Skip to content

Chapter 40

Chapter 40

Abari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

kallon Mairo, cike da fargabar Allah Ya sa ba ta jiyo abin da Yayanta ya ce ba. Ta ga hankalinta ba ya kanta, ya tafi ga lallashin Little Mairo ta ci abincin da ta ke ba ta da dan kankanin cokali. Ta godewa Allah da abin da ya darsu a ranta (mutuwar Amiru) ba shi ne ba. Ta kawo gwauron numfashi ta ce "Kano za mu taho ko Abuja?" Ya ce "Ku biyo jirgin Abuja, idan kun sauka ki kirani zan zo na dauke ku". Don haka a daren yau bakidayansa Dina ba ta samu isasshen barci ba. Tausayin Mairo ya cika mata zuciya. Irin yadda ta ke wahala akan karatun nan, ta kwallafa rai a kansa, kullum cikin ‘solving assignments' ace ya tashi a banza! Shekaru biyu cur! Sai dai kwarin gwiwar da ta ke da shi, shi ne Habibu ba zai kai 'yar uwarsa inda za ta tozarta ko ta wulakanta ba. Duk son da ta ke yi mata ta tabbata bai yi rabin-rabin wanda shi yake yi mata ba. Sannan akan Amiru ba abinda bazai iya ba. Da safe karfe takwas ta yi shirin fita don yi musu booking din tickets na jirgin ‘Lufthansa’ wanda zai tashi karfe goma na daren ranar. Sannan ta dawo, ta cimma Mairo ta fito daga wanka tana shafa akan stool ta ce (tana mai kawas da kai) "ki hada kayanki masu dan yawa, gida Najeriya zamu tafi, ban san kuma ranar da zamu dawo ba". Tana mai kawas da idanunta daga gare ta, don ba zata iya fada mata abin da Habibun ya gaya mata ba. Cikin mamaki Mairo ta ce "Me ya faru? Irin wannan tafiya haka unexpected?" Dina ta ce "Bai fada min ba, amma dai ya ce lallai mu tafi". Kamar ta yi kuka, ta ce "Ina da 'test' yau, kuma jibi za mu fara jarrabawa, kuma Yaya Habibu ya sani, yaya yake so in yi?" Dina ta ce "Hakuri za ki yi, haka Allah Ya shirya miki. Wani hanin ga Allah baiwa ne". *** J irginsu ya sauka a Abuja karfe biyar na asubahi. Ban da kunci da kumburi ba abin da Mairo ta ke yi. Dina sai lallabata ta ke tana ba ta hakuri. Idan takaicin ya yi takaici, sai ta kai hankici ta tsane hakwayen da ke 'racing' a fararen kundukukinta. Idan Dina ta ce "Ki yi wa Allah Mairo ki yi hakuri..." Sai ta ce "Haba Aunty Dina? Shekaru biyu ina wahala, in fadi, in tashi amma ace sun tashi a banza?" Wani farin dattijo, dan kimanin shekaru sittin da biyar, wanda alamun jin dadi, tsantsar ilimi da gogewar rayuwa ya boye shekarun nashi. Sanye cikin kaftan na wata irin farar sassalkar shadda da akalla ta baiwa naira dubu dari baya, yana da tsagin biyu-biyu a gefen fuskarsa na Fulanin Gaya. Biye da shi escort ne har guda biyu cikin bakaken suit wadanda harsashi na kowacce irin bindiga ba ya huda su, sun maka 'dark-spaces' fuskokinsu kamar hadari, sabanin dattijon wanda kyakkyawar fuskarsa ke yalwace da ni'imtaccen murmushi wanda da alama tabbatacce ne akan fuskarsa cikin kowanne yanayi. Abin nufi, cikin halin bakin ciki da farin ciki, kwanciyar hankali da tashin hankali, wannan sassanyan murmushin ba ya gushewa daga fuskarsa. A takaice dai na halitta ne, watau 'nature', shi ne a gaba wajen tarbar su Habibu a baya. Don haka kwarjininshi da haibarshi ya sanya dole Mairo ta daina kukan da ta ke, ta tsugunna har kasa ta gaida shi. Ya dora hannun damanshi a kanta ya ce "Barka da zuwa Maryamu. Godiya ga Allah da Ya sauke ku lafiya". Yaya Habibun kuwa ko arzikin kallo bai samu ba, sai matarshi ke binshi da kallon mamakin muguwar zabgewar da ya yi cikin kwanaki biyar kacal. Mairo ta sha mamakin ganin 'chebrolit' yau a gida Najeriya. Motar da ko a America, sai wanda ya ci ya tada kai. Ba wannan ne kadai ya razanata ba, sai tangamemen 'gate' irin wanda ake kira 'Mahdi ka-ture' da aka wangame musu a lokacin da motarsu ta sawo kai cikin unguwar Asokoro. Ta hango wani irin ‘American billa’ mai kama da jirgin ruwa. Ita dai Mairo ido ne nata, sai kuma ta cilla kafa duk inda ta ga an cilla. Tana cewa a ranta, watakila Yaya Habibu siyar da mu zai yi. Dama ni kudin nan nasa ai ban yarda da su ba. Sai dai kuma babu dar ko tsoro ko yaya cikin kalbinta, wadda ke cike taf da takaicin rabota da karatunta da aka yi babu gaira babu dalili. A kofar wani kayataccen falo mai kofar gilashi Yaya Habibu, dattijon da sauran mutanen da ke take mishi baya suka tsaya. Su kuma aka sa wata mace wadda ga dukkan alamu mai aiki ce, ta yi musu jagora cikin gidan. Ta nuna musu dakin da za su sauka, sannan ta sanar da su cewa, matar gidan tana asibiti, idan sun kimtsa su danna 'bell' za a shigo musu da abinci. Dina ce ta amsa, amma Mairo ta zama hoto. Dina ce ta fara yin wanka, sannan Mairo. Suka dauro alwala suka bada faralin sallar subhi da ta riske su a jirgi. Suka shirya tsaf, Mairo cikin 'swiss lace' ruwan madara da yarfin kananan duwatsu, riga da 'wrapper zani', ta yi 'simple' nadin kallabi a kanta. Dina cikin atamfar 'super' shudiya ita ma riga da zani da yalwataccen mayafi. A tsaitsaye suka ci abincin sabida kiran Yaya Habibu cikin wayar Dina cewa, su fito za su wuce asibiti. A babban asibitin koyarwa na Abuja, ita Mairo ta sha wajen matar gidan suka zo da ta ji an ce tana asibiti, sai raba ido ta ke cike da son ganin wace ce mamallakiyar wannan 'bungalow' din. Wanda aka yi amfani da hikima, ilmi da tunani wajen sarrafa shi. Kai ita a iya yawonta cikin U.S ba ta taba ganin irin wannan ginin ba, wanda ta fahimci cewa gidan wannan farin dattijon ne, da ya je tarbo su filin jirgi. Dattijon ne a gaba, sai 'escort' dinshi, sannan Habibu da Dina biye da shi, Mairo ce karshen shiga dakin, wanda ya kasance 'amenity'. Sabida cikowar da dakin ya yi da kyawawan mata masu kama daya, kuma masu kananan shekaru akalla daga mai talatin sai mai kasa da haka, sai kuma 'yammata tsararrakinta, wadanda ga dukkan alamu ko auren fari ba su yi ba, ta rasa inda tasan fuskarsu kamar ta sansu a wani wuri. Daga can gefe wata dattijuwa ce kyakkyawa cikin kyakkyawar suttura zaune bisa darduma, ta yi nisa cikin sujjadarta ba ta san me ake a dakin ba. Cikowar da dakin ya yi, shi yasa Mairo ba ta yi nasarar hango 'patient' din ba, wanda ke ta kelayo aman jini, har da guda-guda. Daya daga cikin matan ta rike shi tana kuka, sauran ma duk sharar hawaye suke yi da gefen mayafansu, wanda ke nuni da cewa kauna ce mai tsanani tsakaninsu da dan uwansu. Da sauri dattijon ya karasa gaban gadon ya tallafe shi cikin kirjinsa. Ya danna wani abu, da gudu likitoci biyar suka shigo. Nan suka yi umarnin kowa ya fita. Mairo dama tana bakin kofa, don haka ita ce ta farkon fita. Dattijiyar ma tana sallarta ko dagowa ba ta yi ba, su ma likitocin ba

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66