Skip to content

Chapter 14

Chapter 14

Abari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

nike ki debi jinina idan ya yi dai-dai ki sanyawa student dina". Ta ce "To bari in diba kadan a auna a gani". Ta zuka kadan a sirinji ta mikawa lab asisstant ta auna, ya nuna (negatibe), ga duk wasu gwaje-gwaje da akayi, sannan dukkansu a 0+. Ya kwanta ta debi leda biyu ta ce ya ci gaba da kwanciya ya huta. Ta ba nurse ta sanyawa Mairo ta dawo tana fada mishi irin abincin da zai ringa ci har zuwa kwana bakwai. Nan da nan labari ya watsu cikin FGGC cewa Uncle Junaid ya yi donating jini wa Maryam. A'ah, cece-kuce ya soma (round) zagaye makarantar musamman daga 'yan ajinsa da daman suna hankalce da su. Yara kanana da su amma sun iya gulma. 'Yan manyan aji kuwa masu yi masa asirtacciyar soyayyah, wadanda a da ba su san da Maryam din ba suka zo suna kallonta, duk ta takura ta rasa inda zata sa kanta, balle da ta lura har da masu yi mata mugun kallo. Ranar da ta dawo hostel Kausar kunyarta ta ke ji, ko ido ta kasa hadawa da ita. Daga baya da ta ga Maryam din ma ba ta damu ba harkar gabanta kawai ta keyi, sai ta zo bakin gadonta ta zauna ba ta ce komai ba. Nabilah ta shigo itama ta zauna a katifarta abin da ko da wasa ba su taba yi ba. Suka ce "Don Allah don Annabi Maryam ki yafe mana. Wallahi sharrin shaidan ne, kuma mun gode da sacrifice (sadaukar da kan) da kika yi mana. Muna rokonki daga yau mu zama daya a makarantar nan, wato mu zama mu uku cikin amana". Mairo ta yi murmushi ta ce "Babu komi, ni dama ban taba kullatarku ba, mamaki dai kuke ba ni. Amma shi ke nan, komi ya wuce". Daga ranar Maryam, Nabilah da Kausar ba a kara jin kansu ba. To sai kuma ciwon ciki ya kama Kausar, kullum ba ta iya barci, sai murkususu da kuka cikin dare, haka suke kwana tsaye a kanta har asubah sannan zata samu barci. Da suka ga abin ya fi karfinsu sai suka yi reporting ga hukumar makaranta. Aka dauki Kausar zuwa maternity inda aka gano kabar ciki ke damunta. Nan da nan aka yi hamzarin mikata gida, domin abin ya fi karfin asibitin makaranta. Suka koma kewar Kausar tare da yi mata addu'a, kullum, har lokacin jarabawa ya matso. Kokarin Uncle shi ne Maryam ta saki ranta ta yi abin kirki a jarrabawarta, amma ina! Tunanin Kausar da halin da ta ke ciki ya hanata zama lafiya. Ranar da suka soma jarrabawa suka dawo hostel sai suka ga babu ko allurar Kausar a dakin. Captain da Metron sun kwashe sun bai wa iyayenta. A gigice Mairo ta fita kafarta ko takalmi babu, kanta babu kallabi. Nabilah ma ta bi ta dakin Metron suna tambayarta yaushe aka kwashe kayan Kausar? Ta ce "Allah sarki, wannan yarinyar diyar Gwamnan Jos, ta rasu. Tun satin da ya wuce". Suka rushe da kuka, suka zube anan suna ta yi. Tsoron Allah Ya kara shigar Maryam da Nabilah. Tun daga ranar suka koma wasu irin sukuku, ba fuss ba ass. Shi kansa Uncle ya girgiza da mutuwar Kausar, ya yi ta lallashinsu yana ba su baki. Ya ce da Nabilah abin da yake ankarar da ita ke nan kan daukan duniya da zafi. Shi Ubangiji ba ruwansa da ko kai wane ne, dan wane ne, wane ne ubanka face ayyukanka kyawawa. Nabilah ta fi Maryam ramewa, ta fi ta gigicewa, domion dai ta fi ta shakuwa da Kausar. Sannan ta kara rungumar Maryam a matsayin 'yar uwarta don sai ta ke ganinta kamar Kausar. Aka yi jarrabawa aka kare, sai hutu sati mai zuwa. Sai dai fa daga Maryam har Nabilah kowacce cike ta ke da zullumin sakamakonta. Uncle ya yi fushi da Maryam sosai, domin ta dauko na talatin da takwas yayin da Nabilah ta dauko na arba'in. Ta kaskantar da kai ta dinga ba Uncle hakuri, ta tabbatar masa zango mai zuwa za ta dage ta yi abin da zai ji dadi. Mutuwar Kausar ke nukurkusarta har zuwa lokacin. Ranar hutu malam Bedi sammako ya yi domin hedimasta ya gaya masa tun ana saura kwana uku, don haka a kwanakin nan barcin da suka yi kalilan ne sabida dokin dawowar Mairo. Barin ma Inna Hure da shiga goma, fita goma sai ta siyo abin da zata ajiyewa Maironta. Tun daga kan goriba, kurna, goba, magarya, dinya da ire-irensu wadanda tasan Mairon na so babu wanda ba ta nemo ta ajiye mata ba. Duk sammakon Baban Mairo bai isa makarantar ba sai da aka soma dadewa. Mairo da Nabilah na zaune karkashin dalbejiya dukkaninsu cikin damuwa suke na rashin ganin kowa nasu. Nabilah ta ce "Da na san gidanku Maryam da na zo kamin na wuce Lagos hutu wurin Auntyna". Maryam ta jinjina kai ta ce "Ba zaki iya zuwa gidanmu ba, can ne cikin surkukin kauye, cikin Fanshekara". Nabilah ta ce "Don ba kisan yadda nake son zuwa kauye ba ne, idan kuma kin musanta hakan ki gaya min ki gani". Ta dauko biro da jotter tana jiran ta bakin Mairon. Mairo ta ce "Fanshekara, motar Gurin Gawa, idan an shiga Gurin Gawa, sai a tambayi gidan Malam Bedi kowa ya sani. Idan kuwa yara ne kika ce musu 'MAIRON HURE' da gudu za su rako ki". Duka Nabilah ta dauke cikin jotterta, wanda ke bayansu ma ba su san da tsayuwarshi ba shi ma ya dauke cikin kakkaifar kwakwalwarsa. "Lah, ga Babana nan!". Mairo ta fada cikin matsananciyar murna, kamin ta kwasa da gudu ta rungume Malam Bedi. Nabilah ta dago daga rubutun da ta ke ta bi bayan Mairo da kallo, sai ta hango ta rungume da wani yagulallen tsoho, sanye cikin yadin algarara, kanshi duk furfura. Ta ce a ranta, "Ya za a yi ace wannan ne ya haifi Mairo? Ya fi kama da kakanta fiye da babanta". Ba tasan cewa ba wai shekarun da ya yi a duniya ba ne suka janyo masa wannan tsufan ba, a'a, wahalar rayuwa ce kawai ta noma, girbi, da sussuka irin ta kowanne manomin kauye. Tausayin Mairo ya kamata, ta tabbata ita 'yar talaka ce futuk, amma she is contented with what she habe (a gamshe ta ke da abin da ta ke da shi, ba ta taba kwadayin abin hannun wani ba). Mairo ba ta taba tambayar Nabilah ita 'yar waye ko daga ina ta fito ba. Wannan ya sa Nabilah tambayar kanta, shin Maryam wace iri ce? A zahiri miskila ce, abin da tasa a gabanta shi ne kawai ya dame ta. Ta mike ta tadda su tana gayas da Malam Bedi cikin tsananin girmamawa. Mairo ta ce "Baba Nabilah sunanta, ajinmu daya, dakinmu daya. Da har da Kausar amma ita ta rasu". Fuskarshi ta nuna bai ji dadi ba, ya ce, "Sannunki Nabilah, Allah Ya jikan Kausar". Idanunta ya ciko da hawaye, ta juya tana sharewa ta ce, "Amin". Babu irin neman da ba ta yi wa Uncle ba, don su gaisa da Babanta, amma ba ta ganshi ba. A haka cikin rashin jin dadi ta yi sallama da Nabila rike da 'yar jakar kayanta ta buhu (Ghana Must

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66