Skip to content

Chapter 47

Chapter 47

Abari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

umarnin ubangidansu. Masu fushi da fushin wani. Fatali kawai suke da komai dake cikin gidan. Ya fizge kafarshi cike da kyama yana ja da baya tamkar ta dana masa garwashin wuta, a baya in Habibu ya ce kyamar Harrit yake mugun haushinsa yake ji, amma a yau ji yake har zuciyarshi na tashi da kallonta, ya fice babu waiwaye yana mai kara jaddada mata cewa, kada ta sake ya dawo ya ganta ko wani tsinkenta a cikin gidanshi. Bai kara bi ta kan Harrit ba, don ya lura idan ya ce bakin cikinta zai sa a ranshi shi ne zai cutu a banza. Amma alal hakika Harrit ta sanya kasar America ta fice mishi a rai. Dan burbushin kewar kasar da ya rage a baya ya kara zagwanyewa Ya samu kanshi da rashin yarda da kowa, hadi da shi kansa kuwa. Mairo ce kadai yake tunawa ya ji sanyi a zuciyarshi. Itan kam ya yarda da ita da wata irin yarda da bai taba yiwa kowa ba bayan Habibu in ka cire iyayensa, bayan budurcinta data kawo masa cikin girma da daraja, yana da wata irin yarda akanta, yana samun wata irin nutsuwa a duk lokacin da yake tareda ita. Amma ita kanta Mairon a yau sai yaji bazai iya magana da ita ba. Don haka ya kashe dukkan wayoyinshi. Cikin sati daya rak! Duk abin da ya kai shi ya gama shi, hankalinshi ya yo gida kwarai, amma dole ya biya wajen Habibu maganar karatun Mairo. Don haka daga Washington kai tsaye Michigan gidan Habibu ya nufo a Detroit. Habibun ya je da kanshi filin jirgi ya taho da shi. Hakika idan ka dube shi zaka lura cewa, a razane yake, a firgice da al'amarin mata. Ita ma Mairon sai yake ganin kamar kafin ya koma zata yi mishi haka! Don haka ya kulle kanshi a hotel din (RAMADA INN) tare da kulle wayoyinshi don ya samu daidaituwar kwakwalwarshi da tunaninshi. Ba abin da ke tashinshi daga shimfidarshi sai sallah da cin abinci, shi kansa Habibu bai san inda ya shiga ba. Tsayin sati guda sannan ya samu ya yi 'regaining consciousness'. Sannan ya nufo gidan Habibu. Habibun ya ganshi kamar daga sama, koda wasa bai yi gigin fada mishi abin da ya faru ba, don yasan dariya zai yi mishi, dariya har da ta keta, tunda babu yadda bai yi ba ya nuna mishi illar da ke tattare da auren mushrikiya, amma Amirun bai gane hakan ba, sabida giyar soyayya na dibanshi a wancan lokacin, don haka idan yana da kunya ai ba zai neme shi ba. Da ya tambaye shi Harrit sai ya ce da shi, sun rabu ta koma Philppines, bayan idan za a kashe shi bai san inda ta nufa ba. Dina na kicin tana hada musu abincin dare, a yayin da su kuma suke baje a falon suna aikin takardunsu cikin systems. Kallo daya Habibu ya yi mishi ya tabbatar yana cikin wani bacin rai mai zurfi, ya yi tambayar duniyar nan amma zurfin ciki irin na Amiru ya hana shi fadar abin da ke damunsa. Shi kuma Habibun ya takura sai ya ji, daga karshe ya yanke shawarar fada mishi ko da kuwa zai yi mishi dariyar ne, akalla ya samu rangwamen radadin da zuciyarshi ke yi da nauyin da ya danne ta. Habibu ya yi shiru, can kuma ya ce "Ban yi mamaki ba. Shi arne wannan (adultery) a wajenshi ai ba wani abu ba ne extraordinary. Sai a yi hattara, Allah Ya kara tserar da mu daga kutungwila da kaidin ZUCIYA. Amma ni a ganina wannan ba wani abu ba ne da zaka sanya shi a ranka har ya haifar maka da hawan jini, tunda ka san abin da ka aura ai ka aura din. Sannan sabawa mahaifa ai ba abin da ba zai janyo mana ba mu 'yan Adam, don haka sai mu yi fatan Allah Ya kiyaye gaba, Ya sa mu gama da duniya lafiya". Ya ce. "Ina son farantawa Mairo Habibu, kamar yadda ta ke haifar min da nau'o'in farin ciki a kullum. Don haka nake ganin zata dawo nan ta karasa karatunta kamar yadda ta faro shi cikin nasara. Ba zan bari ya kasance ni din na yi silar rabata da burin rayuwarta ba, da tubalin da ka jima kafin ka assasa. Don ko a yanzu na fita na dawo kullum sai na ganta tana bitar littafanta, duk da cewa bata taba yi min korafi akan hakan ba. Ni da na yi mata na ga farin cikinta fiye da kullum, tayi min abinda bata taba yi ba, idan na samu sarari zan dinga lekowa akai-akai insha Allahu". Habibu ya ji dadin wannan karamci da Amiru ya yi mishi, don shi ma abin yana damunshi, don bai san tsarin sa bane shi yasa tun farko bai neme shi da zancen ba. Don haka a washegari suka nufi Michigan State University tare don gyara mata registration dinta. Ya rage saura kwana uku Amiru ya dawo, Hajiya ta yi kiran Mairo, ta hadata da wasu jarkokin magani da zuma roba guda da Mairo ba ta san ko na mene ne ba. Ta ce, ta je ta yi ta kwankwada, ta kawo mata jarkokin kafin kwana uku. Ta bi umarnin Hajiyar don tasan ba zata ba ta abin da zai cuce ta ba, bare wannan magani mai shegen dadi da zaki. A'ah! Ai tun a washegari ta ji yanayin jikinta na sauyawa, ba abin da ta ke bukata sai dawowar Ameeeru, da yake saukar karfe shidda na yamma za su yi, don haka tun safe tana kicin dinta tana hada abincin tarbar angon nata. Da taimakon daya daga cikin masu aikin Hajiya da Hajiyar ta bata don su Sabah duk sun koma makaranta, komai ya hadu. Babu yadda Hajiya ba ta yi ba ta je airport ta tarbo shi ba, amma kunya ta hanata. Wannan na daga cikin halayen yarinyar da suke kara mata kaunarta. Ta lura bayan kunya, tasan mutumcin kanta, kuma ta iya zama da kowa da wata mu'amala ko ya ya ta hadata da shi. Tana sassan Hajiya suna sauraron labaran MBC a lokacin da ya iso, daga bakin kofa ya tsaya, ya tokare kofar da hannunshi na dama yayin da na hagun ke dauke da falmarar din ‘Italian suit’ ruwan toka, wato 'grey' da ke jikinshi. Ya rausayar da kai yana kallonta, da kyawawan idanunshi, ba tare da ita din ta sani ba. Sassanyan kamshin 'miyaki' da ya bakunci hancinta shi ya ankarar da ita tsayuwarshi a bakin kofar n wasu mintuna. Ji ta yi kamar an yi mata gafara sabida farin cikin dawowarsa cikin koshin lafiya. Ta lumshe ido ba tare da tasan lokacin da ta yi hakan ba. Hajiya tana ta magana, amma ba ta ji Mairo ta bata amsa, sun yi nisa a kallon junansu kamar yau suka fara ganin juna. Ta juyo don ta dubi Mairo, a sannan ne ta ankara da inda Mairon ta kafa wa ido. Ta ce "Au, ashe mijinki kika gani kika manta da ni nake ta sambatu ni kadai?". Ya yi dariya ya idasa shigowa dakin. Ita kuwa don kunya sai ta zame ta gudu gidanta ba ta kara lekowa sassan Hajiya ba. Tana shafa a gaban mudubi,

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66