Skip to content

Chapter 14

Chapter 14

Zuciyar Masoyi Book Two Complete Hausa Novels 1,151 words 0 views Progress saved
Download Book

yamata rahma yasa ta huta, ya raya abinda tabari . Ku kuma Allah yabaku hakurin rashi . Allah yasa idan tamu tazo ,yasa mu cika da kyau da imani Ameen πŸ™πŸΌπŸ™πŸΌ Allah sarki faiza 😭😭😭😭😭😭😭 Page 60 Faiza tace kai mama mutane nan fa sun wuce duk yadda muke zato fa. ta koina abin arziki a jike yake . ba ga mami ba ba ga uban ba hatta shi kansa Abdullah din mai tsansar abun duniya ne . Mama hafsa Tace ke sai yanzu kika san haka kennan . ai shiyasa na tsarawa uwar duk yadda zasu bada sadakin kmr dai yadda suka bada na waccan Yar masu tatsan nono gidaje shida da motoci kinga ai an nininka kennan . Faiza tace kai mama kina wuta ina binki da fetir wlh ta Mika uwar hannu suka kashe. sannan tace ke in banda bana so abin ya wuce wannan lokacin ai da watar kasar za'a kaimu mu zabo kayan gado kinsan su masu fita ne . Sun fi sanin inda za'a samu na garari . Faiza tace dakata mama bangane maganar ki ba .. ai a hakan ma dole ne kayan kitchen lefe da sauran kayan duk a waje za'a siyo su. ai ba wani batun dan za'a yi biki wani a kurarren lokacin. tunda dai ba'ariga an soma raba AV ba. me zai faru abinda ance shi dady sai yayi kusan wata hudu kafin ya dawo. ko ana sauran sati ne ya dawo aka daura ai dai an daura. kuma komai kwakwa da nacin sa dole ya hakura . Mama hafsa Tace haka ne fa . kinibabbe banza kawai , ai ni nafi son kisamu kmr wata daya da aure Abdullah akanki kafin yadawo. sannan nasan mun dan fara tatsan abinda muka tatsa kafin yazo ya hanamu rawar gaban hantsi. akwai abubuwa na musamman dana zan tsumaki dasu. saboda Abdullah din dan haka ana daurawa ,zaki lillike masa ajikinsa sai yadda kikayi dashi . idan ya dandana zumarki kuwa. zai mannemiki har sai kindinga korarsa. Faiza ta saki shewa dan murna hade girgiza nonuwa irin dai yadda manyan yan iska keyi . tace A'a haba dai mama bawani korarsa da zanyi ai sai dai na kwashi da....... can Kuma tayi shiru jikin faiza yayi mugun tsanyi tuno halin Abdullah datayi. mama hafsa Tace karki taba damuwa naga kin wani canza kisha sha'aniki diyata . idai Abdullah ne muna nan zaki zo har nan kibani labari komai. kema ai yanzu kinzama babbar yarinya . Faiza ta mike tana dariya har zata fita kuma ta dawo tace uhm mama kigayawa mami fa ni nafi son mu zauna acikin gidan nan a part din Abdullah bazan zauna a wani guri ba Mama hafsa ta kalleta a bazance tace meyasa ke tsamiyace . ga gida can ke kadai bbu wani dan sa idon da zai dami rayuwarki da takuran yan'uwan miji. komai kuma yayi a gidan sai abinda kike so zaki canza . Faiza ta dan sake rage murya sosai tace uhmmmm ke Abdullah din nan fa da kike Gani bai da kyau fa . ni na fi son ko meza'ayi Gani ga uwarsa . mai sashi yayi mai hana shi ya hanu . yanzu kina ganin duk abinda aka sha wahalar yi a kansa idan ranar da aka kaini ma yaki zuwa fa gidan fa! . kinga tun anan ma wani abun zai karye idan kuma anan ne fa. nasan karyashi tasha karya dole mu kwana tare . Mama hafsa Tace kuma fa haka ne . faiza tace ke dai kice mata ana zamu zauna kawai naga part din nasa ma wata aljannar duniya ce . Mama tace to ni ina zan wani san hakan tunda bashiga na taba yi ba. Kinga haka ma za'a yi bari kiga na koma gunta . Kwana takwas kennan dayin maganar a maimakon ranakun bikin faiza . mama hafsa da faiza da kanwar faiza rahma suka Lula waje hado kayan amarya mami ta bude musu account dinta sosai suyi yadda suke so . Abdullah Yayi shr kansa a sunkuye byn ya gama jin abinda mami ta fada cewar ya rubuta takardun gidaje gudu shida da motoci hawa guda shida a matsayin sadakin faiza. kansa har ciwo ya farayi saboda girman al'amarin Amman ko dagowa bai yi ba yace shikenan mami za'a yi yadda kike so. Fita zai yi Amman ya kasa dole ya dawo part dinsa ya kwanta. yayi shr kullum abin ma gaba yake yi bbu wani sauki acikin al'amarin. sai randa Allah ya kawo . Kwanaki sun shude da yawa komai ya gyaru a ma'aikata. Amman banda bangaren rayuwarsa tunda ya rabu da Aisha bai kuma ganin wani mai kamanin ta ba sai a hoto. Wani lokacin har wani dan shawagi yake yi da daddare akan hanyoyin gidansu . ko gidan aunty Maryam Amman cikin ikon Allah kmr anyi ruwa an dauke ko a yan'uwanta bai taba cin karo da kowa ba . sau daya ne ma ya taba hango umar akan machine traffic ya tsayar dasu. kuma ba a hannun dayake bane kafin yayi wani yunkuri tuni sun wuce. yayi ta hange hange bai ko ga alamunsu ba. Amman ranar ko ba komai ya dan ji dadi har yayi tayiwa masu gadi da ma'akata kyautar kudi balle salis da a rana ya warke . Duk yadda mami tace haka yayi . komai kmr yadda tace haka yayi . Da yayi niyyar sanar da dady sai ya ga kmr idan ya fada tamkar ya kai karar mami ne . dan haka kawai ya kyale tunda dai abun ba gagara zaiyi ba . haka ya bude account ya fidda kudi masu dunbin yawa . kuma yadda ya siya komai na sadakin faiza haka ya kwashi makudan kudin ya zuba a account din Aisha. wanda ya bude mata hatta pin din ATM da card suna hannuta. yabata tun ana gobe zasu rabu bai dai yi mata bayani bane. haka Kuma daman yawanci yana tura mata kudade a cikin salary dinsa. dan shi tunaninsa tana can tana bukata dasu . Ya tuna wata aunty dinsa a Egypt sanda suka je ta kalleshi . cikin yarensu tace Abdullah matarka na da kyau kuma tana da shiga rai . ko zaman mitina biyar kuka yi daita kyaunta da yanayinta mai tsayawa mutun arai ne . Ya dafe kanshi da duka hannuwansa yana jin kmr ya saka kuka ballanantana shi da ya zauna tare daita ya kusanceta yasan dadinta. sannan wai Dr sagir zai ce wai ya rage tunaninta saboda ya rame da yawa ai bbu ranar daina tunaninta sai ranar da aka dawo masa da abarsa . Satin su faiza biyu mama hafsa azalzala mata akan su dawo. saboda shirye shiryen biki. Mama hafsa tayi tayi daita . Amman ina ita kuma faiza ta kafe ita lallai sai tagama abinda ya kawota . dan haka dole tasa mama ta barta . ta fara yin gaba a saboda ta dan yan shirye shirye cikin gidan kuma a fara rabon AV faiza Kuma tayi alkwarin dawowa zuwa wani sati to ba yadda mama hafsa ta iya haka ta yarda . a acewarta dai dama ce tasamu shi yasa ita faizar zata tsaya din . Kai tsaye tsaye ta sokoto mama hafsa ta

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46