Skip to content

Chapter 3

Chapter 3

Zuciyar Masoyi Book Two Complete Hausa Novels 1,157 words 0 views Progress saved
Download Book

karba . Hatta scanning shi yayi mata sannan ya dibi jininta ya auna.. Aunty Maryam ta dawo har kusan uku yana nan gurin Aisha sai da zai tafi sallah ne ya fito ransa a dan bace yana nannade hannu riga zai yi alwala yake cewa aunty Maryam . Kikace sister din kice yarinyar nan tace kanwata ce mana doctor me faru daita cikin fargaba ta amsa masa ya sake dubanta yace tana da aure ne ?. Aunty Maryam tace tana da mana amarya ce ma yace ina mijinta ? Aunty tayi Jim na wani lokaci sannan tace bayanan yayi tafiya me yafaru ne doctor ta fada jikinta na rawa . Ya kara bata fuska sannan ya kauda kai yace ciki ne daita bai kai wata daya ba .. Yacigaba akan samu wasu mata idan sun samu ciki sai suyi ta ciwon ciki . To itama ina ganin tana cikin wannan jarin Amman duk da haka ya nuna ta Sha wani abu ne wanda bai kamata ta Sha ba shine ya sake janyo abun yayi worse har cikin yake kokarin zubewa . Amman Allah yasa bai fita ba . Dr salim ya numfasa yace sai a kiyaye . Ya tsugunna zai fara alwala aunty tayi gaba da sauri zuwa dakin da aka kwantar da Aisha tana zubda hawayen tausayin.. Dr salim yayi shiru yakasa alwala yayi matukar bakin ciki jin matar aure ce duk tunaninsa bata da aure koda ya fara aunata ya gane tana da shigar ciki . Sai dai ya rantse ko cikin shegene daita yana sonta haka.. Bai taba ganin yarinyar da ta tayar masa da hankali lokacin guda ba sai ita . Komai nata irin wanda yake so ne , tunda ya zauna kusa daita kamshin jikinta yake shiga hancinsa da gangar jikinsa shi yasa har bai so fitowa ba . Yaso yakasance tare daita yayi ajiyar zuciya ya dafe kansa yace kai..Kai Kai har sau uku sannan yace Amman dole na bincika idan bbu yadda zanyi dole sai hakuri kowaye wannan mijin nata yamasa shigar sauri ya ja tsaki . Aunty Maryam ma har jikin gadon takarasa tana baccinta ta zauna a gafe ta ruko hannuta ,tana kallonta da irin balain kyan data kara ga ciki . Amman Abdullah ya saketa meyasa ? komai ba jikinta ya canza hatta gashin kanta yafi da tsawo ,fatarta tai balain gogewa daga Gani Abdullah ya jiyar daita dadi Sosai . Ta sake kallon fuskarta tace yanzu cikin Abdullah ne ajikin Aisha ?tana maganar tamkar wanda Aisha ke jinta sai kuma tasa tana goge hawayen dake xubo mata ... MMN SUDAIS CE [3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗 ZUCIYAR MASOYI 💖💖💖 💗💗💗💗💗 AISHA A BAGUDO Page 49-50 Aunty Maryam ta turawa inna cewar likita ya kwantar dasu, saboda har zuwa la'asar Aisha bata farka ba. ga tunanin yaranta a gida . dan haka bbu wani jimawa sai ga inna da usman sun iso zuwansu yabawa aunty Maryam damar tafiya gida . Dr salim yatashi aiki Amma Sam ya kasa tafiya gida ya barta Kuma yana can office dinsa zaune . yayinda tunaninta ke fizgarsa zuwa gareta "dan haka cikin sanyi jiki ya Mike zuwa dakin da take . Kwance take har yanzu bacci take kusan awanni biyar zuwa shida kennan da kwantar daita . A sannan ne ya gaisa da su inna cikin girmamawa. yaji ajikinsa cewar duk yadda akayi jininta ce dan ga tsabar kamanin nan a bayyane hatta namji da suka gaisa yake fada a ransa . Ahankali yakara yiwa inna bayanin ciwon. inna jinjina kai ko kadan batayi kama da masu ciki ba shiyasa tayi ta banka mata abubuwa tana Sha . Dr salim yace Amma ina ganin tana farkawa komai zai zama daidai. inna tace Allah yasa . Yakasa sakewa dasu inna a gurin ,dan haka ya karasa kanta yana dudduba komai ,ruwan magani ma ya dade da karewa ya zubawa fuskarta ido gabansa ya dinga faduwa anya kuwa ba zai mutu ba idan yarinyar nan ta tafi batare da ta zama tasa ba ,. hannuta kawai ya taba wajen zare drip Amman wani abu yaji har tsakiyar kansa. da sauri yayiwa su inna sallama ya fita har ya bar harabar gurin yana shinshina hannushi daya taba nata . Ko minti goma bai yi da barin wajen ba tafara motsi usman yakaraso wajenta da sauri inna ma ta matso kanta. ahankali take bude idanunta har ta bude su duka. har tana kokarin tashi inna tayi saurin kama hannuta ta Mike zaune , wannan tashin hankali data dinga ji acikinta ya ragu sosai. komai ya daina sai sauran kawai dan burbudin mikin ciwo . da take ji ta dafe kanta tana dan kallon su inna , Inna tace kai ko . ahankali tace innarmu jiri nake ji ,tace ba dole ba yaushe rabon da ciki yaga abinci. likita yace kina tashi kici tace ni inna bana son abinci gara ruwan zafi ko kunu. usman ya tashi ya Miko aka zuba mata tasha sosai suna nan tare har mlm abu ya iso da umar suna tambayar jikin nata. Tayi sallar azahar da la'asar tana zaune tana jiran magriba ta karasa yi. jinta take tamkar yanzu idanunta ya bude a tun lokacin rabuwarsu da Abdullah taji ziciyarta na wani irin harbawa da sauri da sauri . ta runtse ido kawai dan ita kadai tasan halin da zuciyarta da gangar jikinta suke ciki a game da rabuwarta dashi Shi kansa mlm sai daya jinjina wannan sarkakken al'amarin wai Aisha ciki gareta ? Kuma har zuwa lokacin ita da kanta bata san da zance cikin ba ,. bayan tafiyar su mlm sai ga aunty Maryam da mijinta aunty takawo musu abinci. shima mijin aunty har ciki yashigo ya dubanta sannan suka wuce sai da inna ta matsa mata sosai sannan ta iya tsakutar abincin. taci kadan tayi sallar ishai ta koma kan gado ta kwanta saboda har lokacin bacci take ji kwananta nawa rabon data tayi , ga shi sunyi mata allurar bacci . Ko kadan batason zuciyarta ta tuno mata da Abdullah. saboda tashin hankali kawai zuciyarta zata shiga ,sunansa ko wani abubuwa da suka yi a dan rayuwar da sukayi tare da juna . Taki yarda ta tuna ko tayi tunani Saboda yanzu hankalinta zai tashi tarikice, yayinda hankalinta da na iyayenta ne kawai zai tashi . ta kudindine jikinta har kanta da bargo Amman sai ga Abdullah din har acikin bargonta yana shashafa mata jiki da kaiwa wuyanta sumba. domin a haka suke kwana ita dashi wai sai taji shi yana tayi mata rada a kunne yadda yasaba tasa hannuta duka biyu ta toshe kunnenta tana mai runtse idanunta gam. Amman still bata fasa jin hannushi a tsantsar jikinta yana sarrafata ba kmr yadda yake manne mata a duk lokacin da suke tare . Kawai taji wasu hawaye masu dumi nabin gefen fuskarta , ahankali take kukanta tana sake felling din tumin jikinsa yasan zai barta meyasa kullum yake mata hudubar da zata so shi , tabbas ita da kanta bata ja akan soyayyar Abdullah tasan zuwa yanzu son shi ne zai yi ajalinta .why why Abdullah why did you do this to me ? meyasa sai da ka koyamin yadda zan soka sannan kabarni "meyasa ka cutar

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46