Chapter 23
Chapter 23
mike yace yana zuwa . Yana fita Abdullah yatashi ya koma daf da ita" inda take ya zauna har sai da ta dan kalleshi jikinsa a dan sanyaye ya kirawo sunanta bata amsa ba. yarigada ya saba da hakan Amman yasan tana ji yace Aisha lokuta da dama abubuwa suna samun mutun iri iri ya zamo yawanci duk inda ya juya bbu dadi har ya dinga tsammanin ko shi kadai ne ba'a so ... Amman duk wannan ana gwadawa ne a gareka a ga yadda zaka dauki al'amarin kafin daga baya alkhari yasameka. ka dinga ganin kmr kai ake so. yayi shr yana dubanta kanta a sunkuye yace Aisha a da ina tunanin rabuwar da tashiga tsakaninmu mun shiga wani tashin hankali ne na rayuwa. na rabuwar kusanci da mukayi Amman tun yanzu na gane cewa ni kadai na shiga halin tashin hankali Amman ni din ma ga shi Allah ya wanke min da alkharinsa da ban taba samu ba sai a tare dake . Kiyi hakuri dan Allah Aisha komai ya wuce shi kansa danmu sai yafi alfahari idan ya bude ido ya ganmu tare dashi sai yafi yin farinciki . har alokaci bata dago kanta ba hawayen takaici ne duk ya dameta a idanunta . kawai Abdullah zai sake dawowa ya yaudareta tana zaman zamanta lafiya ahankali yasake kiran sunanta ta dago suka hada Ido ganin da yayi zatayi kuka yasa ya dada rikicewa ya kara matsota sosai kmr zai cire mata abinda ke damunta . Matar Dr ta fito tana ganinsu haka da sauri ta juya ta koma . su duka biyun suka bita da kallo har aka kira sallah magariba har sannan bata ce komai ba Abdullah kadai ke maganarsa ita taji ta hakura da abinda a kamata ya wuce har a cikin zuciyarta . Amman ita kam bata kara yarda Abdullah ya Kuma yaudararta ta kuma komawa aurensa. anan gidan sukayi sallar magrib har isha'i matar Dr sagir tayi saving dinsu abinci Amman shi Abdullah kasa ci yayi ganin har yanzu Aisha taki sakin ranta bare ita da tun lemun data dan kurba a tun dazu da suka zo da sister zahra. har Dr sagir yana magana yace gaskiya Aisha abun naki zai zama da Kwara fa saboda bake kadai kike cin abinci ba idan baki ci ba na jikinki ba zai samu ba Abdullah ya kalli Dr sagir sannan ya juya kanta ya zuba mata ido yakoma kalar tausayi Dr sagir ya sake fita falon ya kara zama su biyu Abdullah yace Aisha tashi mu tafi na kai ki gidan inna. Shr bata amsa ba sai daya sake dan matsota sosai yace kinga fa dare ya fara zamu takurasu . Sai alokaci ta kalleshi itama tayi tunani haka tun farko ba dan zata takurasu ba ita ko akan kujera zata iya kwana. tunda dai tasan Abdullah ba zai barta ta fita ta je gida ba .. da kansa ya nuna mata yes haka ne. yace kinga damu zauna muna shiga hakkin wani gara mu tafi maganar ta dan shigeta dan haka ahankali ta mike. ganin ta mike ne ahankali ya dan sauke numfashi sannan shima yamike yana kiran Dr sagir tare suka fito da matarsa da kyar Aisha ta kakaro murmushi karfin hali tayi mata sallama sannan tayi gaba abinta Abdullah kuwa suka jiro tare da Dr sagir hannunsu rike da juna suna magana da sauri Abdullah yakarasa ya bude mata kofar mota ta dan jima tsaye kmr mai tunanin kada tashiga. ganin dukkan idanunsu akanta yake yasa tashiga suka sake yin musabaha da Abdullah sannan da sauri ya zagaya yashiga dayan hannun ya tayar da motar Dr sagir ya sunkuya yana mata sallama Amman tayi banza dashi dan tasan duk dashi aka hada kai wajen rai namata wayo . Ganin inda Abdullah ya tsayar da mota ne yatashi hankalinta ainihin gidansu na aure ne idan ba gezo idanunta kemata ba ai kuwa tana tabbatar da haka ta saka mishi kuka wato wani wayon ya sake mata ahankali tace ni gidanmu zaka kaini gurin innarmu haka kace . Abdullah ya gyara parking ya juyo yana kallonta ganin ya tsayar da motar yasa tacigaba da kukanta . Ahankali yace Aisha har yanzu baki hakura ba ?tace ni gida zaka kai ni sai da yayi wani tunani sannan ya rage murya yace kinga Aisha tunda kika baro gida na koma na gaya musu cewar zan biya na sauke ki dan haka duk su baba sun san yanzu kin gidana Aisha ta zaro masa ido tana yimasa kallon tsoro ya sake cewa kin san aurenmu ya maidu tunda nace na maidake yanzu matsayin matata kike . Ai kuwa ta sake sakar masa wani sabon kukan tace ni bazani gidanka ba. ni gidanmu zani yayi shiru sannan yace to shikenan kiyi hakuri kiyi shiru . Ta dan tsagaita kukanta yace kinga yanzu duk su inna su san muna tare tun karfe uku yanzu byn dare ya fara su ganmu mun koma musu . me yuwa sun fara bacci baki ganin zasu dauka ko wani abun ne dan haka kiyi hakuri zan kai ki wani gida can ma gidan yan'uwane . ki kwana inyaso Gabe sai naje na daukeki na kai ki gidan yafi muje musu da wannan daren. tayi shr tana jinsa ya Kuma cewa kiyi hakuri muje can din duk gida ne a gurinmu shirun tayi ta sakeyi shirun da tayi ya fahimci ta amince . Dan haka ya juya kan motar . Masu gadin gidan suka bude musu get kafin ya karasa filin inda motoci suke yayi parking sannan ya dan kalleta yace ina zuwa ya fita can gurin masu gadi yana kiran yahuza ya karaso da hanzari daga inda yake dana tunda ya hango shi din ne yataso . Abdullah yace yaje ya bude part dinsa . ,key din ya amsa da sauri ya tura cikin aljihunsa ya tafi ,. Abdullah na nan na jiransa har yahuza ya dawo ya Mika masa key ya karba yasa a aljihun wandonsa na baya. Iya tunaninta yasa ne ayi musu iso kafin su shiga cikin gidan. daga inda take tana hangensa yana magana da yahuza. Amman bata iya jin abinda yake fada a saboda tana daf da inda injin yake faman aiki . , Abdullah ya karaso ya bude mata kofar motar yana yi mata magana da kyar ta fito. shi kuma ya hade fuska kmr da gaske tamkar bashi ne ke lallabata ba ,tana fitowa ta dan tsaya tana kallon tsarin gidan ahankali tace ina kuma ya kawota? ita dai ta taba hange gidan gwana ta waje Amman bata taba shiga ciki ba. dan haka tasan tun daga waje gidan ya tsaru iyakar tsaruwa fitilu ne suka haska koina kana Gani yadda wajen ya dau haske ,da duk kannin alamu ba gidan mutun daya bane saboda bangare bangaren da ta Gani . ita tsoro ne ma ya kamata har gabanta yana dan faduwa . shiyasa ta tsaya tana kalle kalle dan ta gane yadda gidan yake ,ita bata san inda Abdullah ya kawota ba. dan haka ta dinga binsa ahankali ahankali har suka shiga part dinsa wani irin kamshi ne ya doki hancinta. ba kamshin turare bane kawai naturaly ta saba jinsa a jikin da Abdullah ,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46