Skip to content

Chapter 3

Chapter 3

Abari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

abada! Amma bazata iya jure bukatar gangar jiki da zuciyarta ba irin na kowanne lafiyayyen dan Adam. In hakane aure ya zama dole a gareta domin kare kanta daga _zina_ , da sauran ayyukan alfasha, cikar mutunci a idon duniya da karuwar matsayi a fadar Ubangiji. Wayarta dake karkashin filo ta soma dan kidi mai sanyi, alamar shigowar sako (text ). Cike da mamakin wanda ya yo mata sako a daidai wannan lokacin karfe biyu na sulusin dare agogonsu na can ta mika hannu ta lalubo wayar ta danna. Bata san lambar ba don kuwa bakuwa ce, ga abinda ke rubuce; ".......... _When life changes, and we go our separate ways, you will still be in my heart till my dying days...... my world has never meet a person like you!"_ (A yayin da rayuwa ta canza ni da ke muka bi hanyoyin mu mabambanta (muka rabu) zaki cigaba da zama a xuciyata har karewar numfashi na. Duniyata bata taba haduwa da mutum irin ki ba). Haka ta sa sakon a gaba tana ta karantawa har akayi kiran Assalatu. Don ta tabbata ba kowa bane; Amiru ne. Duk da bai saka suna ba ko wata alama mai nuna shi din ne. Allah sarki! Har YA HUCE ne? Tana so ta bashi amsa bata san me zata ce masa ba. Da safe take nunawa Dina a kitchen, ta karanta tayi dan miskilin murmushin nan nata. Tace "ke kuma kika ce me?" Ta zumburi baki "ni ko kula sa ma na yi?" Dina tayi dariya tana kwaikwayon muryar ta tace "Haba Mairo! Yi hakuri ki dan kula sa. Kin ga shi yayi fushin amma ya sauko, sabida ya fahimci Mairo ba sonsa bane bata yi, kawai ita din mai *amana* da *rikon alkawari* ce". Tayi murmushi har kumatunta ya lotsa. Dina kam akwai shegen wayo, kanwa ce uwar gami. Tace. "To me zan rubuta???" "Ki ce kawai yazo yayi _joining_ dinmu _breakfast_ ". Mairo ta rubuta ta tura. Amsar da ya bata ta sa ta yin murmushi, domin ya ambato rabin ranta. "A'ah kirawo JUNAID......" " He's far away....!_ " (Amsar Mairo). "And I'm not closer too.... I'm far away either, and I will not come back. On my way to Detroit-Metro". Hankalinta yayi mummunan tashi. Saboda ita ne Amiru zai bar kasar da haihuwarsa ne kawai ba'ayi cikinta ba? Da sauri ta jefar da wayar. Da gudu tayi daki ta dauko mukullinta. Dina na kira amma bata juyo ba take fadin. "Shima zai tafi ya barni, kamar yadda Junaid ya gudu ya barni. Bayan sun kimsa min soyayyarsu. Banaso in samu wannan _heartbreak_ (karyewar zuciyar) a karo na biyu". Dina tace. "Bi shi Mairo. Shine ZABIN ALLAH!!!" Gudu take shararawa a kan titin da zai kaita _airport_ din Detroit. Cikin kankanuwar motarta *GMC Terrain.* Hawaye na sauka akan kundukukinta. Da gaske Dina ta ke; wannan itace SOYAYYAH! Da gaske Dina ta ke Amiru shine ZABIN ALLAH! Da gaske Dina ta ke da tace ta kama mai sonta, ta rabu da *JIRAN TSAMMANIN WARABBUKA!* Ta karbi *soyayyah* a hankali zata rikide ta zama *kauna* . To ga shi soyayyar ma zata gudu ta barta da tsammanin warabbukanta wanda bata fata. .........................!!! Koda Ta iso airport din ko kulle motar bata yi ba, a jikin motar ta bar mukullin. Da gudu ta shige cikin _reception_ tana dube dube. Babu Amiru babu ko mai kama da *AMIRU* ! Ta karasa _terminal_ bayan ta hankade ma’aikacin dake kokarin hanata shiga. Daidai sanda anka rufe kofar jirgin ( _Lufthansa_ ) wanda zai tashi zuwa kasarmu mai dimbin albarka. Ba da jimawa ba kuma ya soma ruguginsa mai gigitarwa bisa kwaltarshi, kafin ya daidaita sosai a sararin samaniya. Mairo ta durkushe anan tana kuka. Kukan da ta dade batayi irinsa ba tun bayan rashin BABANTA da INNAR TA. Fita yake tun daga karkashin zuciyarta. Amiru ya tafi tareda dukkan farin cikin data samu cikin *Michigan* wanda Yaya Habibu ya dade kafin ya assasa. Bai shigo rayuwarta da sauki ba ashe! Ashe ya shigo ne ya kara rusa komai. Ya tafiyar da sauran karfin zuciyarta. Ya dawo da rayuwa *unbearable* kamar kamar uncle Junaidun? Me yasa ita bata da sa'a a soyayya komai kankantarta??? Ji tayi kamar an tsugunna a gabanta, kamin ta dago kuma an kai hannu a hankali an dafa kafadarta. A sannu ta dago idanunta jage-jage da hawaye, don ganin ko wanene wannan??? *A BARI YA HUCE* . ...... Littafin *_Sumayyah Abdulkadir Takori*_ _Wannan littafi tukuici ne ga masu sha'awar ganin rubutun TAKORI a yanar gizo. Ga mai son cikakken labarin (book 1-4) ya biya N1000 ga wannan account number_ *Sumayyah K Kabara* *Zenith bank* *2089357770* _Sannan sai ya turo screenshot zuwa 07030137870_ NAGODE 7/28/21, 10:59 AM - Buhainat😝: KAUYEN GURIN-GAWA, 1988 Gurin-gawa karamin kauye ne mai tsohon tarihi da ya kunshi al'umma masu sana'o'i daban-daban, amma duka tushensu daya. Galiban malamai ne da manoma, kuma kauye ne da manyan malaman da a halin yanzun suka barwa duniya abin da ba za a mance da su ba suka fito. Gurin Gawa na nan cikin karamar hukumar Kumbotso, yankin Fanshekara ta jihar Kano. Karamin kauye ne, wanda ya samu tallafin gwamnati ta hanyar wutar lantarki, ruwan sha mai tsabta, da takin zamani, wanda ke taimaka musu kwarai wajen bunkasa harkar nomansu. Akwai sanannen hadin kai tsakanin al'ummar garin mazansu da matansu. Sai dai kuma babu titi mai kyau a Gurin-Gawa. Idan mota ce zata shiga kauyen sai ta yi futuk da kura, mutanen cikinta sun gwaggwara kawunansu sabida rashin kyawun birjin. Duk da haka wannan bai hana al'ummar cikinta jin dadin zamanta ba, motar haya ba ta shiga cikin kauyen, sai dai ta aje ka a titin ka hau achaba ko bayan akori-kurar Rake ta mutanen garin ka karasa ciki. Don haka da wuya ka ga mutanen birni na shiga kauyen, don a ganinsu ba su ga mai zasu tsinto cikin wannan kalataccen kauyen ba. Samarin garin Gurin-Gawa kan fita cikin Fanshekara da wajenta domin neman kwabo, ta hanyar ga-ruwa, sayar da rake, dukanci, dako da sauransu. Don kalilan ne suka damu da makaranta wadda dama idan dai ta boko ce, to ba a zancenta cikin garin Gurin-Gawa. Makarantun allo da na Buzu su ne Allah Yai yawa da su a garin. Malam Bedi, yana daya daga cikin dattawan garin Gurin Gawa, haifaffen nan ne iyayensa da kakanninsa. Sana'arsa shi ne noma, yana da gonar rake da gyada, sannan yana nome dankalin Hausa, makani da gurjiya. Bedi da matarsa Hure, fulanin Gurin-Gawa ne na usul. Mutanen kwarai ne da duk Gurin Gawa ba wanda bai sansu ba, tare da yi musu kyakkyawar shaida. Babban dansu shi ne Habibu, wanda tun yana karami Malam Bedi ya dankawa kaninsa mai bi masa a haihuwa ya ke taya shi sana'ar fataucin goron da yake yi daga Shagamu zuwa Kano, wanda daga baya shi Habibu ya shiga makarantar horas da malamai (SAS) tun daga wancan lokacin kuwa ya koma Kano kwata-kwata. Shi da Gurin-Gawa sai dai yazo da yawo idan ya zo gaida mahaifansa wanda yakan dauki dogon lokaci bai yi hakan ba. Su ma su Malam Habibu ba su wani damu da shi ba, don ba wata cikakkiyar shakuwa ce a tsakaninsu ba. Duk wani burinsu na duniya yana

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66