Skip to content

Chapter 16

Chapter 16

Zuciyar Masoyi Book Two Complete Hausa Novels 1,151 words 0 views Progress saved
Download Book

duk duniya zata hade ba zai tafi shi kadai ba . kafarsa kafar Aisharsa sawa zaiyi a sato masa ita kawai . Ba zai yarda yayi wani rayuwar aure da wata byn Aisha ba . dan haka yana tafiya zai manta da wani auren faiza dake kansa. in tagaji da jira tasan yadda zatayi da kanta . in baya ga iyaye ma da idan yayi gaba. ya tafi kennan sai dai idan yaso lekowa. Tunanisa ya dawo kan kujerar sa ta office idan yayi tafiyar nan . tunaninsa wanda zai riketa da amana yayi shr yasan dady zai iya hadawa har nasa kujerar. Amman yasan ayyuka zasu yi masa yawa sosai Dr sagir yake dubawa a yanzu shima yana da aikinsa. Amman yana da kyau yayi wa Dr sagir wani abu mai mahimmanci a rayuwa. saboda Allah shi ya hada shi Aisha Amman ta dalilinsa . Faiza ta kankane komai nata da duk wani abu da akayi oder sa ta juye shi a part din Abdullah . kayan gado dana kitchen iyakar tsaruwa komai part din ya tsaru yadda ake so matuka gaske. cikin abinda yabawa mutane mamaki gabadaya ta tare a part din tun ba a daura auren ba. tun dawowarta daga kasar waje sau biyu ta taka sokoto. shima direba ne yakaita kuma a ranar ta juyo hatta kawanyenta na can daidaiku ta gayyata . dan haka duk bikin da'ake a sokoto bbu amarya suke gudanar da komai. amarya tana can gidan mijin nata. dan Abdullah yabar part dinsa acan take kwana mutane kuwa suka samu abin fadi sai surutu ake .. Wata yayar baban faiza ce tace kai jama'a ai sai a zage mu koma ana kan zaginmu . ace amarya ana biki a gidan ubanta ita kuma tana ca. har takai kanta tana can gidan iyayen miji ai ba zai yiwu ba wlh. dan haka sauran kwana biyu a daura auren tun asuba suka baro sokoto zuwa kebbi tace dole su tafi da faiza a kalla dai ta bari ko daura auren ne ayi tana can. idan yaso ta biyo yan daurin auren. da kyar da sudin goshi dai aka lallaba faiza ta biyosu duk da tayi ta bata musu lokacin "tana zumbire zumbire don da basu sameta ba a gidan taji labari zuwansu. bazata dawo ba ,sai dai suka raci zaman su . , su koma byn ta hada komai nata ta kulle part din Abdullah ta bawa teema ajiyar keys din saboda kada ta tafi dasu can a faki idanunta a dauka a dawo a taba mata wani abu . sai byn sallah azahar sannan suka bar kebbi daga ita sai kaya kala biyar Tun. Karfe uku ,na ranar har biyar Abdullah yana tare da Dr sagir . Dr sagir ya kalleshi yace haba friend har yanzu baka saduda ba kennan jibi ne za'a daura yakamata ace ka dan ajiye wani abu . tunda dai shi aure yarigada ya zama dole kawai ka saki jikinka , a dan yi wani abu kada ma ka sake ka fito da damuwarka a gane . ,tunda duk aure sunansa aure . Abdullah ya kalleshi ya girgiza kai yace wani aure sunan sa ne kawai aure Amman ba aure bane , yanzu zaka hadashi da auren Aisha koda nake cikin damuwa a lokacin . Amman wlh Allah Allah nake a mallakamin ita na ganta a kusa dani. wannan kuwa baka ji yadda nake jin zuciyata ba kmr zata buga haka nake ji. sannan kace na daina damuwa ina... Doctor nayi asara fa sosai dana rasa Aisha ,. ina sonta ina sonta sosai ina kaunarta har bansan yadda zan gaya maka ba . ina jinta a cikin naman jikina , . doctor ban san haka so yake ba sai yanzu kullum na tuna yaya zataji lokacin da aka bata takardar sakina .. sai naji wani daci ya tsayamin a makogaro. Sai danayi kwana uku bana jin test din komai Idan naci. why why da zan dauki aurenta dana wata daidai ai kai ma kasan fada kawai kayi. Dr Aisha yarinya ce bata san komai ba na rayuwar duniya ,baya ga zama gaban innarta . ,sai da Allah ya hadamu ni koyawa Aisha koma ciki harda yadda zata soni . baka ga yadda nayi rayuwa daita ba komai a nutse take yinsa . Ta yaya zan iya manta ta haka . Abdullah ya runtse idanunshi sosai. hakan ne yasa Dr sagir yaji kwalla ta yakawo a idonsa . nan da nan ya wayance dan kada Abdullah ya Ganshi. Shi kuwa Abdullah samma bai ma lura dashi ba. yace Amman yaya zanyi doctor dole ne ma na hakura daita . gobe ko jibi iyanzu an daura aure na da wata ko daga baya Aisha ta dawo min cewa za'a yi duk abinda nayi daita dole ne nayi da faiza . ni Kuma wlh bazan taba iya rayuwar aure da wata ba bayan Aisha . sai dai wani ikon Allah shine naga da haka gara nasawa Raina hakuri shi zai fi min sauki. tunda safe yau dana tashi jikina yake bani komai ya kusan zuwa Karshe . na sawa Raina ba zan iya yi komai da wata macce ba . to Aisha ma na hakura zanyi rayuwata a haka bbu ita ballanantana wannan . kawai ba komai ba ko..... Wayarsa ce ta katse shi tana kida . Sai da tayi kara sau biyu yana ji . sai daga baya Abdullah yasa hannu ya dauka ya kara a kunne. daga can daya bangaren dady na saukowa daga matattakalar jirgi yace Abdullah kana ina ne? Jin muryar dady tasa Abdullah ya dan natsu yace ina nan gida . dady yace to ai mun iso yanzu ko kai ko wani a samu mai zuwa dauko ni yanzu . Bye bye faiza👋🏻👋🏻👋🏻👋🏻👋🏻 MMN SUDAIS CE [3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗 ZUCIYAR MASOYI 💖💖💖 💗💗💗💗💗 AISHA A BAGUDO Page 63-64 Da sauri Abdullah ya mike zumbur jikinsa har rawa yake yana kiran dady.... dady kuwa tuni ya kashe wayar da gudu Abdullah ya fito Dr sagir ma ya biyo shi yana tambayar sa abinda ke faruwa. A airport ma haka yarinka yi gudu gudu sauri sauri suna yin arba da dadinsa kuwa ya kankame shi sosai . tun sanda wannan tashin hankali ya faru sai yanzu Abdullah yaji hawaye sannan Dr sagir ya karaso shima da murnarsa ya risina yana gaisar da dady . da kyar dady ya bambare Abdullah daga jikinsa saboda hawayen da yake bayason mutane su Gani. Dady yayi mugun kaduwa da irin ramar da yaga Abdullah yayi . koma yace ya lalace ,yayi duhu tamkar majinyaci shekara guda . Abdullah bai iya jan su ba sai Dr sagir ne yayi tukin shi da suna baya . Bbu wanda yasan da dawowar dady a yau hatta shi kansa Abdullah bai sani ba sai da dadin ya nemishi a waya . dan haka tun daga bakin get masu gadi gidan kowa ya fara yashiga taitayinsa . duk da ita kanta mamin bata cikin cikakken haiyacinta Amman sai da dawowar dady ya dan tsorata . bbu wani abu daya nuna na cewar yasan abinda ake ciki to sannan ne yake tambayar Abdullah ya nuna masa shi baya shiga part din kwata kwata . ya dubi

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46