Chapter 27
Chapter 27
tasan ko ta karba rabon su Ladidi ne, dama ace za su gode ne, to a'a, zagi da bakar magana ne zai biyo baya. Hajiyar ta ce "Ni ba babarki ba ce? Ba zan yi miki ihsani ki karba ba?" Ta sake kai dubanta ga Uncle Junaid da ke cikin hoto yana murmushi. Sai ta ga kamar ya turbune mata fuska, cikin rashin jin dadi. Ta maido ga dubanta ga Hajiyar, kallonta ta ke tsakaninta da Allah da matsananciyar kauna cikin kwayar idanunta. Ji ta yi kamar ta kwantar da kai a kafadunta ta yi kukan da ke cin ranta, ta gaya mata matsananciyar kaunar danta da Allah Ya dora mata. Ta ji dumin da Junaid ya ji, a jikin wannan nagartacciyar UWA, ganin hawaye na neman tona mata asiri ta yi hamzarin karba ta ce "Na gode". Har ta kai bakin kofa zata fita, Hajiyar ta kirata jikinta a sanyaye, don daga dukkan alamu akwai abin da ke damun wannan yarinya, ta ce "Har za ki tafi, ba ki gaya min sunanki ba, idan Ilham din ta yi waya in gaya mata". Mairo ta ce "Ki ce mata Maryam ce". "Maryam-Maryam!" Tana ji a bakin su Ilham, amma a wannan karon Allah bai bata ikon ganewa ba. Har yarinyar ta fita, ba ta motsa daga inda ta ke ba, ta dade tana tunanin inda tasan yarinyar. Mai yasa ba ta tambaye ta daga inda ta ke ba? To akan me zata tambaye ta? Don kwaita zo wajen Ilham? Amsar shi ne, don zuciyarta tana sonta. Ta koma falon ta zauna cike da tunani. Sai ana kiran isha'i ta iso gida, Baffa na alwalar sallah a nan kofar gida, ta tube takalminta sannan ta wuce shi, zuciyarta cike da jin haushin dadewar da ta yi. Ya ce "Ban ce kada ki kai dare ba Mairo?" Cikin matsanancin ladabi ta rausayar da kai tace "Ka yi hakuri Baffa, mota ce ban samu da wuri ba". Ya ce "Ni dai duk inda za a je aje ido na ganin ido, amma bana son ayi dare. Idan kin shiga ki turo min Lawan". Ta ce "To". Habiba na kwasar tuwon dare sanda ta shigo, ta dago kai ta dube ta a ranta ta ce, "Kai wannan yarinya da kashin arziki ta ke, kullum ta fita ba ta dawowa haka nan, sai bakin jini har yau babu wanda ya taba sallama da ita, duk kyawun nan nata. Ladidi kuwa kullum idan mutum biyu ba su yi sallama da ita ba, hudu za su yi". Ta dubi Lawan wanda ke bin ledar hannunta da kallo, ta ce "Ka je Baffa na kira". Ya ce "In an ki fa?" Ba ta yi magana ba ta wuce wajen Habiba ta durkusa ta ce "Mama Na dawo, sannunku da aiki". Lawan ya ce "Wani feleke wai 'Baffa', mu 'Baba' mu ke cewa Babanmu, ba wani Baffa ba. Wai mama yarinyar nan ta fara bin maza ne ta ke shigowa gidan nan da manyan ledoji?" Habiba ta ce "Idan ta bi sun ina ruwanka, ko mace ba don namiji aka halicceta ba? Me muka samu ne Mairo? Miko nan in gani". Ta mika mata ledar ta tusa karkashin kujerar da ta ke zaune kada Hajara ta fito ta gani, ta ce sai an raba da ita. Ta dauki tuwon da ta saka mata a wani kwano duk lamba, ta zuba miyar karkashi akai ta mika mata. Ta karba ta wuce daki cike da takaici. Ashe wani takaicin ke jiranta. Tana sanya kai dakin wani mugun karni ya dake ta. Ladidi ta kelaya amai tun daga bakin kofa har bakin katifarsu. Tana kwance a katifa tana barci kamar mushe ba abin da ya dame ta. Ta fita ta dauko tsintsiya da abin kwashewa ta soma aikin aman kamar zuciyarta ta yo waje don bakin ciki. Tuwon da ba ta iya ci ba ke nan sabida karnin da dakin ke yi, haka ta kwana da yunwa. Washegari Ladidi da kanta abin duniya ya ishe ta, ta rarrafa katifar Mairo ta tashe ta, misalin karfe bakwai na safe. Mairo ta bude ido tana kallonta, yawu ya ciko mata baki ta juya bayan kofa ta tsartar ta ce "Zo ki raka ni asibitin don Allah, na kasa gane abin da ke damuna, amma da gaske ba ni da lafiya". Sai Mairon ta ce "Ki fara zuwa ki tambayo mama tukunna, idan ta amince sai na rakaki". Ta ce "Rabu da ita kawai, zo mu fice tana daki". Mairo ta ce "A'ah, ba za a yi haka da ni ba". Ba da son ran Ladidin ba ta fita ta tambayo Habiba za su je asibiti. Habiba ta dubi diyarta ta ce "Bana so ku dinga jerawa ne kada a ga muninki". Ladidin ta kyabe baki, ta ce "Lallai ma Mama, ni ce ma mummunar?" Habiba ta ce "Sai idan ba ku jera da wannan mai kama da aljannun ba". Ladidi ta ce "Ke wannan ya dama, ni da munin nawa dai ai na fi ta farin jini, kin taba jin ko bera ya aiko yana sallama da ita?" Ta ce "Haka kuwa, ku je sai kun dawo". Suna tafe a gefen hanya har asibitin Murtala, Mairo ta yanko mata kati suka hau layi. Suna nan zaune har aka kirasu 7/30/21, 10:24 PM - Kawata: 98 Likitan yana rubuce-rubuce a file lokacin da suka shiga, Mairo ta tsaya ta harde hannuwa a kirji a bakin kofa. Ladidi ta karasa ta zauna a kujerar da marasa lafiya suke zama. Ya gama ya dube ta ta karkashin gilashinsa ya ce "Me ke damunki?" Ta ce "Ina fama da haraswa, zazzabi da ciwon kai mai tsanani, ga wani yawu da yake taruwar min a baki, bana jin dadin bakina". Likitan ya dau abin awonsu ya sanya a hannunta yana sauraro, sannan ya yi rubutu a wata 'yar takarda ya ce, su je laboratory su kawo masa result. Suka fita suka tambayi lab aka nuna musu. Nan aka bai wa Ladidi robar fitsari aka ce ta je toilet ta yi ta kawo. Nan da nan result ya fito suka koma ofishin likita. Ita dai Mairo tunda ta ga an rubuta positibe hankalinta yai matukar tashi. Likitan ya dube su bayan ya duba takardar ya ce da Ladidi, "Ina mijinki?" Ladidi ta ce "Ba ni da aure". Ya kura mata ido na 'yan sakonni ya ce, "Amma you are pragnant,(kinada juna biyu) watanni biyu cif?" Ladidi ta fiddo 'yan idanunta gaba daya suka yi kuru-kuru, wannan bai damu likitan ba ya ci gaba da aikin da ke gabansa bayan ya rubuta mata magani a wata 'yar takarda. Suka fito jikin Mairo har rawa yake, saboda dimuwa da razana, ita kuwa Ladidi in banda kuka ba abin da ta ke, wai likitan sharri yai mata, duk girman kan nan ta sauke shi tana rokon Mairo wai su je wani asibitin a sake dubawa. Mairo ta sa mata ido, ta ce "Wannan asibitin specialist ne, duk Kano daga Aminu Kano sai shi, hakikanin gaskiya suka gaya miki. Don haka ni babu inda zan kuma zuwa". Ta yi shiru hawaye na zubar mata. Ba tausayin Ladidi ta ke ji ba, tausayin Alhaji Abbas ne, bawan Allah, Baffa bai cancanci 'ya'ya irin wadannan ba.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66