Chapter 20
Chapter 20
Nemo mami koda ta shigo fuskar nan a hade tamkar hadari ,shi kuwa anasa ya sake fuska sosai tamkar bbu wani abu a kasa . byn gaisuwar datayi da kyar yace akan maganar da mukayi jiya ne duk na fahimci abinda kike so nima kuma dana yi tunani sai naga dacewar hakan "a tsakanin yaran dan ko ba komai hanya ce ta karfafa zumunci . Mami da dago da sauri ta kalleshi da kyau tasan abu ne mawuyaci idan ya hau ya sauko da wuri. Dan dady ya sake bata haske sosai yace kinga ita hafsa tun ba yau ba take sonki "dan ta so hada diyarta da danki wannan ai ba aibu ne abu ne mai kyau "ina ganin Karin so ne ya kawo haka.. Mami ta saki fuska tace abinda nake son ka fahimta "kennan yanzu jiya da ba'a je daurin auren nan ba" nasan duk laifina hafsa zata Gani . ko meye ma nasan a kaina zai Kare . dady ya kura mata idanunshi ya tabbatar da abinda yake zarge akan mamin "sannan ya dauke idanunshi yace duk ba wani abu da zai faru ,yanzu dai nasan me yiwuwa, su daga can zasu so jin abinda ya dakatar da zuwa daurin auren. to kawai sai ace shirye shiryen bikin ne aka canza kinga akwai bukatar kayayyakin al'ada na auren . duk naga anayi kuma suma zasu" bukaci wani abu ko ba haka ba" yana dan duban inda mami ke zaune . Mami tace ai komai fa anriga an gama shi ahankali cikin dabara duka dady ya bincike abinda yake son ji daga gareta "kuma cikin sauki kai duk mami ke masa bayanin komai har da abinda bai tambayeta ba. dan har irin dukiyar da ta sakar musu da fitar dasu faiza sukayi hado lefe da kayan gado duk sai da yaji a karshe ta bayyana masa komai" na part din Abdullah dady har tsorata ya farayi da lamarin "yana can an kusan kashe masa gida kuma duk abinda mamin take a yanzu ya dada tabbatarwa kansa ba'a cikin haiyacinta take ba . Dama kuma duk shekarun da take dashi da ya'yan data yi . idan ta masa wanin abun kallo daya zaka mata kasan diyar fari ce Kuma Yar auta Yar gata . Dady ya jinjina girman al'amarin sosai a karshe shima ya nuna mata yadda duk suke so ita da mama hafsa shima haka zaiyi musu" ko da anzo daga can ma hakuri zai basu me yiwuwa ya bisu a daura auren a ranar . Mami tasan meye kulawa a rayuwarta "ya amince da wannan tunda ga kansa har zuwa kan ya'yansa tana basu kulawa yadda ya kamata tana rawar jiki akansa sosai musamman idan yayi tafiya ya dawo. Amman wannan karon yaga canji me yawan gaske atare daita tunda ya dawo baifi sau biyu tashigo part dinsa ba shima murtuke ,da fuska da rikici iri iri suke rabuwa . sai a yanzu yaga fara'a ta sosai saboda abinda ya fada zaiwa mama hafsa har hira ta barke tsakanin su ya gaya mata abubuwa da makwaftan su na abuja suka zo dashi . ya kwaso ya Mika mata ta karba tana Gani ya zuba mata ido jiya ko baccin kirki bai samu yayi ba. yana ta addu'ar Allah ya fahimtar dashi abinda yake akwai har istahara yayi duka a daren jiya . sai gashi Allah ya sanyaya masa zuciya yanzu gashin cikin dabarar da yayi mata game da zance biki yasan komai . kuma yasan inshallahu komai ya wuce . A yadda dady yazata kuma yake sauraro. .hakan ce takasance dan karfe 1 daidai yakarbi wayar daga wajen masu gadin gidan "yana ajiye wa shima yayi tasa wayar Jim kadan sannan ya fito" da kansa" zuwa wajen get din gidan. yadda yazata din kuwa haka ya Gani mama hafsa ce ita da faiza sai kanwar faizar rahma ganinsa yasa su da kansu suka tsorata a bazatan da yayi musu. dan tun zuwansu da masu gadi suka tsaidasu basu sanar musu dady ya dawo ba . dan mama hafsa har huci take tana numfarfashi hade da zagin masu gadin . dama kuma tazowa mami da zafinta . mintina kadan suka wuce bbu mai iya magana acikin su ,ba abin su gudu ba su fallasa kansu ko cikakken minti goma ba'a yi ba "sai ga motar police biyu cikin fararen kaya "dady yayi musu nuni da mama hafsa ai ko kmr Jira suke suka ciro I'd card dinsu suka nuna mata . Hade da nuna musu su shiga mota a frigice mama hafsa take kallon abinda Ya ke shirin faruwa ita faiza so tayi ta gudu suka cafko ta sai cikin motor suna cewa bawani abu za'a musu ba illa yan tambayoyi . dady yace aje dasu sai yazo nemansu. motar taja bbu wani wanda yasan abinda ke faruwa a waje . dan ko masu gadin tun kafin yan sandan su zo dady yace su shiga ciki mami ma na can cikin gida batasan wainar da'ake toya ba. bare Abdullah da gabadaya baya unguwar ma haka aka tafi dasu dukkansu su uku rahma kuwa kuka kawai take tana kiran wayo Allah .. (wannan shine akoba adaba 'olon ma'jerin') inji yarbawa . Tayi shr a daki mamaki abin take ,ta dade rabon data kawo shi a ranta tun byn rabuwarsu . data dinga tunanin shi tana kuka a karshe ta hakura dashi "tunda bbu alamun shi. komai nasa tabarshi sai a jiya da daddare data kwanta tayi mafarki dashi . ta ganshi yana kuka kuma sosai har tazo kusa dashi ya kama hannuta yana cigaba da kukan sai itama taji tana neman tayashi . adaidai lokacin da kukanta zai bayyana ta farka tun daren takasa komawa bacci . dan bata gane kan mafarkin ba . tasaba ada muddin ta kwana da tunanin Abdullah to tabbas ne ranar sai tayi mafarkin shi. Amman sai gashi ko mai sunansa bata tuno ba sai gashi tayi mafarkinsa ,. to byn saukowar masallaci jumma'a ne kadan sai ga babanta da saurinsa yashigo. yana kwasar tabarmi da abubuwan sallah yana gayawa innarmu wai yayanta ne yazo . tana kallon yadda innarta ke murna da dariya farinciki hade da daga hannuta sama tana addu'a . to har zuwa byn la'asar Aisha bata motsa ba tana daki a kwance har sanda taji babanta sun shigo tare da dadyn Abdullah sun gaisa da inna sosai . yayinda mlm abu yadan basu waje su gana . Kwanaki biyu kennan da mlm abu yaje dubota da yaya yusif ta biyosu dan taga innarta . idan ta kwana biyu zata koma dan tafi kaunar zaman can . Tana nan har lokacin da taji uhun ya'yan aunty Maryam da hargowarsu sun shigo tare da aunty sai lokacin ta dan mike ta fito tayi alwala . Aunty Maryam na can tsakar gida tare da inna da ta iddar da sallar la'asar . tariga ta gama yanke shawara aranta dan haka tace ni aunty tare zamu tafi gidanki na dan yi kwana biyu sai na dawo na wuce ka'oje aunty Maryam ta dan kalleta kadan tace ai ni haka nake so da zaki yarda ma da muyi zamanmu tare idan su inna zasu ganki ba sai sunyi tafiya mai nisa ba . Ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46