Skip to content

Chapter 18

Chapter 18

Zuciyar Masoyi Book Two Complete Hausa Novels 1,150 words 0 views Progress saved
Download Book

shirin shiga iska sannan yace tasamu waje ta zauna . da kyar ta zauna din shi kuwa Abdullah kansa a sunkuye yake yana zaune kan karfet . Dady ya dubi mami da kyau yace maganar daurin auren na dageta daga yau. kuma na sallami kowa kmr yadda kika amincewa Abdullah to haka itama yarinyar da iyayenta sai naji daga garesu na farko kennan tunda shi kika soma nema . abu na biyu kuma nagode nagode da wulakanta min diyar yar'uwata da kikayi . abunda ni bazan taba yi miki ba kennan har duniya ta nade a tunanina yarinyar ko b daga jinin take ba yakamata mata ki mutuntata A saboda tana auren danki . Amman duk na gode . abu na karshe kuma da zan sanar miki yarinyar da kikayi kokarin raba Abdullah daita. to ina yi miki albishir itace zata fara kawo miki jika a gidan nan . Gabadayansu suka soma kallon dady ,dady yana murmushi sosai ya kalli Abdullah yace Aisha na dauke da ciki tun lokacin da kuka rabu . haka tazu iyayenta suka bani tabbacin "sanda tabar hannuka ciki dake tare daita bai kai wata ba zuwa yanzu abinda da ake hasashe cikin ya shiga wata hudu . Sauran kadan Abdullah ya narke a zaune a gurin saboda yadda yarinji a jikinsa. hawaye ya fara zubo masa yana kallon dady da mami duk a lokacin daya. fuskarsa ta nanu kmr ba daidai yaji abinda yace ba. sai Kuma ya dinga murmushi yana zubda hawaye . duka abubuwa masu mahimmanci a lokacin guda . dady ya kalleshi yana masa murmushi shima dan tsabar abin farinciki da yajiyo ne yasa shi manta bakincikin abinda mami tayi masa . Kuma ya fita a zuciyarsa . Mami kuwa ta hade fuska tamau dan ita maganar takaici ta kara mata . ta cewa dady ni ga abinda nake son ji takamaimai Amman ka fara min wata magana can . Abdullah ya juyo yana kallon bakin mami tace shikenan hujjarka ta hanawa a daura aure a yau. kana son mama hafsa tace banyi mata ba daidai ba kennan . dady ya kalli Abdullah yace shikenan Abdullah zakana iya tafiya abunka . sai na nemeka Abdullah ya mike dady ya kwaso wayoyinsa ya bashi . har kusan tara na daren ranar mami na tare da dady tamkar wacce ranta zai fita daga jikinta tana fadan akan hana daurin auren dady yayi . ita ba ma kowa take ji ba cikin al'amarin sai mama hafsa . abinda ya kara girgiza dady kennan . yadda take maganar cikin tsanyewar zuciya tana kuma fada masa duk abinda yazo bakinta kmr ba mijin ta ba . yasan ta sosai tsahon shekaru da suka kwasa tare . Amman bai santa da hakan ba. ransa idan yayi dubu to duk yayi kaca kaca ya baci ya dubi mami sosai yace aure tsakanin Abdullah da yarinyar nan na haramta shi . sai dai bayn raina mace daya na amince masa itace yarinyar da kika sa shi ya rabu daita sai dai kuma idan daga baya shi yayi ra'ayi dan kansa . idan har da wani abu da zai faru to ni ishaq ina jiransa . gashi nan ubangiji yana shirin nuna miki ikonsa a jikin yarinya . Amman kin zauna kina hakilon banza. dan haka duk abinda zai faru ya faru Allah yasa yankaki hafsa zatayi akan rashin yin auren to Bismillah. Maganar ta Sosa ran mami matuka fiyye da tunanin mai karatu. dan haka itama ta rinka fadar magana iya yadda zata huce. ta kara da cewa randa duk mama hafsa ta tako gidan nan dole ayi wacce za'a yi . Kuma wlh dole dole ayi yadda take so a karshen ta cewa dady kuma bazata taba amincewa da wasu can su lakawa Abdullah cikin banza ba. byn ya rabu da yarinya sama da wata uku a dawo ace wai ciki gareta me yasa tun lokacin basu fadi hakan ba sai a yanzu . mami tana huci ta kada kai ta bar part din dady ya zubawa kofar data fita ido "ko kwakwaran motse kasawa yayi. saboda dacin da yake ji na bacin rai a wuyansa idansa yayi jawur tamkar zasu fito. me yake shirin faruwa ne dashi da rayuwar gidan nasa . yana nan zaune har tsawon mintina talatin bai bar gurin ba teema ce tashigo ta kofar da mami ta fita.. tana yi tana kallon bayanta . kallon ta dady yayi . Ya jima sannan ya dan hadiye miyo mai dacin daya tsaya masa a makoshi. yace yaya dai teema . Teema takaraso kusa dashi ta zauna. yana kallonta Tace dady mami ce sai kwalla ta fara cika mata ido yace ya isa meyafaru da mamin ? teema Tace dady kwata kwata mami ba ita bace ba yanzu . kowama baya gabanta a yanzu . dady mami bata da ra'ayin kanta a yanzu ta sake fashewa da wani kukan. Dady ya rufe idonsa sai da ya barta ta danyi kukan sannan ya dakatar daita . teema ta dan goge hawaye . ta dan sharbe majina tace abin tsoro ma dady mami fa yanzu ko ibadarta bata gabanta sai tayi kwana biyu ko uku batayi ba. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun abinda dady yake fada a ransa kennan yana cikin tashin hankali abinda mami ta gama yi masa a dazu . sai ga teema tazo da wani "duk akan mami ya zubawa teema ido kawai ya kasa magana "yasan teema da natsuwa ya Kuma san yadda suke da mami. koma meye zata iya fahimta. tace na kula da haka sosai yanzu ibada ba a gabanta take ba . ita dai a yanzu duk yadda zatayi ta farantawa wannan mama hafsa shitakeyi . Teema ta dan kalli kofar data shigo ta rage murya sosai. sannan ta kara matsowa kusa da dady tace ni dady ko wani hali mami take ciki ina ganin akwai sa hannu wannan mama hafsa din. tana da alhakin a ciki saboda ranan nan naji tana cewa mami wai iyayen aunty Aisha sun mata asiri ita da brother Abdullah . dan haka ta kawo wani abu tabata tace shi zata dinga garwashi tana turara jikinta dashi kullum . Brother Abdullah kuwa ta bayar da wani abu baki a Leda wai a dinga masa abinci dashi . wai duk asirin daaka musu zai karye. kuma ta dinga jadadda mata sosai tayi kada tayi kuskure yin haka . mami ta dinga yi wani lokacin ita mama hafsa da kanta ke karba tayi mata . Dady ya zubawa teema ido sanda ta dago tana kallonsa yace Allah dai yasa teema ba labewa tayi ba ta ji abinda iyayenta sukeyi ba . atsorace ta kalleshi idonta cike da Hawaye tace wlh dady ba labe nayi musu ba . ita mama hafsa din ce idan tana yin wani abun sai kaga kmr bata Gani. duk abinda zatayi wani lokacin muna gurin zatayi . Amman wannan da naji din ma ina bedroom din mami ne "a kwance ta shigo ta Sami mami ta dauka ko ina bacci ne . take gaya mata ahankali. rannan kuma ina wanka ta hawo da sauri take cewa faiza wai ta zubawa brother Abdullah din maganin kuwa gashi can za'a tafi kai masa abinci "tasan ance kada

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46