Skip to content

Chapter 36

Chapter 36

Abari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
Download Book

daga baya rikidewa ya ke ya koma soyayya. Kuma dama ita irin wannan dadaddiyar soyayyar ba a fiya auren juna ba. Wasu ma har su mutu, ba sa kara ganin juna. Wasu kuma daya ne yake mutuwa ya bar dayan cikin soyayyar, kuma babu yadda dayan zai yi, a karshe dole zai hakura ya auri wani, wasu kuma hakura suke da auren har zuwa sanda nasu ajalin zai riske su. Amma Ubangiji ba ya son hakan, don haka bana son ki zamo daga cikin wadanda za su kyamaci sunnar Ma'aiki sabida soyayya. Manzon Allah (S.A.W) cewa ya yi "Ku yi aure don ku hayayyafa... Bai ce ku yi aure don soyayya ba. Karewama, duka matan ma'aiki da dalilin da ya yi sanadin da ya aure su, ba soyayya ba. Soyayyarsu tana kafuwa ne a hankali cikin gidan aurensu. Ki yi koyi da Nana Khadijah wadda halayen amana na Ma'aiki ya kwadaitar da ita ga son aurensa, shi ma kuma ya aure ta don dukiyarta, addininta da nasabarta. Ki auri Amiru don yana da nasaba, addini, ilmi da arzikin ma, ku raya sunnah ku haifi 'ya'ya ku yi musu tarbiyyar musulunci in gaya miki karshen soyayya ke nan. Ke nan har wata soyayya kika sani ko halarci? Wallahi HALACCI kike yi mawa ba SOYAYYA ba. Amirun shi kike so da gaske, na gani a kwayar idonki, na gani a gangar jikinki. Kina jin abubuwan da kike ji kan Amiru a Uncle Junaidun? Kina neman Junaid ya aure ki ne don ya tallafi rayuwarki a lokacin da kike neman matallafi, amma ba don kin san hakikanin me aure ya kunsa ba. Kina so ki ramawa Junaid halaccin da ya yi miki ne ta hanyar 'aure' don da shi kika saba, ya sanki, kin sanshi, a tunaninki wannan shi ne karshen soyayya, to ba shi ba ne, soyayyar aure daban ta ke, Allah ke hadata, kuma bata fassaruwa. Haka ita ma kauna daban ta ke, sai kin auri Junaidun za ki ji kamar kin auri Babanki. A sa ma shi din ya ce yana son naki, balle bai ce ba. Tsayin shekara biyun nan wallahi da duk inda kike ya neme ki, da fa ya damu da ke. Ita zuciya an halicce ta ne da son mai kyautata mata, wannan shi ne tsakaninki da Junaid ba soyayyar aure ba. Idan kuma mata sun fara zuwa neman aure ne, to sai mu je gidansu mu neme shi mu kai kudin aure, mu gaya mishi yadda kike sonshi har kina gayawa masu sonki da auren, ke ba kya sonsu, sabida kar ki ci amanar soyayyar sa da ya ba ki…..." 8/2/21, 10:31 PM - Kawata: G Ala dole ta murmusa, don tasan zambo ne take mata. Duka wannan bata lokacin da Dina ta yi tana bayani, ba duka abin da ta ce ne ta yarda da su ba. Ta dauki Dina a matsayin mai campaign ga Amiru, sabida shi ta sani, shi ne mai irin tsarinm rayuwarsu. Ita kudin Yaya Habibu ma tsoro ya ke bata, balle na Amirun da ta sha jin suna cewa yana world bank, karewar Barclays. Ta yarda ta hakura da Junaid sabida kwararan hujjoji masu karfi da kowa yake gaya mata, hatta Nabilah. Ta ce da ita lokaci ya yi da ya kamata ta manta da soyayyar da ta ke wa Uncle Junaid ta yi aure. Ta dubi irin auren da ita ta yi, amma ga shi ya zame mata ALHERI, don yanzu ba abin da ta ke so a duniya sama da mijinta, kuma shi ma hakan har ga albarkar haihuwa. Ta sauke ajiyar zuciya, ta koma ta kwanta a gadonta, ta ja bargo har kanta. Barci ta ke so ya zo ya dauke ta, amma ya ki zuwa. Al'amarin na neman tarwatsa mata kwakwalwa, tareda wargaza mata tunani. Tana son ta yarda da Dina, halaccin da ke zuciyarta na karyatawa. Amma abubuwan da ta zana ai duk haka suke, zata je neman auren Uncle Junaid ne? Ko haka zata kare da zaman jiran tsammanin warabbuka? Zata iya ci gaba da zaman jiran ranar da Junaid zai neme ta, ya bayyana mata soyayyarshi, ya ba ta uzurin da ya hana shi yin hakan har nan gaba da abada. Amma ba zata iya jure bukatar gangar jikinta da zuciyarta ba, kamar kowanne lafiyayyen dan Adam. Idan haka ne tana bukatar aure, domin kare kanta daga ZINA, da sauran ayyukan ALFASHA, cikar mutunci a idon duniya, da karuwar matsayi a fadar Ubangiji. Wayarta da ke karkashin filo ta soma dan kidi mai sanyi, alamar shigowar sako (text). Cike da mamakin wanda ya yo mata sako a dai-dai wannan lokacin, karfe biyu na sulusin dare agogonsu na can. Ta mika hannu ta lalubo wayar ta danna, ba tasan lambar ba, don bakuwa ce. Ga abin da ke rubuce. '... When life change, and we go our separate ways, U will still be in my heart till my dying days... My world has never meet a person like U……...! (A yayin da rayuwa ta canza , ni da ke muka bi hanyoyin mu mabambanta (muka rabu), za ki cigaba da zama a xuciyata har karewar numfashi na. Duniyata bata taba haduwa da mutum irin ki ba). Haka ta sa sakon a gaba, tana ta karantawa. Har aka yi kiran assalatu. Don ta tabbatar ba kowa ba ne, Amiru ne, duk da bai sa suna ba. Allah sarki ko YA HUCE ne? Ta fada a fili. Tana so ta ba shi amsa, ba ta san me zata ce masa ba. Da safe ta ke nunawa Dina, ta karanta, ta yi dan miskilin murmushinnan nata, ta ce. "Ke kuma kika ce mene?" Ta zumburi baki. "Ni ko kulasa ma na yi?" Ta yi dariya, ta na kwaikwayon ‘yar muryar ta tace, "Haba Mairo? Yi hakuri ki dan kula sa. Kinga shi ya yi fushin amma ya sauko, saboda ya gane ba son sa ne ba kya yi ba, kawai ke mai aminta amana da alkawari ce!". Ta yi dariya har kumatun ya lotsa, Dina kam akwai shegen wayo, kanwa ce uwar gami.. Ta ce "To me zan rubuta?" "Ki ce kawai ya zo yayi joining dinmu break fast…..". Ta rubuta ta tura, amsar da ya ba ta ta sata yin murmushi. Domin ya ambato rabin-ranta (uncle Junaidu). "...A'ah kirawo Junaid….". "He is far-away...!!"(Amsar Mairo ) "And am not closer too... am far-away either, and I'll not come back...!!! On my way to Detroit Metro…...". Hankalin Mairo yayi mummunan tashi, da sauri ta jefar da wayar, da gudu ta yi daki ta dauko mukullinta, Dina na kira amma ba ta juyo ba, cikin rishin kuka ta ce. "Shi ma zai tafi ya barni, kamar yadda Junaid ya gudu ya barni. Bayan sun kimsa min soyayyarsu. Bana son in samu wannan heart break (karyewar zuciyar) a karo na biyu". Dina ta ce "Bishi Mairo, shi ne ZABIN ALLAH!!" Gudu ta ke shararawa akan titin da zai kai ta airport din Detroit. Cikin kankanuwar motarta GMC Terrain. Hawaye na sauka akan kundukukinta. Da gaske Dina ta ke, Wannan ita ce soyayyah! Da gaske Dina ta ke, Amiru shine zabin Allah!! Da gaske Dina ta ke da ta ce ta kama mai sonta, ta rabu da JIRAN TSAMMANIN WARABBUKA.

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66