Chapter 21
Chapter 21
dan yatsina fuska tana kai aunty ke me fita kullum gara dai na koma can yanzu haka nasan inna nacan na kewata . Aunty ta jinjina kai batace komai ba . To a daren ma da ta kwanta sai da ta sake mafarki dashi ita har tsoro abin ya fara bata ita dai a yadda take ji ko me za'a yi sai dai ayi Amman tagama auren Abdullah ,. cikin sa ne idan ta haife mishi zata bashi abinsa nan taji wata irin faduwar gaba itama tana son danta fa bazata iya bawa Abdullah ba sai dai kawai yayi hakuri ya bar mata ko su yan gidansu dokin ta haifar musu karamin yaro suke . da safen ranar Sam Abdullah yakasa hakuri dole yaje ya samu Dr sagir din daya rakashi yace shi ko me babanta da yan'uwanta zasu ce zai rufe ido ya sauraresu ya Kuma basu hakuri shi dai kawai su sadashi da iyalinsa . To yadda yazata abun ma ba haka yagani ba. yayi sa'a ya samu mlm abu a kofar gida a adaidai lokacin da yake shirin fita ya tafi zariya kala kala duk dai akan maganar .tasu. byn gaisuwa sai dan bayanin daya musu akan zuwansa zariya kala kala sai bayanin ita kanta Aishar . Abdullah yana durkushe kmr wani mai tsansar tsoron ko dago kai baiyi a karshe mlm abu yasanar dasu Aishar ma tana gidan aunty Maryam . Tunda dai duk abinda Allah ya kaddaro bawa dole yayi hakuri dashi duk uban da akace an saki diyarsa a wannan halin dole zai so ace takoma dakin mijinta ta haihu dan haka duk yadda Abdullah yazata sai yaga ba haka ya Gani ba . bbu wani batanci daga babanta har ma sauran yan'uwanta daya shigo gaisar da inna a zuciyarsa yace lallai jini daya ba wasa bane. a karshe sukayi godiya sosai suka mike Abdullah yaji dadi Sosai abu daya "daya dan dameshi kmr yadda dady ma yayi masa kofafi akai har yau suna nan a mazauninsu daya san su. basu da niyyar tashi saboda haka ne akasawa Aisha gidaje a cikin sadakinta tunda an san ita dai bbu abinda zatayi dashi . Mijin aunty suka fara samu a waje yana shirin shiga gidan da fara'a sosai ya tare su . ya shigar dasu sit room dinsa dake ta hanyar waje. byn gaishe gaishe dan shiru ya biyo baya na wani lokacin Amman mijin aunty Maryam dayake yasan halin da'ake ciki ya gane nufin su dan haka. Yayi dan Jim sannan yace koda yake bari a turo ita Maryam din ya tashi yashiga . Abdullah ya rike hannu karamin yaron aunty Maryam yana tambayar sunansa Amman wayance yake tambayarsa Aisha aunty ta shigo hade da sallama ta dinga murmushi ganinsu dan ita tun jiya take murna saboda tasan wannan dan rigimar Dr salim bai san Aisha tazo kebbi ba gashin zuwan nata yazo . mata da alkhari tsohon mijinta mai kaunarta ya dawo gareta . dama kuma tasan abu ne mawuyaci Abdullah din bai dawo ba . Aunty ta zage sosai ta nuna musu bbu wani abu komai ya wuce Allah ya kiyaye gaba tunda dama wata rana dole a sake haduwa tunda me hadawa ya hada. matsalar dai a gurin Aisha take ta nuna musu tun jiya dataji dadinsa yazo shine ma ta gudo gurinta. to anan tsakanin su su uku suka shirya duk yadda za'a yi aunty Maryam takara da cewa ai ko yanzu da zata ji kunzo to bar gidan kennan. Abdullah yayi murmushi kadan yasan za'a yi haka Aisha bazata son ganinsa ba ya fada a ransa.. MMN SUDAIS CE [3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗 ZUCIYAR MASOYI 💖💖💖 💗💗💗💗💗 AISHA A BAGUDO Page 66-67 Aunty Maryam da Dr sagir ne. suka tsara duk yadda za'a yi tafiyar " musamman da kowa yaji inda dan'uwansa ke aiki akwai wanda yasani a gun . washegari da yamma sai da suka sake zuwa gidan Amman ko kadan bata bari Aisha tagane ba. dan aunty Maryam ta kagu taga Aisha ta koma gidan Abdullah ko dan saboda wancan jarababben salim din yadda idan yata shi balbalinsa ya kone shi kadai . Da daddare tana dakin aunty kwance Aisha tana kan gado sun gama wasa da diyar aunty Maryam har tayi bacci a jikinta. aunty tace ni ko Aisha ina ganin yanzu yadace ki fara zuwa awo asibiti tunda kinga watan cikinki yanzu yashiga wata na hudu kennan. Aisha tayi shr bata ce komai ba. Aunty tace Amman yadda kika gani fa. wai saboda lafiyar abinda ke jikinki ne dan akwai magunguna na musamman da'ake son mai ciki ta dinga amfani dasu" domin ta haifi yaronka cikin koshin lafiya . da yake cikin na ranta dan haka ta tsaya sosai tana saurara auntyn. Amman in kin fi son sai kin kusan haihuwa ne shikenan aunty Maryam ta fada batare da ta takura mata ba . Aisha ta dan mike ta jingina da jikin gadon" ahankali tace ni aunty kawai sai a ganni na tafi wani asibiti kowa ya dinga" kallon ina da ciki. aunty tasa dariya tace to ke meyasa kikayi abinda yasa kika samu cikin? Aisha ta turo baki tana cewa haba aunty haba aunty da kanki . Aunty Maryam ta sake fashewa dariya sai da tayi mai isarta sosai "sannan tace ai bangaren daza kije asibitin ko wacce ta kalleki itama abinda yakawota kennan . Amman yanzu kina komawa ka'oje bbu wani zance zuwa asibiti akai akai. Aisha Tace ai can din ma akwai asibiti sai ba sai naje ba . aunty Maryam tace ki ajeye komai kizo na kaiki asibiti malam ki kwantar da hankalinki bama asibitin mu ,zan kaiki ba nasan saboda Dr salim baki son zuwa . wani zan kaiki duk da akwai wadan da nasani acan za'a yi miki komai ko ba nan. Aisha ta girgiza kai alamun ta amince . aunty tace to kishiriya gobe in Allah ya kaimu sai muje a yankar miki card daga nan zasu gaya miki randa zaki dawo ahankali tace shikenan. aunty kuwa har godewa Allah tayi da taga ta fada tarkon farko . Tun shigarsu asibiti Aisha ta gane tabbas sun taba zuwa asibitin ita da sister dinta dubiya . Wata nurse ce ta karbesu hannu bibbiyu da fara'ata sosai" inda ta dada birge Aisha taji dadi Sosai har cikin ranta kuma ta rike sunanta sister din kafin su baro asibitin. komai akayi mata shi cikin sauki ba yadda ta zata ba . A dan lokacin ma har taji tana sha'awar irin aikinta sister din. Tama awo duk a lokaci sannan tace dole zata dawo jibi da akwai gwaje gwaje da za'a yi mata . To hakan kuwa komai akan idonsu Dr sagir da uban tafiya Abdullah ya faru . ta gabansu "su aunty Maryam suka wuce "tun shigowarsu Abdullah ya kura mata idanunshi ta canza sosai ta kara kyau matuka fiye da lokacin da Suke tare. ko Kuma a lokacin dan yana ganinta ne koda yaushe ne . yanzu kuma ya dan jima bai ganta ba sanda suka zo daf da inda suke da sauri Abdullah ya juya bayan wani ginin. ya dafe kirjinsa ya rufe idanunshi yana jin yadda zuciyarsa ke wani irin dokawa da sauri da sauri. ita
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46