Chapter 2
Chapter 2
tayi hade saki hannunta ta shiga cikin dakin nata ta dauko hand bag dinta ta biyo ta dashi . wanda a wannan lokacin har ta nufi get , minal tace direban dayakawo su mami yabita . yakaita ka tabbatar ka kaita gida . zaiyi magana ta nunashi da dan yatsanta tana huci tace wlh idan baka kaita ba idan dady ya dawo a bakin aikinka. Tuni ya tsorota da maganarta dan yadda yakeji dadin aiki gidan idan ya rasa shi ai ji zai yi tamkar ya rasa ransa. minal kuwa sai kwafa take tamkar dai yadda dady yake idan ranshi ya baci . Dole tasa direba yabi bayan Aisha wanda har tayi nisa a tafiyar kafa . Minal ta koma ciki ta riske mami tana kuka dama ita kadai ta biyo su . ahankali tace mami meyasa kikayi haka byn kinsa kema kina da ya'ya mata , yanzu idan mu akawa haka wazakiji ....meyasa ma kike kinta byn ita din jininmu ce cikin sheshekar kuka ta juya ta bar falon mota tashiga ta tuka da kanta. da hannuta da bai gama kwarewa ba. dady ma ya hanata tuki Amman ba yadda taiya . Da taimakon Allah tazo gida . ita kuwa mama hafsa dadi goma da shirin kafin wannan gadddafin uban nasa ya dawo sai dai yatadda faiza a gidan haka ta rayawa aranta . Koda ya sauketa da taimakon Allah tashiga lungunsu . Amman tana shiga gidan ta yanke jiki ta fadi bbu wuta a garin lokacin. ga sanyi kowa na ciki daki . usman ne ya fara fitowa da kyandir yana haska jin alamun faduwa .ai kuwa yaga Aisha kwance shame shame. nan da nan ya jefar da kyandir din hannunsa yasa ihu . Allah yasa kafin kyandir din yakara kasan ya mutu . ya shiga kiran su inna kafin ma yayi wani yunkurin sai gasu gabadayansu banda aliyu har da mlm abu . inna ta kamata agigice yayinda gabanta ke dukan tara tara suka dagata. usman kuwa sai kuka yake yana kiran sunanta . a dakin inna aka kwantar daita . gabadayansu bbu wanda ya runtsa aranar. Gashi taki yiwa kowa magana. inna ce ta dauko rigarta ta sanya mata ganin yanayin ta jikinta ta bacci ce. bata boye komai na jikinta ba. sai da safe ne ma ya umar ya tsinci takardar sakin nata a zaure inda ta fadi . Tun zuwanta sai yanzu aka fara gane kan al'amarin Amman har yinin ranar bbu wanda tayiwa kwakwarar bayanin abinda ya faru. saki dai gashi nan a rubuce anyi shi. mlm abu yake tambayarta itama iyakar abinda ta iya cewa kennan . sakinta yayi bbu wani bayani data kara akan haka . duk tsawon lokaci bbu wani mai cikakken sukuni a gidan. mlm abu yace inda Allah ya rufa asiri shigar dare tayi bbu wanda yaganta da sun dada shiga uku ga masu zundensu sun siyar da yarsu . Ko magana bata iyayi dama can yaya . kafin dare kuwa sai zazzabi har da frigita. haka suka kwana a kanta cike da tashin hankali . mlm abu yana mata tofi a ruwa ana bata . da safe ma cutar karuwa tayi sosai har da su ciwon ciki wanda shi yafi matsa mata ma alokaci . Bbu wanda yasan da zuwanta sai isu isun su. sai ko da yamnar da inna ta turawa aunty Maryam cewar tazo Aisha na gida ba lafiya ,to a ranar ma ahaka suka kwana dan ciwo cikin har yafi daga masu hankali sosai duk dauriyarta in tana ciwo. Amman sai da inna tasan cikin ya damunta sosai. inna ta jika mata kanwa ta bata har ungurnu duk zafinta sai da tasha. Amman still ciwo sai gaba yake kafin asuba har suma ta dinga yi ya umar ma sai da zubda mata kwalla. kafin safiya ta farfado Amman duk tafita haiyacinta kallo daya zaka mata tabaka tausayi. kuma har a lokacin cikin bai daina ciwo ba. da safe mlm abu yake cewa inna kawai ina ganin zuwa gobe su tafi daita can ka'oje gara tayi zamanta can kyauye. gurinsu mlm . yana ganin ciwon nata akwai alhinin wannan mutuwar aure ciki . can mlm dahiru ya dinga mata rubutu dangana tana Sha. Inna tace haka za'a yi . ma tsira ma daga surutun mutane. Aunty Maryam ce ta katse su da sallama tashigo suna gaisawa da mlm abu tana tambayar me jikin . yaya yusif ya shigo shima da kunun gyada mai zafi a kwano ya siyowa AISHA . Dan yaji inna tace Sam taki cin komai. da kansa yashiga ya zauna a gefenta ya tsiyaya a Kofi yace ta tashi tasha . daga rufar inna take jiyo mlm abu yana yiwa aunty Maryam bayanin abinda ya faru . A rikice aunty Maryam din tashigo rumfar inna tana zabga salati ganin yadda Aisha takoma cikin kwana biyu . Ganin kashirban yasa aunty Maryam kuka. inna ke kara mata bayanin rashin lafiya. aunty tace ai inna ina ga asibiti kawai zamu tafi yanzu . duk wannan jike jiken ba zai yi ba . daman can zan tafi na biyo naga jikinta nata. idan yakamata mutafi asibiti sai mutafi .. Usman tasa ya nemo masu taxi da kyar AISHA ta iya daga kai ta kalli aunty Maryam tace ki barni kawai aunty zan warke a gida . tace dan Allah tafi can kina cikin daki ne zaki warke. baki fita an nemo miki magani ba . A irin kayan data bayar arabawa mutane lokacin aurenta akwai ragowa guda biyu . su aunty ta karba gun inna tasa mata. suka fita har da yaya yusif . da kyar ta iya kai kanta baki titi . Yayinda cikin nata ke dameta . Yana sake murdawa . ta rike cikin sosai tana cicije lip's dinta . Suna isa kai tsaye aunty Maryam tasa aka wuce daita gurin likita.. MMN SUDAIS CE [3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗 ZUCIYAR MASOYI 💖💖💖 💗💗💗💗💗 AISHA A BAGUDO Page 43-44 Suna isa kai tsaye aunty Maryam tasa aka wuce daita gurin likita . Doctor salim shine akan duty da haka da saurinta tace doctor taimaka kanwata ce bbu lfy mun rasa gane kan ciwon nata .wani irin ciwon ciki ne yake damunta . Ita kuwa Aisha a lokacin ji tarinkayi tamkar mutuwa ce tazo mata saboda balain ciwo dake ji ajikinta sai zufa take hade da tsinkewar zuciya . Tayi sharkaf a gado dr salim ya karaso kanta ya zuba mata idanunshi sosai tayi kmr batasan yana kallonta ba nan da nan yace a sauya mata daki . Yaba ta taimakon gaggawa , ya jima yana checking dinta sannan ya daura mata drip din magani . Allurar bacci aka mata sannan ya fito yana sake tambayar aunty Maryam game da ciwon tana masa bayani a karshe tace bari taje tayi reporting a bangaren su ta dawo. Dr salim ya dawo dakin ya zuba mata idanunshi sosai bacci take Amman daga Gani tana jin jiki ya dinga kallonta kmr wata halitta ce da bai taba ganin irinta ba . tamkar diyar wasu manya ko kusoshin gwanati a cikin Nigeria . Ya jima yana dube dubensa da aune aunensa Amman gabadaya kacokan hankalinsa ya daura akanta . Ragowar marasa lfy ma wani likitan ne ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46