Chapter 32
Chapter 32
ratsa zuciyarshi, ya ce "Shikenan kuma don kin yi kanwa ni kin yaye ni?" Ta soma yi masa alama da ido, Mairo na jinsa. Itama Mairon juyawa ta yi ta fice a ranta tana ce, 'Ku cinye kanku da soyayyar". Ai kuwa tana fita ya yi super ya suri Dinan yana cewa "Gaya min wanda ya ce da ke kanwa ta fi miji????" Mairo wajen Hajiyar su Dina ta koma tana goga goro a magoginsu na tsoffi, da gani ka ga 'yar gatan tsohuwa da da ya hucewa takaicin duniya. Ga wasu mulmulallun awarwarayen zinari a hannunta guda uku, sai walwali suke, tufafin jikinta kadai, sun ishi karamin talaka jari. Ta zauna gefenta ta ce "Hajiya kawo goron in goga miki". Ta mika mata dankwalelen goron fari sol da magogin ta soma gogawa, in ya taru ta mika mata ta hambuda a baki. Tana bai wa Mairo labarin Dina. Ta ce "Kin ganta nan, duk cikin jikoki na ashirin da biyar na fi sonta. Sabida halayenta na kwarai da rashin daukar rayuwa da fadi. Babanta shine da na biyar cikin 'ya'ya biyar da na haifa suna mutuwa, shi kadai ya tsaya. Kuma daga shi Allah bai kara ba ni da namiji ba, sai kannensa mata guda biyar. Ita ce 'yarsa ta fari, sai tarin kanne guda bakwai. Ta kawo Yayanki dalibi da ba shi da komai ta ce ita shi ta ke so ta aura. Da fari ba mu yarda ba, tunda ba mu ga iyayenshi ba, shi kuma ya ce, ba zai koma gida a wancan lokacin ba. Ya fito neman ilmi da arziki ne sai Allah Ya yi mishi zai koma, don haka muka saduda muka yi musu aure. Da ya ke abokiyar arzikinshi ce ga shi Allah Ya azurta su, da 'ya'ya da dukiya. Allah Sarki, ashe iyayen da ya nema don su huta, kamar yadda nake hutawa a tsufana, Allah bai yi za su mori arzikinsa ba. Ki saki jikinki, ki kwantar da hankalinki da Dina, zata zame miki uwa, abokiya, kuma Yayar kwarai, kin ji Maryamu?" Ta girgiza kai, ta ce "Na ji Hajiya, Yaya Habibu ma ya gaya mini". Dina da Habibu suka shigo, sun jero, tsawonsu daya, takunsu iri daya, sai annuri ke fita daga fuskokinsu, ga dukkan alamu an ci soyayya an koshi. Ta dubi Hajiya da Mairo da ta takarkare sai nika goro ta ke yi, ta yi dariya ta ce "kawa da kawa, hirar me ake yi?" Hajiya ta ce "Ina ruwanki da hirarmu? Ko mu mun tambaye ki hirar me kika je taya mijinki?" Habibu ya nitse cikin leather yana amsa waya da thuraya dinsa, cikin wani dan bantan uban Turanci kamar Karl Mad sabida yadda Turancinshi ke fita tar-tar irin wanda Mairo ba ta taba ji ba. A da, tana tsammanin a duniya babu wanda ya iya Turanci irin Uncle Junaidu, ashe Junaid rarrafe yake yi, ga wadanda suka mike suke dabo, suka tsaya da kafafunsu. Kwanansu uku a Dutsinma suka tattaro suka yo Kano, Mairo dai kamar ba zata tafi ba sabida jin dadin zama da Hajiya, har hawaye ta ke da suka fito za su tafi, Habibu da Dina na mata dariya. Hajiya ta cika mata Bacco fal da atamfofin edclusibes irin wadanda 'ya'yanta ke kawo mata, don ta dinka, amma ta tattara ta bai wa Mairo. Wannan a jinin Mairon yake, FARIN JINI da shiga zucci. Idan ka zauna da ita yini guda, zaka so ka kwana da ita. Idan ka kwana da ita, zaka so kayi wata tare da ita, idan ka yi wata tare da ita zaka so ka yi zaman shekara da ita, haka idan ka yi shekara da ita, zaka so ka zauna da ita har zuwa karshen rayuwarka. Karfe uku dai-dai na rana suna cikin Kano, Habibu ya karya kan mota suka shigo Yakasai. Tun daga nesa wani dankareren European Billa (Bungalour) ya dauki hankalinta, ya karkada mata 'ya'yan hanji. Abin mamaki a get din gidan Habibu ya sanya hancin motarsa kirar Porsche. Zuciyarta na gaya mata, wai wannan gidan Baffa ne? Amma wani sashen na karyatawa. To idan ba shi ba ne, wanne ne? A nan dai gidan Baffa ya ke, ga makotansu nan ba su motsa daga inda suke ba, su ma sun samu arzikin sabon fenti irin na gidan. Dama dai gidan Baffan babba ne, ga kuma bene an daura, ko ina gilashi da tile ke zagin idonka. An fidda sashen baki daga gaban gidan, a cikin gidan kuma sashe biyu ne na matan gidan, sashe guda na yara, Baffan yana sama, sai dakin 'yammata. Kowanne daki an kafe plasma a sama tana ta aiki cikin tasoshin tauraron dan Adam, ga dindima-dindiman kujeru masu nishi 'yan Italy da labulaye masu garai-garai da gani tafiyayyu ne tun daga China. Abin dai ba a cewa komai sai a gaida Habibu, a gaida ma'aikatan Julius Berger. A gaida Habibu da aikin ZUMUNCI, da rama hairan da hairan. Suna tsayuwa su Rahma suka diba yuuu! Suka yi cikin gida suna ta ihu, “turawan sun dawo da Mairo, ba su sace ta ba. Baba ga Mairon nan sun dawo da ita". Baffa dai baki ya ki rufo, ya fito ya taro su, Abbas ya gane shi, ya je ya kama hannunsa, Hajara da Habiba kowacce ta fito daga bangarenta bakin nan kamar gonar auduga, har rige-rigen daukar Mairo karama su ke. Mairo fa ta fara jin tsoron al'amarin Habibu. Allah dai Ya sa ba kungiyoyin nan na matsafa da sassan jikin mutum ya shiga ba. Allah Sarki! Da tasan Barclays da ba ta ce haka ba. Hankalinta na kan 'yar uwarta Ladidi da halin da ta tafi ta barta a ciki. Don haka suna shigowa ta tambayi Habiba "Ina Ladidi?" Habiba wadda ke jin kamar ta suri Mairo ta goya don ta samu fada wajen Baffa wanda ya daure musu fuska tam ya ki kula su don yasan duk borin kunya suke yi. Ta nuna mata dakin da Ladidi ta ke, ta ce "Halan Mairo a inji matar Habibu ta sakaki ta wanke?" Mairo ta yi murmushi ta ce "A'ah, a lagireto ne". Ta wuce ta barta nan, tana ta sosa keya don kunya. A dakin ta cimma Ladidi, an yi dai-dai cikin Italian bed, ana shan lemon Safari ana kallon tashar Zee-Aflam, ba tasan sanda dariya ta kubuce mata ba, don kwata-kwata ba ta yi matching da gadon ba da dakin gaba daya, ta fi dacewa da mai aikin dakin ba mamallakiyarshi ba. Tana ganin Mairo ji kake kat, ta kware. Ta dinga tari ba kakkautawa. Mairo ta zauna a bakin gadon tana yi mata sannu. Ta mutsittsike ido ta ce "Mairo ke ce kuwa?" Ta ce "A'ah, ba ni ba ce, Ladidi ce". Ladidi ta soma kuka ta ce "Don Allah Mairo ki yafe mini. Ga shi dai tun a gidan duniya mun ga ishara, dan uwa duk lalacewarshi ba abun wasa ba ne, sai dai nasan kome zan fada miki a yanzu ba zaki yarda ba, za ki ce don na ga Habibu ne, ko don abin da ya yi mana, amma wallahi ba haka ba ne. Yadda kuma kika rufa min asiri a duniya, Allah Ya rufa naki duniya da lahira". Ta sa habar zaninta ta share ido.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66