Chapter 48
Chapter 48
ga dukkan alamu daga wanka ta fito. Daure da tawul iya cinyoyinta. Ya bude kofar ya shigo cikin bakaken pyjamas, tana hango shi ta cikin mudubin a lokacin da ya iso gare ta. Ya dora kai a hankali kan kafadunta ta baya, kyawawan fuskokinsu suka bayyana cikin mudubin a jere, a hankali ya sanyata cikin jikinshi ya lullube da hannayenshi, yana shakan sassanyan 'bathrobb' dinta na ‘rasasi’ yana lumshe ido. Ya ce "Tell me how much you misses me, ko ba ki yi kewata ba ne Mairo? Don na ga ke har wata kiba kika kara abunki, ni kuwa ina can tunaninki ya hana ni sukuni". Murmushi kawai ta yi har 'beauty point' din mai kara mata kyau ya lotsa ciki sosai. Ya sumbuci wajen with a very warm kiss, kana a hankali ya soma warware mata tawul din suka soma aikin lada. *** Wata guda da dawowarshi, suka yi shiri suka nufo Kano don yi wa Baffa sallama, kasancewar a cikin satin ne zata koma Michigan. Su Habiba an shiga makarantar ta nutsu don yanzu Mairon da suke wulakantawa ta zame musu uwargijiya da bazarsu suke rawa. (To ina ruwan Allah!) Tuni aka sa Lawan ya gyare musu dakin baki, ya kunna 'burner'. Abinci kam sai wanda suka zaba. Baffa ya ji dadin ganin yanayin da Mairon shi ke ciki, ta cika ta yi bul, ta zama babbar mace, kamar kajin Agric jawur da ita. Ya tarasu duka ita da Amirun ya yi musu kyawawan nasihohi akan rayuwa, da kuma yadda za a yi a ci ribarta. Ya kare da yi masu nasiha akan muhimmancin riko da sallah akan lokacinta. “Ita ce idan ta yi kyau dukkan ayyuka za su kyautata”. Amiru na son Baffan Mairo, sabida sauran mazan jiya ne ba na yau ba, irin wadanda kyale-kyalen duniya ba sa gabansu. Ya cika su da alheri duk gidan, a washegari suka nufo Michigan. Dina ce ta zo ta tarbe su, domin Habibu ya yi balaguro zuwa New-Jersey. Mairo ta rungume 'ya'yanta kamar ta tsaga kirjinta ta sanya su. Suna fada mata, "Mun yi missing dinki Anti Mairo, da gaske ne da Daddy ya ce anyi miki aure da Uncle Amiru???" Inji Bedi. Murmushi ta yi, cikin matsanancin nishadi tana shafa kan yaron, amma ba ta amsa musu tambayar ba. Amirun ne ya ji, ya juyo daga maganar da suke yi da Dina ya bashi amsa cikin daga gira. “yes Muhammad da gaske ne, Daddy is absolutely right! Har ma ta kusa ta kawo wa little Mairo kanwa, nan da wasu watanni kadan”. Da sauri Mairo ta bace a wurin. A ranar Amiru ya juya Washigton don karasa wasu hidimominsa tare da jaddawa Dina amanar rayuwarsa, wato Mairon da ta dusar da hasken sauran matan duniya baki daya daga idanunshi. Sun kulle a daki ita da Dina ana labarin bayan rabo. Dina ta kura mata ido ta ce "Anya Mairo? Jikin nan naki babu bayani? Irin wannan fari da kyau haka sai ka ce mai shafe-shafe? Ko dai kwanan nan za fara goyo ne? Naji Amiru na fadawa yara dazu na dauka wasa yake" Mairo ta rufe fuska da tafukan hannunta, ta ce "Kai Anti Dina, wallahi ba ni da komi. Karewa ma yanzu haka period nakeyi. Ni fa tunda na je gidan dakina daban nashi daban. Kuma ba sai ana kwana daki daya ne ake yin cikin ba?". Dina ta kyalkyale da dariya ta ce. "Amirun? To abar kazar cikin gashinta tunda ba kya son a fige ta kada in zama babbar banza". Ta jawo lokarta ta soma fiddo mata magungunan mata masu kyau da tsada 'yan Indonesia data ke saya tana yi mata bayanin tsarin shan su. Mairo ta ce "Maganin mene ne?" Dina ta murmusa, ta ce, "Maganin basir ne, ke dai ki dinga sha don da alama akwai basir a jikinki tunda ga shi nan duk kin yi fari". Mairo ta yi dariya. Ta rasa dalilin da yasa kullum Dina ke treating dinta yarinya kamar Little Mairo. Idan dai wadannan magangunan ne ai tunda ta zo gidan ta ke ganin Dinan na shansu, sai dai ba ta taba tambayarta ko na mene ne ba. Amma yanzu ai ta yi girma da hankalin da zata san amfaninsu. Daga baya ko me Dinan ta tuna? Ta zaro ido ta ce "Ke! Bani magungunan nan bai kamata ki fara amfani da su ba, sai mun je asibiti anyi checking dinki don ban yarda da ke ba. Mai juna biyu ba ta amfani da irinsu". Mairo ta bata fuska kamar ta yi kuka, don gani ta ke kamar Dinan na kallon abin da ta ke yi a goshinta. Ta tashi gudu tayi dakinta. Dina sai ta yi dariya, kuruciyar Mairo da halayenta na alkunya suna burge ta matuka. Satin Amiru daya da tafiya sai ga shi kamar an jefo shi. Tana kicin tana hadin salad don haka Dina ce kadai a falo, ita ma ba ta jima da dawowa aiki ba, ta sanya Mairon ta hada mata salad zata ci. Kararrawar kofar shigowa ta yi kara, ta umarci Lynder ta bude. Amiru ya bayyana a falon cikin bakaken suit-spanish. Ta daga kai tana kallonshi tare da amsa mishi sallama, ganinshi wani 'as a smart pace' (afujajan) ya bala'in ba ta dariya. A gajiye ya zauna cikin kujera idanunshi a kwance ya ce "Dariyar me kike yi min?" Ta ce "Ganinka na yi kamar an jefoka, lafiya dai ko?" Ya ce "Da babu lafiyar ai ba za ki ganni ba, sai dai sako. Ina kanwar takin nan ne? Yanzu haka kina nan kina hadata da wadannan girke-girken naki na tsiya". Ta ce "Au na tsiya ne, amma idan an baka kake ci?" Bai amsa mata ba ya nufi kicin inda ya jiyo motsin tangaraye. Ta juya baya ta takarkare tana bude gwangwanin 'heinz-beans' ya mika dogayen hannuwanshi ya rungume ta. Ya soma sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Kwanaki bakwan nan da ya yi ba tare da ita ba, jinsu ya yi kamar shekaru bakwai. Ka zalika ita ma Mairon, don dai ta kasance mai zurfin ciki da kawaici ne. Amma ta yi missing din mijinta yadda harshe ba zai iya bayyanawa ba. Sun yi nisa cikin duniyar faranta ran junansu, kafin Mairo ta ankara da inda suke, ta yi kokarin kwatar kanta. Ya dago habarta da hannun damanshi yana son kallon kwayar idanunta, amma bai yi nasarar hakan ba sabida matsananciyar kunyarshi da ta lullube ta. Ta yi azamar hankade shi sabida warin 'aspen' da ta tsinkaya cikin bakinshi. Ya sake kamota ta fuzge, ya ce, "Haba Mairo? Mairon Dina, Mairon Yaya Habibu?" Zata fice ya sha gabanta a galabaice, ya ce, "Kina so Mala'ikun rahma su soma tsine miki ko, bayan da kina ta kwasar lada?" Inda abin da Mairo ta tsana to wannan furucin ne, kamar ta yi kuka ta ce, "Ni na ce ka sha taba? Tun a gida ka ce min ka daina sha, amma ai ga shi nan na ji-ta a bakinka". Ya rufe mata baki, ya ce, "Wallahi bazan kuma ba. Wannan din ma a jirgi aka ba ni. Ba kudina na sanya na siya ba. Ce miki nayi “bazan kuma sayen taba ba”, ba “bazan kuma shan taba ba..” Sun ba ni 'wine'
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66