Chapter 30
Chapter 30
wujiga-wujiga da ita, ba wanda ya ga shigowarta sai Mairo don duk sun yi barci, ta lallaba ta kwanta a katifarta, ga dukkan alamu ta je an cire mata cikin. Ladidi sai ta daina bai wa Mairo mamaki, ta koma ba ta tsoro. Washegari ta shirya ta yi wa yaran wanka ta shirya su, Hajara ta ba su abin kari koko ne da kosai da agada, da suka kammala suka tadda Habibu a dakin Baffa suna kalaci shi da Baffan. Yaran suka nufi Babansu suka baibaye shi, ya ce "Ba ku gaida Baffa ba Muhammad". Suka hada baki suka ce, "Baffa ina wuni?" Ya ce "Ina kwana dai takwara na, kamar ba haihuwar Turai ba, Hausa ras a bakinku". Habibu ya ce "Ai ni bana yi musu Turanci, Mamarsu ce ta ke musu. Ita ma ina hanata don kowa yabar gida gida ya barshi". Baffa ya ce "Wannan haka ya ke, Allah Ya raya mana su cikin addinin islam, amin". Suka bar yaran wurin Habiba, suka nufi Immigration office, can hanyar farm center cikin dan lokaci aka yi wa Mairo passport aka ce su dawo bayan kwana uku su karba. A hanyarsu ta dawowa Habibu yana tuki cikin nutsuwa Mairo tasa ido tana kallon shi yana burge ta, ya yi kyau ya yi girma, ya zama ingarman cikakken mutum ma'abocin kwarjini na musamman da cikar zati. Ta fadi a ranta gaskiya wannan Dina ta caba miji. A ranta kuma tana kissima shin ita kuma Dinar yaya zata kasance? Jikinshi ya ba shi Mairo kallonshi ta ke, ya yi wani irin murmushi mai ban sha'awa har fararen hakoranshi suka fito. Ya dan juyo ya ce "Ya ya dai Mairo? Irin wannan kallo haka? Ko na yi kama da saurayinki ne?" Kunya ta kama Mairo, ta rufe fuska tana dariya, "Ni ba ni da wani saurayi. Ka yi kyau ne da yawa Yaya Habibu, ka zama babban mutum mai ban mamaki, don Allah mai Anti Dinar nan take ba ka ne?" Ya yi murmushi ya kai hannun hagunshi ya shafi kwantacciyar sumar kanshi, ya ce "Soyayya ta ke ba ni Mairo. Duk wata kauna ta duniya Dina ta ba ni tun a lokacin da nake dalibi, ba ni da komai, ba ni da ko kwabon da zan aure ta, a matsayina na dan kauye da matsayinta na diyar Ambassador. Habibun kawai ta ke so ba wai wani abu da Habibun ya mallaka ba". Mairo ta ce cikin zuciyarta, "Kamar ni da Uncle Junaidu". Ba tasan cewa furucin ya subuto ya shiga kunnensa ba 7/31/21, 8:31 PM - Kawata: 990 Ya rage gudun motar ya dube ta sosai, hawaye ne fal idanunta "Kika ce mun ba ki da saurayi, Mairo". Ta kai 'yan yatsu ta share hawayen idanunta "Kuka Mairo? Mairo me ya sanya ki kuka?" Ba amsa, karewa ma, sai ta soma shesshekar kukan sosai. Ya sauka gefen titi ya kashe motar. Ya mika hannu ya kama hannunta, ya damke cikin nasa "Daga yau ba zaki sake kuka ba Mairo, tunda ga ni. Babu abinda Allah bai mallaka min ba. Gida a America, gida a Abuja, motocin hawa sai wadda ranki yake so. Ga babban aiki da BARCLAYS BANKS, ga takardun ilmi har zuwa PhD, wanda nake da yakinin daga mu har jikokinmu da 'ya'yan jikokinmu babu mu babu talauci. Jami'a sai wadda kika zaba cikin kasar America. Gaya min wane ne Junaidu? Ni kuwa in aura miki shi ko shi ne beran masallaci sabida talauci, ko shi ne Bill Gates sabida arziki, amma fa sai idan yana da ilmi, ya kuma yi alkawarin zai rike min ke da amana". Mairo ta sunkuyar da kai, ta ce "Ai bai taba cewa yana sona ba!". Habibu ya ce "Ke ce kike sonshi ke nan?" Ta ce "Ni ma ban sani ba ko son nasa nake yi. Alherinsa da kyautayinsa masu yawa ne a gare ni. Ya tsaya tsayin daka akan karatuna, ya tsaya tsayin daka akan lafiyar Baba da Inna, ya ce nima cikakkar mutum ce a lokacin da nake jin kaina cikin inferiority compled. Don haka bazan iya ce maka Uncle Junaidu saurayina ba ne, sai dai duk duniya babu wanda nake jin zan iya aure sai shi…...." Ta shiga baiwa Habibu labarin tun bayan tafiyarsa, yadda akai ta je FGGC, haduwarta da Junaid, Kausar da su Nabilah, saran da maciji ya yi mata, ba da jininsa da ya yi gare ta, karfafa mata gwiwa da kwarin gwiwar da yake ba ta a karatunta, amanar da Malam Bedi ya ba shi a kanta, tsayawa da ya yi akan lafiyar iyayensu, har zuwa gama makaranta da nemansa da ta yi ranar candy ba ta ganshi ba. Ta kare labarinta da ba shi labarin zuwansu karbo sakamakonsu a makarantar inda aka gaya musu ya tafi karo karatu Russia. Ta dakata ta share hawaye, ta cigaba da ba shi labarin zuwanta gidansu wajen mahaifiyarsa, amma ba ta gaya mata ko ita wace ce ba. Habibu ya yi shiru, cikin zuzzurfan tunani na ma'abota hankali. Ya rasa ta inda zai bullowa al'amarin Mairo. Tabbas soyayya ke dawainiya da kanwarshi tilo, ba tareda ita din ta sani ba. Dole ya tsamota, ya ba ta (hope) na yadda zata manta, ta fuskanci sabuwar rayuwar da ke gabanta. Neman Junaid agareshi ba wahala ba ne, zai iya kai ta kasar Russia, to amma ba zai iya cewa da Junaid don Allah ya aureta ba, tunda shi din ba sonta ya ke yi ba. Da yana sonta da ya nemeta, tunda ta ce yasan da Alhaji Abbas. A ganinshi ma, a wannan sabon zamanin da muka shigo. Mairo ta yi kankanta da aure, yana sonta da ilimi mai zurfi ba soyayya ba. To amma shi kansa ya kasa yanke hukuncin cewa Junaidun yana son Mairo ne ko ba ya sonta? Idan ba sonta yake ba haka kawai ba zai yi ta dawainiya da rayuwarta har haka ba. Allah ne kadai Ya san wane ne mijinta. Don haka ya kada harshe ya ce "Za ki yi min wata alfarma, Mairo?" Ta dago a hankali ta dube shi "Ta mece ce Yaya Habibu?" "So nake ki manta da Uncle Junaidu. Ba wai ki manta da alherinsa gare ki ba, a'ah, ki manta da soyayyar da zuciyarki ke yi masa, da tunaninki na ba zaki iya auren kowa ba sai shi. Amma kullum kika yi sallah ki dinga yi masa addu'ar budi da nasarar rayuwa kamar yadda ya zama sanadin da kika samu ingantaccen ilimi. Ni ma zan tayaki, zan dinga yi wa Junaid addu'a, wannan shi ne kawai alherin da za ki yi ki rama mishi, ba lallai sai kin aure shi ba. Da yana sonki da ya zo neman aurenki. Ko bai zo neman aurenki ba, da ya zo ya yi miki sallama a lokacin da zai tafi, ya gaya miki wata kwakkwarar magana, mai nuni da yana son aurenki a nan gaba. Ko ya ce ku yi alkawarin aure, don haka ki manta da soyayyarsa, ki tsaya ki yi karatu irin na Junaidu, ke ma ki taimaki mutane kamar yadda Junaid ya taimake ki. Ki zama malamar makaranta, mai nagarta irin Junaidu. Idan Junaid mijinki ne, wata rana ni na gaya miki zai zo inda ki ke, Allah Zai hada
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66