Chapter 8
Chapter 8
ba kmr soyayyar yarinyar nan. tunda na ganta na rikice narasa gane kaina. kiyi hakuri sister Aisha tana gida a yanzu sun rabu da mijinta. aunty taja numfashi tace kai ko wani me balain bincike ne ya gano maka haka . Dr salim yace that's very good abinda nake son ji kennan . aunty Maryam bata gane nufin shi ba sosai dan haka ta sake cewa maganar gaskiya doctor a ina kaji wannan labarin?dan nasan maganar nan ko makota basu sani ba .. Dr salim yayi dariyar murna sosai har cikin ransa yaji dadi tarkonsa yace sister kennan ni bbu wanda ya gaya min hasalima ban san wanda zan tambaya wanda yasan Aisha ba sai ke. Nina na gano hakan da kaina . aunty tayi sororo tana kallon doctor . tace doctor bbu maganar wasa a nan fa . Shima yadan nutsu yace da gaske nake sister ina son kanwarki. Kuma aurenta zanyi. ta sake zaro Ido waje ina wannan maganar ba mai yuwa bace . A cikin lokacin daya ta canza fuska tace doctor ba fa son irin wadannan magangunun an gaya maka Aisha tana da aurenta duk ma wanda yace maka bata da aure ya gaya maka gaibu . Dr salim yace wallahi azim ke kika sanar dani yanzu . sannan nasan zatona ya zamo gaskiya .. MMN SUDAIS CE [3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗 ZUCIYAR MASOYI 💖💖💖 💗💗💗💗💗 AISHA A BAGUDO Page 53-54 Aunty Maryam ta dubeshi da kyau ta gano yadda ya nuna mata tsantsar wayo tun farko. taji haushin kanta na Subul da bakan datayi. nan da nan ta sake bata fuska tace eh da gaske ne, Aisha sun rabu da mijinta "Amman doctor ina tabbatar maka bazaka taba samunta ba. garama ma tun wuri kabawa zuciyarka hakuri ta hakura da abinda baza taba samu ba . tana shirin mikewa Dr salim ya dakatar daita murya a sanyaye yace yi hakuri sister Maryam. ni ban dauki abin da zafi haka ba ,kmr yadda kika dauka . nasan Aisha kanwarki ce Kuma abin ikon kice . na gane koma ya akayi akwai wani abu da kike gudu . shiyasa kika yi saurin fadar haka a kaina. Amman ki sani sister a yadda naje jina a yanzu dana rasa yarinyar nan na gwammace na rasa wannan ya Nuna farar rigar aikin dake jikinsa . ya numfasa sannan yace dan nasan duk me mace irin wannan Kuma yayi gangancin sakinta komai daren dadewa zai waiwaye ta . Auty ta kalleshi tace doctor duk kimarka da nake Gani ba zan hana na shaida maka cewa kana shirin sa kanka a uku muddin bakayi gaggawa cire son Aisha aranka ba . Mike ko gezau baiyi ba sai ma murmushin samun nasara dayayi . Ahankali yace afuwa dai sister Maryam ai ni nariga naga abinda yayi daidai da tsarin zuciyata dan karfin hali irin naki zaki tauyeni ina bazai yuwu ba wlh , a zafaffe tace to Allah yabada sa'a. da karfin shi ya amsa mata da Ameen dan har da gaske kike . ta wuce shi har gabanta na dan faduwa uhm ba za'a fara jin mutuwar sarki a bakinta .shima yajima zaune a wajen yana saka da warwara hade jin haushin aunty Maryam . Faiza tace dan Allah ni mama ki kyaleni na ci kaniyar wannan Yar iskar da bata gaji iskanci ba. sai dai ta ara ta yafa. kibarni nacasata na gurje bakin rashin mutunci shegiya Mar kirjin a gwagwa itama Sami kokarin rama zagin take Amman faiza dam ke bakin ta murde . mama hafsa dake kokarin shiga tsakanin faiza da aminiyarta Sami. Amman ina faiza taki sakinta sai jibgar Sami take kmr Allah ya aikota da kyar da sidin goshi mama hafsa tasamu ta rabu su . Faiza ta bude baki zata lailayo wani a shar din mama ta katseta ke Ke ke tana nuna da dan yatsa. ya isa haka nace sannan ta tura keyar Sami tana bata hakuri tanuna faiza ke dai akwai Yar jarabar yarinya ana yaki kina ga kura Tjeey din cin durin uwarki. duk yawon danayi a kigajen bokaye da yan tsubu kenan zai tashi a banza. ki wuce kebbi ga wanda ya fi Tjeey da komai ta koina can Amman kin tsaya kina asarar yawun bakin akan wannan mai sololon kan kmr na miciji. Da wuya awa marakin lema . faiza tace ai mama nasha gaya miki kece dai baki da fahinmta ina son Abdullah kodan kyaunsa Kuma wlh dole ne na aure shi tako wani hali na kanannade shi ta koina. na dai tsaya ne naga ta karyar iskancin Sami wai daga naje mata sallama na tar daita da Tjeey. dan na tsaya muna gaisawa dashi kawai tashiga bace bacen rai ni Kuma dana ga haka sai na dada shishige masa ni daman can yayi min. shima Kuma ya nuna yanayi dani shikenan take ta balain shine yanzu tabiyoni har gida dayake jakace . ba dole nazage dantse na nuna mata karyar iskancin takeyi ba . Mama hafsa ta rike baki tana jujjuya kai . a ranta tace dole ma ayi tafiyar nan kebbi tare da ita zai fi ma'ana. Sannan cikin yin kasa da murya tace nasan halinki da rawar jiki sauran kije kina zubda aji agunsa . nasan duk yadda wannan banzan yaron yake bai kama kafar masu wankin Abdullah ba balle matsayi . dan haka kibarwa Sami shi suje can sukarata idan mulke shi zatayi da mai kullum wannan ba ruwanki bane. ke dai ki duba cigaban ya zo miki . yanzu kije ki hada inaki inaki anjima nan zamu tafi har ni sai naga zaman naku ya daidaita sannan zan dawo. dama naso kifara yin gaba ne. saboda ni ma nan akwai abunda nasa ayi min saboda Abdullah din ya dinga rawar kafa akanki. daya dinga yiwa waccen Yar matsiyatan masu tasan nono ,gara yadinga miki . Sai yanzu hankali faiza ya dawo kan maganar mama hafsa tace wlh kuwa mama . Dan yana daya daga cikin abinda nake tunani kennan akan auren Abdullah . nifa ko kallona yayi nan duniya ji yake kmr ya kashe ni. Ko cikin farinciki ko nishadi yake danazo gurin yanzu nan zaiyi kicin kicin yarinka cin magani . mama hafsa tace kinga abinda yakama ki nutsu kiyi . kisamu yadda zaki kwatowa kanki martaba a gunshi . shine kika zauna kina fada da wannan cima kwance. faiza ta kwashe da dariya tana Miko mama hannu wai sukashe . Ai kuwa mama taba suka kashe suna tuntsira dariya . Faiza tace nida nake da burin indan na aure shi na samu na sake dashi sosai. to yana haka yaya za'ayi abu abubuwa su kasance . Mama hafsa Tace ina.. wane shi dan ubansa dan baki san kullaliyar dana sake kullowa bane kai arziki ma idan ba a gurinka yake ba aikin banza ne. Ko kana sa wutsiyar ido ka hango shi a wani guri ya zame maka balain ka kasa tsugunne da duwawunka duba ki ganni har Yar rama nayi saboda ganin auren naku ya yuwu.. faiza ta katse mama da cewa ni yanzu nafi so ayi abinda Abdullah zai dinga lashe ni tamkar dawisu saboda so shine kan gaba. dan wannan jikin nasa idan ya kasance yana son
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46