Skip to content

Chapter 12

Chapter 12

Zuciyar Masoyi Book Two Complete Hausa Novels 1,156 words 0 views Progress saved
Download Book

ne su gwaggo laure da matar mlm dahiru ne suka zo dubata yadda matar mlm dahiru taga jikin gabadaya cewa tayi zata wuce daita can ka'oje saboda yinin ranar cur ciwon ciki ya dawo sabo ko iya tashi batayi. ga bala'in yinkurin amai tamkar dan zai fito ta baki . dan ita gwaggo laure dan tausayi har kuka tayiwa Aisha. ranar da zasu Wuce da safe takin cin komai ga yunwa tana ji kmr tayi hauka komai wari yake mata in dai a gidan aka dafa shi . a sa'a sai ga aunty ta turo mata da dafaffen wake da kawai da ganye shi ta dan samu taci tana murmushi tace aunty ta huce kennan . inna matar mlm dahiru kuwa da taga taci sosai sai kawai ta juye mata sauran acikin Leda suka wuce. Amman kafin su kai ka'oje duk sai da bata ina motar da amai saboda warin man mota da yake cika mata ciki . a motar har wasu na jin haushin yadda take bata musu guri. yayinda wasu kuma ke tausaya mata . MMN SUDAIS CE [3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗 ZUCIYAR MASOYI 💖💖💖 💗💗💗💗💗 AISHA A BAGUDO Page 58-59 Tunda suka rabu da Abdullah duk daren Allah sai tayi kuka rashinsa musamman inda tazo kwanciya . gara ma da rana idan tana tare da mutane bata cika tuna shi sosai ba. ita da kanta bata sanda soyayyar Abdullah tayiwa zuciyarta mummunar illa ba sai a wannan lokacin . barin ma irin rayuwar da take ciki ayanzu. yasa tafi tuno shi sosai akan da musamman yanzu daga ita sai inna matar mlm dahiru . mlm dahiru yawanci shi ke siyo mata duk abinda take son ci, in da har yafi can gidansu a kebbi kennan. Duk abinda take bukatar za'a tafi nemo mata shi. kuma ba laifi takan dan cin abinci inna . da kansa mlm dahiru ya matsa a kaita asibiti da kyar dai Aisha ta yarda suka je .domin daman acan kebbi bata son taga Dr salim shiyasa taki bin aunty suje . har aka mata fadan rashin zuwa asibiti inda akarshe suka rubuta mata magunguna sosai dazata dinga Sha. Da yammacin ranar tana zaune mlm dahiru yashigo taga ankama dan marakin anfita dashi aka siyar. wai ashe magani za'a a siyo mata da kudin . Karo na farko data bude handbag dinta da minal ta bita dashi tun ranar da Abdullah ya saketa ,. ta zazzago abinda ke ciki har da check din da Abdullah ya taba bata lokacin suna Germany na miliyoyi kudi . ta zuba musu kudin jiki ido ya isa ya kawo maganin karshen duk wani bbu . Amman ita basu take so ba kuma basa birgeta tafison sanya Abdullah kwayar idanunta . yafi komai mahimmanci a gareta. ta tuna rayuwar da suka yi dama haka kawai lokacin sai tarinka jin zaman su ba me dorewa bane. saboda ta koina abin bai zo daya", kawai taji hawaye ya shiga bin fuskarta . Tana kukanta Inna ta leko tace mata zata shiga makwafta tayo musu barka" dayake bbu wuta a dakin sai Yar fitilar kwai " yasa inna bata fahimci abinda take yi ba. tana fita kuwa ta sake barkewa da wani sabon kukan tasa hannu ta shafo cikin nata tace ko yaya Abdullah zai ji idan yaji zata haifa masa da ko "ya ? . ,Ta tuna wani kokarin can da suke American ya taba ce mata Aisha idan kika haifa min Yar bby mace zanyi ta ttalinta sosai zan koya mata gayu " ita kuma tana kwance akan cinyarsa tana dariya . yace Allah musamman idan nasamu tayo kama dake ..Kai ai sai wanda nagadama zan bawa tayi, ta sake yin dariya tace to idan namiji aka haifa fa ? kake wannan abun yace kinsan ance duka gadon haihuwa yawanci daga na namiji ne. to kinga ni Kuma duk gidanmu matane ni kadai ne namiji . dan haka killa nima da mata zan fara. sai kiga wata rana nima ana min layi a gida wallahi sai na duba nutsatten siriki . Tasa dariya tace uban "ya" kennan yace yes haka ne . yana dariya itama tana yi . To sai dariya ta kubce mata tamkar a lokacin suke maganar tana kukan tana dariya. har tadan kware kadan ai ko nan da nan ta fara Tari ta fito waje da sauri tana yunkurin amai . ai kuwa sai data amayar da duk abin ta ci tana haci ta kwanta anan kasa gashi inna bata nan . tana kwance kusa da Aman sai data huta sannan ta mike da kyar ta dan kora ruwa sannan ta rarrafa ta koma daki ta kwanta . aranta tace kowa yazo yaga jikinta ko dazu ma daga zariya dangin babanta sunzo . Amman Abdullah yaki zuwa yaganta shikenan Abdullah da gaske ya daina sonta. a da ko dan begewa tayi sai yaji kmr ajikinsa yaji . idan rashin lafiya take" yi yake tamkar wanda zaiyi karamin hauka. tun bata damu dashi ba har yazo yakoya mata yadda zata so shi . gashi da shiga rai ko yaya kake tare dashi sai yasan yadda ya faranta maka. Amman lokacin daya gashi yanzu ya mata ciki ya barta da damuwarta ita kadai wanda ahalin yanzu tafi bukatarsa fiyye da komai. ita Tama sanya shi a idanunta koda bazai cigaba da sonta ba . tayi kuka sosai . abin tausayi ita da kanta bazata iya tuna sanda tayi kuka irin haka ba. tayi fushi da Abdullah da bakinta tace in Allah yaso ko waye Abdullah tabar shi . ahankali take cewa Abdullah na barka na barka dama kai kasa na soka yanzu kuma tunda baka sona ka barni. nima na barka in Allah yaso har abada bazan kuma barin sonka yay min illa ba. har inna ta dawo ta leka ciki tayi kiranta Amman shiru batayi magana ba . inna ta dauka ko ta dade dayin bacci ne shiyasa ta kyaleta. ita ko har lokacin hawayen rabuwa da son Abdullah take da tunaninsa . Tun ranar kuwa yadda tayi alkwarin haka ce takasance dan ko sunansa bata sake tunawa ba. abinda ta kaddara ranta daman can ai bata san shi ba . daga baya ta san shi yanzu kuma tunda ya wuce shi kennan . duk abinda ya danganceshi ta barshi. inna tana lura daita" yanzu nan zaku sha hirar cikin nata Amman da zarar ka bullo da zance uban cikin zatayi cikin cikin da rai tabar zance. koma tayi kwanciyarta ta kudundune har kanta . Haka kawai kuma taji Allah ya daura mata maseefar kaunar abinda ke cikin nata. taji tana son duk abinda zata haifa din. dan haka lokuta da dama idan tana zance cikin inna har fada take mata . wai su anan basa yin haka acikin fari . dariya kawai zata dingayi inna a ranta kuma tace ita wannan innar daukar kowa take yan zamanin su . Dr salim ya riske su biyu bai yi tunani ko ba ita kadai bace. ya dubi aunty Maryam idansa jawur. sai faman huci yake yace sister yanzu akan ina son yarinyar nan. yasa kuka dauke min ita kuka bar garin kwata kwata daita. aunty ta dinga kallonsa wani irin tamkar me shirin dukankata . Cikin zafi

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46