Skip to content

Chapter 23

Chapter 23

Abari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,221 words 0 views Progress saved
Download Book

ga inda zata dosana duwawunta ba a dakin, don haka ta aje jaka ta soma tattara mata shirgin waje guda ta gyare dakin tsaf ta share ta kwashe ta zubar. Ta gabatar da sallar azahar da la'asar da suka wuce ta, ta dauko karamin Alkur'aninta ta soma tilawa. Ko aya biyar ba ta yi ba cikin suratul Ma'idah, Hajara ta kwalla mata kira. Ta rufe Alkur'anin ta ajiye mayafi ta fita. Ta nuna mata tulin wanke-wanke ta ce "Kina ganin aiki ya kacame min amma kika tafi kika kule a daki ko uwar me kike? Oho! Maza wanke su yanzun nan cikinsu zan kwashe tuwon dare". Ta ja kujera ta soma wanke-wanken, Hajara ta sake cewa "Ki dinga iza min wutar nan, sallah zan yi". Ta ce "To". Hajara na shiga bayi Habiba ta fito, ta ce "Cika min randar can da ruwa, ga kuma tsummokaraina ba yawa, ki dauraye min su". Ta zube mata tulin atamfofinta a gefe, ta ce "To bari in karisa wa Aunty Hajara wanke-wanken, ta ce tuwo zata kwashe". Habiba ta ce "Inye, wato aikin Hajara ya fi nawa don ni kin raina ni, sabida ina sakar miki fuska?" Ta tsame hannunta daga wanke-wanken zata fara yi mata wankin Hajara ta fito daga bayi ta ce "Au, bar min wanke-wanken za ki yi sabida kina tsoronta? To ba zaki yi wankin ba, sai kin gama mini". Suka soma bala'i a tsakaninsu, Mairo dai tsayawa ta yi kawai tana kallonsu. Baffa ya shigo yana "Kaiconku! Harshenku a matsayinku na matan aure, amma har a makota ana jiyo ku, asararru wadanda ba su san mutumcin kansu da martabar da Allah Ya yi musu na matan aure ba". Ya dubi tulin aikin da suka tilawa Mairo yana salati, ya ce "Habiba waye zai yi miki wannan wankin?" Ta yi shiru, ya ce "Da ke nake magana fa". Ta soma rawar murya amma ba ta fasa tsiwa ba, ta ce "Au... to, kana nufin haka zamu aje gansamemiyar budurwa kamar Mairo sai dai mu tuka mu bata ta ci ta side hannu ta mike a katifa?" Ya ce "Ina almajirin da nake biya yake yi muku wankin?" Cikin rashin gaskiya ta ce "Bai zo ba". Ya ce "To kwashe kayanki maza-maza tun kafin mu sa kafar wando daya da ke, idan ya zo ya yi miki, ko ki tura 'ya'yanki su kirawo shi ya yi miki, amma bazan lamunci wannan rashin arzikin ba. Mairo ba baiwar uwar kowa ba ce a cikinku, wallahi-wallahi bazan yarda ku maidata baiwa ba. Bazan hanata ta taimaka muku da ayyukan gida ba, amma banda wankau da dakau. Ke Ladidi!" Ya kwala mata kira, ta fito a razane, "Zauna nan don ubanki, ku yi wanke-wanken tare ko in kwashe miki hakora yanzun nan". Ta ja kujera ta zauna tana zumbure-zumbure, suka soma wanke-wanken tare. Wannan tsayawa tsayin daka da Alhaji Abbas ke yi akan Mairo da al'amarinta, ya sayo mata matsananciyar kiyayya a gurin iyalansa, sun dauki tsanar duniya sun daurawa marainiyar Allah, daga su har 'ya'yansu, su suyi mata, 'ya'yansu su yi mata, amma ba zasu kwabe su ba. Barin Ladidi da ji ta ke da da hali, da ta cakawa Mairo wuka ta mutu kowa ya huta da bala'in Baffa a kanta. Kwana bakwai kacal da dawowar Mairo daga makaranta, duk ta bi ta kare kamar kudin guzuri, sai karan hanci da idandunan kadai, sabida rashin dadin rai da rashin kwanciyar hankali. Bata taba ganin mutane marasa imani da rashin darajja dan Adam irin Habiba da Hajara ba. Amma a kullum tana yi musu uzuri da yafe musu cikin zuciyarta. Ba kowa ne zai iya rike dan mutum ba a wannan zamanin, tunda dai sun yarda su zauna da ita, to ba zata kasa yi musu biyayya ba iyakar iyawarta. Wata mota kirar Kia-Rio ta yi fakin a kofar gidan Alhaji Abbas, misalin karfe goma dai-dai na safe. Lokacin Alhajin bai kai ga fita kasuwa ba. Nabilah Bebeji, ta fito daga mazaunin direba tana duba agogon hannunta, ta doshi kofar gidan Alhaji Abbas, tana mai addu'ar Allah dai Ya sa Baffan Mairo bai fita ba. Ta yi sallama a tsakar gidan, Habiba ta amsa yayin da ta bi ta da kallon mamaki. Sanye ta ke da atamfa mai karshen tsada shudiya ta karkata dauri mai ban sha'awa kamar nadin inji, a hannunta 'yar matsakaiciyar jaka ce, samfarin Louis Buittion da takalminta marar tudun dunduniya. In ban da kamshin turaren Rasasi (blue-royale) ba abin da ke tashi a jikinta, ta yane jikinta da gyale kalar atamfarta, daure a hannunta agogo ne shudi samfurin polo. Jiki na rawa Habiba ta dauko sabuwar tabarma ta shimfida mata, ta tsugunna har kasa ta gaishe ta, ta gaya mata ta zo wajen Mairo ne. A lokacin Mairon tana bayi tana wanka, cikin bakin-ciki karara Habiba ta yi mata nuni da dakin su Mairo kamar ba ita ce mai yi mata fara'ar da ta ke yi mata ba. Dakin tsaf ya ke, da yake Mairo ba ta wasa da tsaftarsa, sau dubu Ladidi zata bata, sau dubu zata gyara. Ta samu gefen katifar Mairo ta zauna, ta dauki wani littafi na Mairon da Mairon ta aje, da alama shi ta ke karantawa kamin ta shiga wankan na Dynasties the Ashtons (Condition of marriage), ta ce "Maryama na nan da karance-karancenta". Dai-dai lokacin da Mairon ta shigo, kanta na yararin ruwa domin wankan sallah ta yi, zata soma sallah. Ta harari Nabilah ta ce, "karfe taran ke nan?" Ta yi murmushi ta ce "Go-slow ya tare ni, amma ai na yi kokari, ke fa da sai yanzu kika yi wanka, ni tun asuba Momi ta tashe ni wai inyi maza in shirya in dauko mata Mairo ta ganta". Ta yi murmushi, ta ce "Yau dai da yardar Allah zan ga Momi". Ta ce "kwarai kuwa". Mairo na shiryawa Nabilah na kallonta cikin yin tazbihi ga Sarkin halitta da Ya kaga halittar Mairo. "MAIRO MATAR MANYA CE". Nabilah ta ayyana a zuciyarta. Wani irin jiki lukui-lukui kamar mai shiga wankan inji, ga kwantaccen gashi na fulanin usuli, wanda ke kwance lambam akan dogon wuyanta yala-yala da shi kamar ba zai kitsu ba, alhalin ba ta taba shafa masa relader ba koda wasa. Idanuwanta dara-dara, farare kal masu wani irin maiko da sheki (oily-eyes). Kai ita ba ta taba ganin mace mai lafiyayyen kugu da shafaffar mara irin Mairo ba. Kai ka ce idan ta sunkuya karyewa zata yi. Tana sharce kanta ta lura Nabilah kallonta ta ke, ta ce "Ke don Allah wannan kallon fa?" Ta ce "ke din ce, abun kallon ce Mairo, duk mijin da ya aure ki ya caba, ai ban san haka kike da kyau ba sai yau". Ta yi murmushi ta ce "Ni kuma ban taba ganin mai kyau irin naki ba Nabilah". Ta ce "Kayya! Gyara ne kawai Mairo, ina maganar natural beauty ne". Sai Mairo ta ja bakinta ta tsuke, ba ta kara cewa komai ba. Ta kammala shiryawa tsaf cikin atamfarta ta ganin sarki (Ghana wad), wani tausayi ya kama Nabilah, mace har mace, sai dai ba kayan ado, da da suttura ya ya za a ga Mairo? A hakan ma Mairo abin a juyo a kalla ce, ina ga ta samu

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66