Chapter 9
Chapter 9
mutun nasan zai sakaka ka more kuruciyyarka ka manta da kowa . Mama ta zaro Idanu waje ka manta kowa fa najikince har dani ciki . Faiza ta dan Susa kai ganin saba saiti . wayancewa tayi tace haba mama ai banda ai kece kan gaba in bake ai duniya zata min warbar kuno mama ta sauke ajiyar zuciya hade cewa abinda nake so naki kennan. to kinga dama yau za'a gama abinda nasa ayi to kinga ko zuwa da yamma ne sai mutafi. sai dai kuma idan duhu ne yayi . sai mu bari sai gobe idan Allah ya kai mu . ai baza mu tsaya kallon ruwa ba yanzu masha Kaye a gurin kwado suka sake kashewa faiza har jijiga jiki take zabar murna ... Please kuyi manage da wannan kai ke ciwoðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ MMN SUDAIS CE [3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗 ZUCIYAR MASOYI 💖💖💖 💗💗💗💗💗 AISHA A BAGUDO Page 55 Bai san iya adadin cup din coffee da yaje sha a kullum kafin yabaro office. Hotonta yana nan a bude a system dinshi ,shi ke tayashi hira da debe masa kewarta a duk sanda soyayyarta ta bijiroma masa , sannan yake samun ya gudanar aiyukansa . Dady da kansa yace yadinga yin haka domin ya zama jarumi a office ko idan yana kallonta zai iya aiwatar da komai cikin natsuwa "batare da ansamu wata matsala ba . Kiran dady ne yashigo wayarsa ya daga yana kallon hotota yasa hannu yana shafa beauty face dinta . bangaren dady kuwa cewa yayi mhm Abdullah tell me tun safe zuwa yanzu sau nawa ka tuna Aisha? Abdullah ya dan ciji karshen Biro da ke hannunsa yana tunanin. yayi dan yi murmushin takaici yace sau uku ne ma kawai. shima sai yanzu dana bude system da rufewa nayi saboda ina son kammalawa da wani aiki ne . Dady yace da kyau yarona kaga daga goma Sha ya fara raguwa gashi ya dawo sau uku . Abdullah ya sake yin murmushin kadan dan shi kadai yasan halin da zuciyarsa ke ciki game da rashin matarsa ya dau cewa dady haka ne kawai ahankali ya sauke ajiyar zuciya sannan yacire white glass din dake manne da idaonsa. ya jingina bayansa da kujera yana jujjuyawa ahankali manner da wayar a kunnesa yace dady akwai hanyar dana gano wacce tafi waccen saukin fahimtar komai ina ganin itace zata kawo karshen komai da muke bukata . dady yace da kyau ina jinka Abdullah yace sai zuwa anjima idan na koma gida zan maka bayanin komai . Da sauri dady yace shikenan sai ka koma din"Abdullah yace yauwa sannan yakashe wayar . Yana juyowa ya sake ya zuba mata idanunshi yace kin gani ko Aisha komai na rayuwata ya canza, narasa farinciki da sukuni tun sanda kika tafi kika barni . bana son a bani dariya saboda bana son nayi ,dariyar ki kawai nake so a tare dani . gashi dady yace kada naje gareki ni Abdullah ya zan yi da rayuwata komai ya taru ya cakudemin waje daya. rashin ki kadai ya isa ya tarwatsani . shi kadai yake maganar shi tamkar wani zararre . kawai idanunshi ya gane masa tana yi masa dariya ta cikin system dinsa. ai ko yashiga danne danne a jiki yana sake neman ragowar hotunanta wai shi lallai sai yaga wushiryarta data yi masa dariya yanzu. har sanda salis yashigo da coffee ya ajiye masa bai san wani duniya yake ba . Sai can hankalinsa ya dawo jikinsa . Gashi lokacin tashinsa ya kusa Amman baya kaunar abinda zai saya doshi gidan. sai yarinka jin gabansa na wani irin faduwa" tun kwana biyu da faiza da mama hafsa suka sauka a gidan, yaji gabadaya baya son kusantar gida dan haka gurin Dr sagir kawai yace a wuce dashi dan shi kadai yake tayashi hirar Aisharsa in ba cin dady ya hana aje da tuni Dr sagir ya je masa gunta . to zaune agun Dr sagir ne mami ta neme shi a waya" dan tasan lokacin tashinsa yayi daga office tashin hankali da mami ta sake jefashi da yaje kiran nata yafi wanda yake ciki a halin yanzu . dan magana ce akan faiza ita dai lallai ita take son ya aura Kuma tana son ayi komai kafin dawowar dady . Tana son faiza ta zama matarsa ta hakika . mama hafsa dake kusa da mami ta kara tabbatar da hakan suke bukata ayi auren da wurwuri . Abdullah ya zubawa maminsa ido shi kansa ya amince tun ba yanzu maminsa na matukar kaunarsa fiye da komai . a tun sanda batun aurensa ya bulo ta sauya masa kar dai mami ta tsane shi ne ayanzu yaji gabansa yayi wani irin faduwa da sauri ya kauda wannan a ransa saboda dady ma ya hana shi ganin laifin mami yace yin haka bbu kyau . Yarigada yasan halin dadinsa dan haka sai daya gama yi masa dukkan bayanin tsarin daya shirya game da masu son salwantar musu da dukiyar . dady yayi shr yana jinjina kai yayi Ammanna da shirin Abdullah din. da yaba masa Sosai da irin dabararsa a karshe har yayi masa godiya dasa masa albarka. Bangaren Abdullah kuwa ba wannan ne a zuciyarsa ba . dan haka yana gama jin dady shima ya dora akan sanar da dadinsa halin da'ake ciki na game da maganar auren faiza da ake ciki . dady yayi dif ... Na wani lokaci wanda har Abdullah din yasake kiran sunanansa. dady yace inatare da kai Abdullah ina jinka yadda Dady yaji aransa. haka shi ma Abdullah din yaji. dady yakira sunan Abdullah din rai a bace. yace ka gane ko Abdullah duk abinda mahaifiyarka zata nema daga gareka kayi kokarin kaga kayi mata yadda take so . kasan bbu abinda yafi uwa a nan duniya . Allah (s w t) dan kansa sai da ya ambaci uwa uwa uwa har sau uku kafin ya ambaci uba sau daya. Abdullah ya girgiza kai game da dan rufe idanunshi dady yace to kaga duk abinda zata ce kayi kai dai ka mata biyayya . domin muma mun gama da iyayenmu lafiya. jikin Abdullah yayi mugun tsanyi akan yadda Dady yace haka zaiyi Amman ana shi tunanin me yuwa a sanadin haka ya rasa Aisharsa na har abada. saboda yasan muddin ya aure wannan faiza mutuwa zaiyi . Tamkar dady yaji shi ya Kuma cewa kada Kuma kayi zaton aurenka da wannan yarinyar zai sa baza ka sake auren Aisha ba . A'a kai namiji ne Shari tabaka damar auren mata fiyye da daya . dan haka ka sawa ranka ko kayi wannan aure . in Allah yaso Aisha zata dawo gareka kaji . Abdullah ya amsa da to. dady ya sake yin kasa da murya yace Abdullah na rokeka ka sausautawa zuciyarka damuwa nan kafin na dawo . idan wani abu yasameka ban san yadda zanyi ba . Bansa kalar halin dazan shiga. sannan dady ya ajiye wayar ya jima zaube bai iya motsa jikinsa ba saboda bacin rai da yake ciki. iyakar fushi yayi da mami sai a yanzu ya gano dalilin raba Abdullah da matarsa datayi. ita ko tsoron alhakin yaron bata yi. ko musu baya iya yi mata "tun bai kai haka ba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46