Chapter 32
Chapter 32
da sunayen yaran ajiki.. a ranar da kuka suka baro wajen da yaran dan duk sun gaji da yawan daukarsu da'ake tayi . Dan Adnan har jan rigarsa yake wai shi sai ya cire" alamun yana son wanka kennan . ta abuja suka sauka a gidansu wanda kayansu orready kai tsaye gida sukayo . Washegari suka dauki hanyar kebbi "koda suka sauka agidansu na aure ma'aikata suka tarar kmr ana rayuwa a gidan ko awa basu yi ba. ya fita tare da salis bai jima da tafiya ba sai ga ma'aikata guda biyu daga cikin na mami ya turo mata saboda kula da yaran . Washegari kuwa yace ta shirya zasu tafi gidan akaiwa mami su affan ta gansu" dady ma tun jiya yake maganar yaran duk jikinta yayi tsanyi ,a sanyaye ta gama hada komai da zasuyi amfani dashi ita ba abun tace bazata ba "yace wai dan bata son shi ne "yaran nata tsalle tsanllensu komai sunki yarda ayi musu "sai ita da kanta ko Abdullah hatta wanka da shiryasu "shiyasa duk suka bata lokacin sai kusan karfe daya na rana suka shiga gidan Abdullah har ya bude mota yaga bata da alamun fitowa ya dan kalleta ya lura tunda ya gaya mata zance zuwansu wajen mami jikinta yayi tsanyi bai ji wata kunyar ma'aikata da suka yo kansu ba ,ya jawota jikinsa yace kiyi hakuri fa ta kalleshi Tayi kalar tausayi ya daga mata kai kiyi hakuri da komai nasan ,duk ni ja komai dana makale lallai sai ke " ina sonki tamkar Raina "yadda bazan iya rabuwa dake ba hakka bazan taba canza uwa ba, sannan ya saketa yayi gaba da yaran dan har sun fara kuka ganin za'a tabasu . Koda suka shiga bbu kowa dan duk su teema basanan, sai mami ce kawai a falon "sai mai aikinta tana gyare gyare suka shigo . Aisha kuwa gabadaya jikinta rawa yake dan har wata zufar wahala take tsatsafo mata , Abdullah duk ya gane yanayin da tashiga Amman share yayi kmr bai Gani ba" har gaban mami ya karasa affan yana kafadar hannunsa Adnan kuma yana rike da hannusa yana dariya ya sauke affan ya fara gaisheta Aisha dake labe a bayan Abdullah itama ta dan matso jiki a tsanyaye tana gaishe ta.... MMN SUDAIS CE [3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗 ZUCIYAR MASOYI 💖💖💖 💗💗💗💗💗 AISHA A BAGUDO Wow masoyan arziki , yan biyu masu tsananin shiga rai ,hakika kun shiga Ran bagudo ba karya .kuna ina 🗣🗣🗣🗣🗣 blessing twince ,hasana danlarabawa & huseena danlarabawa ku matso kusa wannan shafin naku ne ku kadai, kuyi duk yadda kuke so dashi, ina matukar sonku har cikin nan ❤ , ina kyawun yi daku irin sosai din nan, ana kyawun tare 🤝🤝🤝🤝nima ina addu'a r Allah yabani blessing twince guda bibbiyu sau goma... 😃😃😃 Page 77-78 Aisha dake labe a bayan Abdullah itama ta dan matso jiki a sanyaye tana gaishe ta... mami ta amsa tana kallonsu a bazatan da suka yi mata ,da turanci Abdullah yake gayawa su affan su gaishe da mami Amma kememe suka ki matsa daga jikin Abdullah"ko jikinsa basu bari ba suka sake mannewa babansu . mami ta zubawa sarautar Allah ido ga Abdullah lokacin yana yaro har guda biyu a gabanta abin ma tsoro yashiga bata . Abdullah ya fahimci yanayin da maminsa tashiga dan haka ya sunkuyar da kansa kasa yayinda yaran suka sake mannewa jikinsa. tsawon lokacin mami tana zaune takasa magana ,ahankali murya cike santsar ladabi da biyayya Abdullah ya dago yace kiyi hakuri mami ' jiya dare yayi bamu ba Muzo dasu ba yau kuma tun safe ake shirinsu ". Mami ta girgiza kai kawai tayi shr "Abdullah yashiga waige waige yace su teema sunje school ne" aHankali mami ta amsa" ya dube su affan cikin harshen turanci yace kuje gurin mami kusha tea " Amman kememe suka ki sakinta sai da kyar yasamu ya bambaresu ya fita ai kuwa suna ganin haka suka koma byn mamansu . Aisha kuwa ko motse bata iyayi sosai ,saboda barinta da Abdullah yayi da mami . shima kuma tun fitarsa yake tunanin yanayin dazata shiga, Amman ba yadda zaiyi gara komai yazo karshe . Mami takasa dauke idanunta akan yaran ,ta kasa magana wani abun kunya duk goce gocen cikin Aisha da take. sai gashi ta haifo irin abinda ta haifa sak ita har guda biyu ma" data tashi haifar nata , gashi su kansu yaran basu santa ba, gudunta ma suke, taji bazata iya zaman falon ba ga Aisha a gurin" ta Mike cikin sanyi ta shige ciki ,tamkar ta zubda hawaye take ji,. Aisha na nan takure a zaune "gashi su affan sunki yarda da kowa" ita a zatonta ko mami wani fushin tayi , shine duk ta kara tsorata ,tana nan zaune su minal suka shigo da ihu suka karaso kanta itama sai a lokacin dan taji dadi "da wayo da calculate suka samu suka dauki yaran , dukkansu kamar su cinye yaran suke ji . Aisha ta kallesu byn sun hau da ita samansu "Tace teema kunbar mami ita kadai teema Tace ina jin bacci take yi" Amman bari na koma na Gani "ta dauki Adnan da karfin tsiya suka sauka . To yinin ranar mami tasa aka canza abinci ,saboda su ,da kyar yaran suka yarda suka zauna kusa daita sai da aka baza kayan wasa da calculate iri iri a gabanta "sannan suka zauna ta zuba musu ido tana kallonsu hannuta ta daura saman kan su affan tana shafawa tana dauke numfashi, wani abu daya kara girgizata yadda taga kmr pampers din jikinsu ,ce ta damesu tasa teema ta cirewa adnan anan bathroom din mami " ta ajiyeshi ta tafi ta gyara affan. mami ta lura da dan tabon dake cinyar Adnan dan duhu gurin yayi kadan wanda hausawanmu suke cewa rowa to yadda yake a jikin yaron haka yake ajikinta "shima a bangaren dama kmr nata. wannan tashin hankali har ina ga Aya ta koina tana zuwa mata" har kara dubawa take .anan aka sake shirya su da abincinsu" duk akawa mami kaca kaca da daki" sannan teema ta hau sama kai affan dan yana son mamansa. Byn fitarta mami ta kamo adnan ta dinga kallonsa tana hawaye taci kukanta sosai ita kadai ba wanda yasani . tunani kawai take mama hafsa ta kusan kasheta a da , take fada a ranta. ita batama san kowaye daga cikin yaran ba a gabanta tunda yaran duk kamaninsu ta baci ta jawo shi jikinta sosai ta rungume ganin datayi yana gyangyadi saboda a can Ma affan din bacci ya fara . Dady kuwa dayaga yaran rudewa yayi ,yana dariya ya cewa Abdullah kada fa dawowarsu nan canjin abinci ,yasa sukiyin kiba da girma" irin haka. Abdullah kuwa dariya yayi yana sunkuyar da kai kasa dady sai sake jinjinawa yake "yana Allah kennan me yin yadda ya so" to yanzu wanene babban acikin su ? Abdullah ya kallesu ya kirawo sunan affan dan sun rigada sun san sunansu . dan haka shi din ne yayi saurin waigowa "sannan ya nuna wa dady shi' dan shima da haka yake ganesu "musamman mami ta canza musu ma'aikata raliyya kadai ta amincewa ta dinga kula da yaran .
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46