Chapter 45
Chapter 45
fada mishi cewa ba kya sonshi, akwai wanda kike so, don haka wannan jikin ma da kike wa marmari ba zaki same shi ba". Abincin da Mairo ba ta iya ta ci ba ke nan, sabida gani ta ke kamar Amirun yana karanto zuciyarta. To da gaske hakan ne, tunda yake shi din ba yaro ba ne. Ya fita ilmi da hankali nesa ba kusa ba. A kwayar idanunta ya gama gane ta tsaf. Yana kallonta sai caccaka cokali ta ke cikin abinci ta kasa kai ko loma guda. Shi kuwa cin abincinshi yake cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yana kallonta a kaikaice. Wani zubin ya yi murmushi, wani zubin ya girgiza kai. Wannan karon bai takurata da lallai sai ta ci ba, don ya tabbata ba zata ci din ba. Dan Abdurrahman Gaya, kadai ta ke so a jikinta. Kararrawar kofar shigowarsu ta yi kara, wannan ne ya ceci Mairo daga kaifafan idon Amiru. Da azamarta ta mike ta nufi kofar ta bude. Ta sha mamakin ganin Daddy da kansa. Cike da girmamawa ta ba shi hanya ya wuce. Sai da ya zauna a 'seater' ta zube a kasa tana gayas da shi. Ya ce "Yaya bakunta Maryamu?" Ta ce "Alhamdu lillah". "Babu wata matsala ince ko?" Ta ce "Babu Daddy". Amiru ya baro kujerarshi ya iso inda Daddyn ya ke ya zauna a gefensa suka soma hirarsu. Ta mike ta je kicin ta kawo mishi ruwan (Eva) mai sanyi da lemun 'shany' sannan ta gabatar mishi da abinci. A nan ne ya yi murmushi, ya ce "Lemun kadai zan sha Maryamu, na Hajiyarku yana can yana jirana, kada inci a wajenki inje in kasa cin nata". Ta yi murmushi ta ce "To Daddy babu komai". Ta koma daki ta barsu don su gana. Yau ma irin kwanciyar jiya suka maimaita, wato shi yana bisa kilishi ita tan kan gado. To haka kwanakin da suka biyo baya. Idan ka gansu a gaban Hajiya da Daddy. ko su Amina, ba zaka taba zaton cewa zaman 'yan Marina suke ba. Kowanne na ji da miskilancinsa ya kasa kwantar da kai ga dan uwanshi. Ga ita Mairo, a ganinta shi ne namiji, shi ya kamata ya nuna mata kulawa irin ta kowadanne ma'aurata amma ba ita ba. Sannan ba haka Dina ta gaya mata ana yiwa amare a renakun su na farko a gidan aure ba. Ba haka kuma ta ga Yaya Habibu yana yiwa Dinan ba. Amiru yace yana son ta baka da zuci, amma bayan aurensu ta ga ba haka ba. Wannan al’amari yana sanya ta cikin wani irin tunani mai zurfi da wuyar fassarawa. Har ta kasa jin dadin rayuwar gabadaya. Shi kuma Amirun, a nashi bangaren, ya riga ya saba samun tarairaya ta karshe daga banasariyar matarshi, kamar ta goya shi. Bai san cewa matar Bahaushe da matar bature akwai wasu manya-manyan banbance-banbance ba. Hakika mu Allah Ya ba mu wannan darajar ta kamun kai da alkunya, wanda ya zamo kowanne irin namiji, duk kyau, aji, mukaminsa da iliminsa dole ya lallame mu idan har yana son ganin yadda ya ke so. Yau juma'a ta tashi da kewar Dina kwarai a ranta, ba abin da ta ke so irin ta ji muryarta. Ya dawo daga sallar juma'a shi da Daddy daga babban masallacin Abuja kamar yadda suka saba kowanne sati idan suna nan. Ta rasa yadda zata yi ta roke shi ya ba ta aron waya. Dabara ta fado mata don haka ta nemo biro da 'yar takarda ta rubuta mishi, ta soke a jikin kofar dakin da ta tabbata shi ne nasa. Ya zo shiga dakin don sauya manyan kayan da ke jikinsa ya cimma sakonta. Ya yi murmushi ya sumbaci takardar ya share ta bai ce mata komai ba. Sai da daddare sun yi shirin kwanciya, bayan ya jefa filonshi ya mike. Ta zuba tagumi a gefen gado abin duniya ya dame ta, idan jurinta miskilanci ta gamu da wanda ya fi ta miskilanci. Ta juyo kadan, ga dukkan alamu barci mai nauyi ya tafi da shi. Cikin sanda kamar barauniya ta iso gabanshi don ta dauki daya daga cikin wayoyinshi sai caraf! Ya damke hannunta tareda wayar ya kuma bude lumsassun idanunshi sannu a hankali a kanta. Kunya ta duniya Mairo ta gama jinta. Ashe ba a yi komai ba sai sanda ya fizgota ta fada gaba daya a jikinshi. Ta rasa inda za ta sa kanta don kunya, fargaba da wani bakon tsoro da ya ziyarce ta duk a lokaci guda. Jikinta ya soma rawa kamar mazari, amma hakan bai sa ya cikata daga sassaukan rikon da ya yi mata ba. Duk yadda ya so da su hada ido cikin dan sauran hasken fitilar baccin dake dakin amma Mairo ta ki. Runtse idon ta shiga yi da karfi. Wani sabon Son mijinta AMIRU da kaunarsa ne farat daya suke tsirgawa a zuciyarta. Wadanda bazata iya tantance tun tsahon wane lokaci hakan ya soma ginuwa a zuciyarta ba. Yana danne wancan feeling din mai karfi da dukkan tasirin sa, wanda zuciyarta ta dade tana kallon Amiru dasu. Tareda gina mafarkanta da shi a kansa. Ya dago fuskarta daga kirjinsa, a wannan lokacin ya yi nasarar hango cikin kwayar idanunta, cikin murya irin ta wanda ya tashi daga bacci ya ce "Sata ko Mairo?" Ta ce "A'a, ina so in kira Anti Dina ne, kuma na fada maka ai ba ka ba ni ba". Ya ce "Ni ban kai kararki wajen Anti Dinan ba, sai ke za ki kai karata?" Kamshin 'mouth fresh' dinshi na fizgarta, yana sanya mata rashin kuzari ta ce, "Me ka yi min da zan kai kararka, kuma nima me na yi maka da zaka kai karata?" Ya ce, "Kin yi min laifuffuka da yawa Mairo, wadanda idan na fadawa Anti Dina sai ta zane ki wallahi". "Dame-dame ne laifuffukan nawa?" "Ai ba ki ma sansu ba?" "Da na sani bazan tambaye ka ba". "To sunkuyo nan na fada miki". "Kinga na farko ba kya gaishe ni da safe, sannan ba kya zuwa dakina taya ni kwana, sai dai ni na biyo ki dakinki. Sannan idan na biyo ki ba kya hada makwanci da ni, sai ki bar ni a kasa ki dare gadonki. Haka Dinan ta fada miki tana yi wa Habibu? Ko ba ki ga har kaya ita ta ke saka mishi ba? Amma ke bana jin ko inda nake wanka kin sani a gidan nan ko don har yanzu ba kya sona?" Taji zafi a ranta da kalamansa. Da zai taimake ta da ya daina zancen rashin so a tsakaninsu. Ta ce "Maganar ina sonka ko bana sonka, tunda mun riga mun kasance cikin inuwar AURE, to bata taso ba, bare kuma ni wallahi ban taba jin kiyayyarka a raina ba. Ko wancan lokacin da na fada, na fada ne kawai don ban amince da irin son da zuciyata ta ke yi maka ba". Ya lumshe ido a hankali, tare da sake yi mata muhalli cikin ni'imtaccen kirjinshi mai cike da gargasa. Yace “wane iri ne shi wancan son?” Ta dan rufe ido kafin tace “irin na shirme!”. “Wane irin so ne irin na shirme?” Amiru ya tambaya cikin mamaki. Mutsu-mutsun kwacewa ta hau yi, ko zai kashe ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66