Chapter 17
Chapter 17
mami da ta shigo yana son karin haske cikin dakewa zuciya mami tayi masa bayanin halin da ake ciki har da bayanin a yau faiza ta tafi sokoto Amman jibi idan aka daura aure zata dawo. ga mamakin dukkansu har ita har Abdullah din dady bai ce komai ba illa yace ai yayi kyau zumunci zaki hada . Ya dubi Abdullah kai yanzu ina kake kwana kennan Abdullah yace a gidan baki dady ya sake maimaitawa Abdullah ya amsa haka ne . mami tace ai key din part dinsa sunan hannu teema faiza ta bata ajiya dazata wuce abin ya sake bashi mamaki . Dady yayi shr yana kallon mami ita kuwa ko gezau batayi ba . sai ma ta tashi tayi ficewarta ,dady bai yi mata magana ba Abdullaha ma ya mike ,zai fita dady yace ya koma ya zauna sannan dady yanemi wayar side din su teema ya kirawo bayan yan mintina kadan sai gata ta sake shigowa a tun dazu da suka zo yi masa sannu da zuwa. bai ce mata komai ba. Baya ga tambayar ta key part din Abdullah da akace yana gunta . taje ta dauko ta dawo nan falon dady Abdullah yasa hannu zai karba Amman dady yace A'a . ta Miko masa ya karba yace shikenan teema gud nig . tana fita ya dawo da kallonsa kan Abdullah yace yashiga nan part dinsa ai akwai dakuna ya zabi duk wanda yayi masa ya kwanta a ciki. Abdullah bai gane yadda Dady yake nufi ba iya tunaninsa shi dady zai bawa key part din nasa ya tafi can ya kwanta. Amman sai yaga zura su cikin aljihun gaban doguwar rigar dake jikinsa. Abdullah ya mike jiki a sanyaye yabi dakunan dake bangaren hagu da part din dady yake kwana ya shige ciki. Har gari ya waye dady bai runtsa ba . ita kanta mamin bata sake neman sa ba a daren tunda tabar part din nasa . da safe abubuwa suka cigaba da daurewa dady kai a game da mami . ita dai kawai hidimar biki take gobe daurin auren. har Abdullah yazo ya gaishe shi ya sake ficewa gidan baki bai ce masa komai ba baya ga amsa gaisuwar da yayi. Dama can ya kan dan zazzaga ma'aikatan gida lokacin zuwa lokacin to yau ma haka ce takasance tin karfe goma ya fito daga part dinsa . gabadaya environment din gidan yayi clear. tun asuban fari dan haka daga nan gidan baki ya wuce . Har yammaci ranar bai shigo gidan ba mami kuma bata nemeshi ba shi . kansa Abdullah bai ji wani abu daga dad din nasa ba. dan haka shima office yayi wucewarsa yayi zamansa dan yadda yaga fuskar dady yau ko magana baya son yayi. shi ma acan ya yini duk da anan hutu gobe daurin auren manager koda Dr sagir yazo nenanshi shima sai can ya sameshi . Amman shi Abdullah ya kosa koma me zai faru gara ya faru dan ya riga yasan halin dadinsa. idan yayi irin wannan shr to idan bom din yashi fashewa kowa sai ya shafa. duk da yace ya hakura da Aisha zai iya yi rayuwar Sa haka ko ba macce. Amman itama yakagu yaji abinda dady zaice a game daita. duk da yaci alkawari n dady . bai nemeta ba har gashi dadin yadawo kusan kwanaki dari da yan kwanaki kennan da rabuwarsu Amman har yau yana zaman jiran dady yaji abinda zai ce a kanta . Da yammacin baki suka karaso daga abuja mawaftansu na can abuja wanda mami ta wakilta su zasu je a matsayin waliyan Abdullah. hannu biyu biyu dady ya sauke su . a gidan baki ganin su duk yadada tada hankali Abdullah shi dai yasan muddin ya auri faiza to yayi alkawari yabar Aisha kennan . itama faiza baizaiyi rayuwa daita ba dan haka kasa zama yayi acikinsu dole yabar gurin duk da dady yana lura da halin daya shiga. Aranar ma dady cewa Abdullah yayi ya kwana a inda ya kwana jiya. Abdullah ya nemi su danyi magana har yana koro masa maganar mutane daya kora a company Amman dady ya daga masa hannu yace yaje ya kwanta . zai neme shi akan hakan cikin sanyi jiki Abdullah yatashi ya barshi . Amman a ranar shima kasa runtsawa yayi shi kadai yasan irin yadda ya dinga ji a jikinsa Washegari garin ranar jumma'a kennan da yakama daurin auren Abdullah da faiza. tun da safe da Abdullah ya shigo falon dady . kallo daya dady yayi masa ya gane halin dayake ciki Amman har a lokacin bai ce dashi komai ba. duk da yasan halin dady Amman har yashiga mamakinsa a ransa" Abdullah yayi dan Jim ....yana Jira ko dady zaice masa wani abu sai dai bai ji komai ba. sai da zai tashi ya fita ne dady yace yabashi duka wayoyinsa Abdullah ya dago yana kallonsa da kansa yanuna masa alamun haka yake nufi. Abdullah ya kwaso su duka ya mikawa masa sannan ya fita karfe takwas shima dady ya kulle koina na part dinsa ya fita gidan baki can ya iske Abdullah .. Abdullah ya kwaso abinda za'a bada amatsayin sadakin faiza ya mikawa dady . ,dady ya jima yana jujjuyasu yana mamaki sabon halin da mami ta daukarwa kanta . Abdullah ya nuna masa yadda mami tace ayi kennan. dady ya girgiza kai kawai Abdullah ya fito zai shiga part din dady Amman yaga koina a kulle gashi part dinsa dady ya karbe key. makullan gidansu da Aisha suma suna part dinsa na nan. gashi dan gidan bakin dayake zuwa yana dan hutawa shima su dady suna ciki da baki . yarasa ma ina zashi yayi tunanin tunda yarasa Aisharsa a yanzu duk abinda ya rasa sai yaji tamkar bbu wani damuwa a yanzu ko cewa akayi ya dinga kwana byn masallaci zai iya . Tunanin yayi ya wuce office ya kwanta ya kulle kansa kawai. dan haka ya sanarwa dady inda ya tafi koda za'a nemeshi . tunda yaji mami tace tana son lallai idan an sauko za'a daura aure. can ya yini daga shi sai salis sai ko tsirrarun ma'aikata. har byn sallah la'asar sannan yayi tunanin ko dady ya masa guzirin ne shi ya zauna inyaso su sa tafi sokoto daurin auren . Mami kuwa tun safen ranar ta kasa zaune ta kasa tsaye ba Abdullah ba dadinsa duk wayoyin Abdullah data nema duka a kashe suke. ta aika gidan baki yafi sau goma bbu baki bbu Abdullah bare dady. itama har yamma takasa sanin tudun dafawa dan ko har dady tanema a waya bata sameshi ba. ga part dinsa koina a kulle. sai kusan magariba sannan shima Abdullah ya baro company yasamu sallah a masallaci cikin gidan a sahu na karshe. dan haka shine ya fara fitowa ,yayi gaba kadan musa driver ya karaso da sauri yana gaya masa dady yace ya jirashi to shima dadin din yake son Gani dan bbu waya ne a hannunsa . da tun dazu ya nemeshi tare suka koma har part din dady suka ci abinci dady ya fara shirin yiwa Abdullah bayanin kennan . sai ga mami tamkar anjihota tana tambayar ya batun daurin aure?dady ya zuba mata ido kmr me
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46