Skip to content

Chapter 28

Chapter 28

Abari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
Download Book

Sun kusa Yakasai Ladidi ta ce "Wallahi Mairo duk abin da kike so zan baki, ki rakani a zubar min da cikin, in Baba ya ji wallahi-wallahi kashe ni zai yi". Mairo ta ce "Ni kuwa mai za ki ba ni Ladidi in rakaki a kashe rai? Tukunna ma ni ban san inda ake zubar da ciki ba. Kin bata wayonki! Amma bana tausayinki, Baffa nake tausayawa. Iyakacin tarbiyya da ilmi ya baku, daga boko har na Arabiyyah, ya tsare muku cinku da shanku, da suttura dai-dai karfinshi. Bai cancanci wannan sakayyar daga gare ku ba….." Ta kai gefen mayafinta ta share hawaye, ta fyace majina, ta ce "Ladidi ke kuwa mai ya kai ki ga yin haka? Idan aure kike so mai yasa ba ki tsayar da daya cikin tulin samarin naki kin aura ba? Mai za ki ce da Baffa ranar da ya gane kin yi cikin shege?" Ladidi ta kufula wai Mairo ta ce ta yi cikin shege, ta ce "Kinga malama bana son wani dogon Turanci, idan ba zaki rakani ba ne mu raba hanya, wancan karon ma da aka ce na yi cikin ai nasan inda na je aka kwakule shi. Ko ance da ke kowa ma kidahumi ne, bakauye irinki? Mtsew!!!" Ta yayyaga takardar likitan da takardar maganin, ta ce "Ki je ki gayawa Baffan naki ya yi duk abin da zai yi kada ya barni da rai idan shi ne..........." Mairo ta sanya 'yan yatsu ta toshe kunnenta, ita kuma Ladidi ta tare dan A dai-daita sahu ta shige, ta ce, ya kai ta Sabon Gari. Tana shigowa gida Habiba ta ce "Ina kika baro Ladidin?" Ba tare da ta dubeta ba ta ce "Tana zuwa yanzu". Ta shige dakinsu ta danno kofa. Ta rasa inda zata sa kanta da tausayin Baffa. Ta soma kuka kamar ita ce abin ya faru a kanta. Wani sassanyan kamshi ya doki hancinta, irin wanda ba ta taba ji ba a rayuwarta. Daga nan ta jiyo muryar Baffa yana salati, yana sallamewa. Ta sake saurarawa sosai sai ta ji ya ce "HABIBU? Wa nake gani kamar Habibu?" Tamkar wadda aka cakawa mashi. Ta ji wani kululun bakin ciki ya taso ya soketa a kahon zucci. Amma hakan bai hanata mikewa ta fito ba, don gasgata kunnuwanta. Wani magidanci ne dan kimanin shekaru talatin da takwas, wankan tarwada, mai zarkadeden dogon karan hanci da yalwar idanu farare kal. Da ganin fuskarshi ka ga Malam Bedi, ta wani fannin kuma Alhaji Abbas sak! Yana sanye da kaftan na shadda Getzner kar-kar da ita, baka wul! Dinkin tazarce, sumar kansa a kwance luf baka sidik, kasancewar ba hula a kansa. Da gani babu tambaya, ka ga mutum da ya dama, ya kutsa cikin ilmummuka daban-daban. Wasu kyawawan yara guda uku, maza biyu da mace daya, sai rarraba ido suke na rashin sabo. Mairo dai tana nan rike da labule tana kallonsu, wasu irin hawaye suka zubo mata, ta yi saurin sakin labulen ganin zai juyo sashen da ta ke. Tana ji su Hajara duk suka firfito suna ta karadi da sallallami, ita kuwa ba ta kara lekowa ba. Mai ya dawo da shi cikin rayuwarsu yanzun? Bayan masu bukatarshi sun shude a doron kasa? Mai zai ce, mai zai yi, ya wanke mugun tabon da ya yi mata a zuciyarta? Mairo kuka ta ke tamkar ranta zai fita, ba ta son ganin Habibu ko kadan a rayuwarta. Gara ta bar gidan, kada ace da shi yana da 'yar uwa, mai zai yi mata wanda ALLAH da UNCLE JUNAID ba su yi mata ba? Ta soma harhada kayanta cikin jakarta da sauri-da-sauri, tana yi tana fyace hanci da hawaye duka. Ba ta ankara ba sai ji ta yi Baffa na kwala mata kira daga tsakar gida "Mairo! Mairo!! Ko Mairo ba ta nan ne?" Ta yi bakam, ta ki amsawa, ta jawo hijabinta ta zurma ta sungumi akwatinta ta yo waje, suka ci karo da Baffa a bakin kofa. Ya ce "Zo Mairo, yau ga Habibu Allah Ya dawo mana da shi". Ta sa kuka, ta ce "don Allah Baffa ka bani hanya in wuce, bana son ganinshi, ba abin da ya hada ni da shi. Idan dai zai zauna a gidan nan to ni zan koma wajen Nabilah". Baffa ya ce "Haba Mairo, waye ba ya kuskure? Ki dinga yi wa dan Adam uzuri cikin kowanne hali, uzuri sau saba'in, kafin ki kama shi da laifi. Ki saurare shi ki ji da wacce ya zo, sannan ki yanke mishi hukunci". Da haka ya lallabata suka nufi dakinshi, inda Habibu da su Habiba su ke. Habibu ya hada kai da gwiwa sai kuka ya ke, kamar karamin yaro. Ba kuma kukan komai yake ba, sai kukan jin rasuwar iyayensa daga bakin Habiba. Baffa ya fada su da fada kamar ya rufe su da duka "Ke kam Habiba ba ki ji dadin halinki ba, ko ruwa ba ki barshi ya kurba ba zaki ce Uwa da Uba sun mutu, gatsar, babu sakayawa, babu nuni da daukan hakuri da YAKANAH (Sunan Littafin TAKORI mai zuwa). Ku tashi ku fita ku ba ni waje, iyayen banza, wadanda ban san yaushe za su san Annabi Ya faku ba". Sum-sum-sum suka mike suka fita. Habibu ya dago kai yana kallon Mairo. Kyakkyawar budurwa ‘yar shekara sha takwas, wadda ya tafi ya bari tana shekaru takwas. Ita ma ta kalle shi cikin ido, sai kuma ta dauke kanta. Ta daure fuska sosai. Ya ce "Mairo Yaya Habibun?" Sai ta fada jikinsa ta sa kukan da ke cinta a zucci. Allah Ya riga ya halicci zuciyarta da kaunar Habibu, babu yadda zata yi, shi ne dolenta a rayuwa. Suka rungume juna suka yi ta kuka, Baffa ma tunanin dan uwansa ya dawo masa sabo. Ya soma share ido da habar babbar rigarsa. Sai da suka yi kukansu mai isarsu, sannan Baffan ya soma lallashinsu. Ya ce "Ni ina nan Habibu, zan zame muku uwa, uba, kuma abokin shawara. Dukkaninmu na haka ne, kowa jiran wa'adinsa ya ke". Habibu ya ce "Kaicona Baffa! Dukiyar da na zauna ina tarawa don Baba ya daina noma, Inna ta daina girki da icce, Mairo ta yi karatu mai kyau sun tashi a banza! Na kintata ne zuwa sanda zata gama sakandire sannan in dawo, ashe bazan tadda Baba da Inna ba, sannan Mairon ba ta ji dadin dawowata ba!!" Baffa ya ce "Wai haka Mairo? Ba ki ji dadin dawowarsa ba in sallame shi?" Ta yi murmushi, ta sake sunne kanta a kirjin Yaya Habibun. Ya ja karan hancinta, ya ce "Ko kallon 'ya'yanki ba ki yi ba, balle mai sunanki, mai kama da ke". Sai a lokacin hankalinta ya koma ga yaran. Cikin murmushin kaunarsu da ta mamaye zuciyarta farat daya, ta ce "Ya'yanka ne Yaya Habibu?" Ya gyada mata kai, "Ya'yana ne. Na yi aure da mamarsu tun sanda na kammala karatun digiri na farko. Ga Abbas, ga Muhammad (Bedi), sannan ga Mairo". Baffa ya yi murmushi, ya ce "Taho takwarana". Abbas ya matsa gare shi, dan kimanin shekaru hudu, Muhammad shidda, Mairo kuma 'yar shekara biyu ce. Babban wato Muhammad ya ce "Daddy wannan ne Babanka?" Ya ce "Eh, shi ne Babana". Ya kuma cewa, "Wannan ce Aunty Mairo?"

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66