Chapter 50
Chapter 50
tausayi ba. kada ki fara ta kaina…...!!!” Kalaman sa sun gama kashe duk wani kuzarinta. Kwayar idanunsa sun gama kassarata. Ba yadda ta iya, dole ta zuro kafafunta ta fito. Zuciyarta na gaya mata ko akan titi Ameeru yakeso su rayu yau zata kasance tare dashi, gata dama da rarraunar zuciya, wadda ta afu ga son Ameerun with infatuation. A kwanaki ukun da suka yi cikin otel din 'Hyatt Regency' tamkar wani sabon babin amarci ne Amiru da Mairo suka balle. Mairo ta ga soyayya a gun Ameeru irin wadda a duk karance-karancen Novels dinta, ba ta taba katari da irinta ba, domin Amiru karshe ne, a fannin nuna soyayyah. A yau zai maida ita gida, domin jirgin karfe hudu na yamma zai bi zuwa gida Najeriya. Tunanin Mairo na yadda za ta fuskanci Dina ne da Yaya Habibu idan ya dawo ya ji ta bi miji, kwana da kwanaki ba a gansu ba. Har kuka ta yi saboda damuwa, don ta lura shi ko a kwalar rigarshi. Ba karamin tausayi da dariya Mairon ta ba shi ba. Don haka ya shiga lallashinta, yana nuna mata wannan ba wani abu ne na tada hankali ba. "Shi Yaya Habibu da Dinar ba daki daya suke kwana a gabanki ba? Su ba su ji kunyarki ba, sai ke ce mai jin kunyarsu akan haka?" Ta balla mishi harara cikin hawaye. Ya tarairayota ya rungume yana dariya, ya ce. "Shikenan ki barni da su, ni zan fitar da ke". **** Lokacin da suka iso gidan Habibu da Dinan ne suke 'lunch' tare da su Muhammad. Cikin bagararwa Yaya Habibu ya saci kallon Mairon da ke bin bango tana son ta shige dakinta, ya ce. "Ai na dauka kun wuce gida Najeriya ne?" Amiru ya yi dan murmushi, sannan ya ce. "Idan mun wuce ina ruwanka? Ni bana son aikin sa ido wallahi". Dina ta yi murmushi tana jinsu suna ta yi, Amirun na cewa. "Sa ido sana'ar banza, Yayan banza, Yayan kwabo". Habibu ya dube shi, ya ce. "Na ji dai, tunda ni dai mace ba ta taba kwantar da ni a gadon asibiti ba". To a nan ya kashe bakinsa, don bai kuma tankawa ba. *** C ike da himma Mairo ta dasa karatunta daga sabuwar shekara, duk da su Ir'eesh sun wuceta, ya kasance ta koma farkon shekara ta biyu. Habibu ya ba ta wayarta, bayan wadanda Amirun ya mallaka mata guda biyu irin wadanda ba ta taba gani ba. Don haka duk dare suna makale a waya suna fadawa juna how much they miss each other. Yadda ba ta iya sakewa su yi hira fuska da fuska, a waya idan ka ji su, sai ka sha mamaki. Kullum tambayarshi shi ne, har yau babu ajiyarshi ne? Da ya fadi hakan zata yi sauri ta kashe wayar, sabida kunya. To haka rayuwarsu ke tafiya, cikin so da kauna, ba sa taba gundurar juna. A Najeriya ne ko a Michigan, har Mairo ta kare karatunta, ta fiddo kwalin first class degree a B.Sc Sociology. Har zuwa wannan lokacin shiru, babu haihuwa babu alamarta, don ko batan wata Mairo ba ta taba yi ba. Tun abun na damunsu har suka hakura suka fauwalawa Allah. Sai dai kuma kamar yadda kowanne dan Adam ba ya rasa makiya, to hakan ce ta faru da Mairo daga dangin Amiru, musamman a Gaya da suka fara kishin-kishin Amiru ya auro musu juya, don ma Hajiya tana tsawatarwa ne amma har su Sabah sun soma sauya mata fuska. Aka soma yi wa Amirun tushen 'yammata, 'ya'yan gata, kyawawa wadanda suke ganin zasu iya gogawa da Mairon da duk abin da ta ke takama. Zuwa lokacin shi ma Habibu ya yi 'retire' daga 'barclays', haka Dina ta bar kotun da ta ke aiki. Sun tattaro da 'ya'yansu duka sun dawo gida Najeriya garin Abuja, cikin unguwar colorado close. Don haka Mairo cikin farin ciki ta ke, ga ta ga iyayenta, wadanda su ne kadai ta ke gani ta ji dadi, kasancewar Hajiyar ma ta soma daukar hudubar 'ya'yanta da 'yan uwan mijinta na Amiru ya kara aure. Daddy bai san abin da ke faruwa ba na matsalolin da Mairo ta soma fuskanta cikin gidan ba. A lokacin tana hidimar kasa a nan jami'ar Abuja, ta kai ga ko ta gaida Hajiya a ciki ta ke amsawa don gani ta ke Mairon ta mallake mata da, yadda har ba ya damuwa da samun dan kansa. (Matsalarmu ke nan al'ummar Hausa, babu ta yadda za a yi a ga mace na zaune lafiya da mijinta yana sonta, yana gudun bacin ranta, sai a ce ta mallake shi. An fi so a ji kullum yana kawo kararta ana yi musu sasancin sulhu, ko ya dinga aura yana saki, ko ya dinga aibatata cikin yan uwansa, Allah Ya sa mu gane mu gyara zuciyoyinmu, amin). A yau ne Amiru ya shirya musu 'wedding anniversary' na cikarsu shekaru biyar da aure. Taro ne da ya tara manya-manyan ma'aikatan bankunan Najeriya, bankunan kasar America, irin su World Bank, Barclays, Bank of America, Comerica, Citigroup, HSBC, Chase... da sauransu. Abokansu na karatu ne da yawa da suka watsu a wadannan bankuna suka gaggayyato. Taron wanda aka gabatar da shi a wani conference hall na 'hotel' din 'Nicon Noga' ya yi matukar yin armashi, kowane bako da maidakinsa, wato by couple'. Mairo da Amiru sun samu kyaututtuka na ban mamaki daga 'yan uwa da abokan arzikinsu. Kudi wannan tsurarsu da Mairo ta samu sun tasarwa lissafi mai girma, ba’a maganar sauran kadarori irinsu gidaje, hannun jari da sauransu. Daddy kadai abin da ya bayar ya girgiza kowa, wai! Ina wuta a jefa marainiyar Allah Mairo a wajen kannen Amiru, dangin Hajiya da dangin Daddy da suka zo daga Gaya. Sun sha alwashin idan Habibu a tafe yake yana tsaface musu Da ta yadda har ba ya jin shawarar kowa sai tashi, baya ganin owa nasa da gashi sai shi, to su a can suka kwan, kuma acan suka wuni. Gadararsu shi ne Amiru shi ne silar arzikinshi, wannan bai ishe shi ba, sai da ya kakaba mishi kanwarshi da a yanzu ta zame musu alakakai, karfen kafa. Don haka sun sha alwashin sai Amiru ya yi auran dangi, kuma sai sun raba shi da Habibun koda za su yi yawo tsirara ne. A wannan dan tsukin Mairo ba ta samun zama, sabida shirye-shiryen fara karatunta a 'Wayne State University' da ke Michigan. Komawa karatun da ya janyo mata kace-nace da dama har ta gwammace dama ba ta tarki zancen ba. Domin Hajiya ta kira Amiru kai tsaye ta fada mishi cewa ba ta yarda ba. Idan ba zata yi karatun a nan ba, to ta bar shi, amma sun daina daukar wannan rainin hankalin na Habibu da mace tana gidan aure zata tsallake ta tafi wata uwa duniya wai karatu. Amiru ya sha mamaki kwarai, don bai taba ganin ranar da wani sabani ya gitta tsakanin Hajiya da Mairo ba. Biyayya ta ke mata tamkar ta yi mata sujjada. Hajiyar da ke fada da shi idan ya batawa Mairo rai, amma yau ita ce ta ke mishi magana kamar ba ta taba sanin Mairon ba. Bai san ba abin da 'zuga' da 'karfar baka' ba sa jawowa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66