da kike yi wa Junaid, maras dalili. Kin ce bai taba cewa yana sonki ba. Kin ce ba ku yi alkawarin aure ba, kin ce yasan gidan Baffa, amma bai neme ki ba. To ki gaya min wacce hujja gare ki da zata tabbatar da cewa yana sonki? Ba ki san akwai masu taimako sabida Allah ba, ba don a aure su ko a saka musu da soyayya ba? Haba Mairo, ki yi tunani mana? Ki yi aiki da hankalinki. Ki so mai sonki a zahiri da badini. Ki yi aure saboda Allah da raya sunnar ma'aiki, amma ba don abin da zuciyarki ta afu akai ba. Mai yiwuwa ne shi wannan abun da kika kwallafawa ran ba alheri ba ne a gare ki, wanda ba kya so din shi ne alherin. Idan kika fauwalawa Allah a hankali za ki so abun, tunda shi ma Junaid ba lokaci daya kika fara sonshi ba, so na soyayya, kin ce sai da tafiya ta yi tafiya kika mallaki hankalin kanki, sabida fahimtar halayenshi da kika yi. Shi ma Amiru a hankali za ki fahimce shi, kuma ki so shi wallahi fiye da son da kike wa Junaid ma. Ba ki ci amanar Junaid ba, ba ki yaudare shi ba tunda ba alkawari kuka yi ba. Iyakar soyayya ta gaskiya kin yi wa Junaidu, ko ba ki aure shi ba Allah Ya shaida ya yi alkawarin sanya masoyan gaskiyan da suka mutu ba tare da sun auri juna ba a aljanna. Ina tunanin Junaid ya yi abin nan ne da Hausawa ke cewa, "A BARI YA HUCE... SHI KE KAWO DA RABON WANI". Ta dubi Dina sosai, ta ce "Idan haka ne Aunty Dina, kema kin yarda Uncle Junaid yana sona? Furtawa ce bai yi ba, kamar yadda Inna da Nabilah ke cewa?" Gyada kai Dina ta yi, ta ce "Eh, yana sonki, amma ya bari YA HUCE... Don babu wata mu'amala ta mutumci da tausayi tsakanin mace da namiji sai SOYAYYAH! Idan ma mutumcin ne da farko, to
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66