Skip to content

Chapter 29

Chapter 29

Zuciyar Masoyi Book Two Complete Hausa Novels 1,178 words 0 views Progress saved
Download Book

boka shine komai yadinga dagulewa "Abdullah ya zubawa dady ido sosai mamaki karara a fuskarsa. da kyar ya iya cewa dady ita mama hafsa ce tace haka dady yayi murmushi takaici ya'yanta ne suka fada ciki har da wacce da ake son ka aura . Amman ita sai daga baya ta amince ta fida duka abinda kunne ma ba zai iya ji ba saboda kazanta . Duk zance batansu da kake ji . suna hannun yansanda ni nasa a tsare min su sai zuwa lokacin da naji na amince da natsuwar komai . saboda abin nata yazama har da rainin wayo a ciki "Abdullah ya sake runtse ido. yace oh shit yana girgiza kai dady ya dan sake murmushi yace maminka daga wata kasa na daukota har zuwa nan inda muke zaune . bata da wani anan sai ku bbu wani nata da , zatace zata kyautatawa ya ji dadi . domin zuri'arsu" ba irin masu neman taimako bane sai dai kawai kayi musu dan farantawa Amman tunda na wayi gari naga ta amincewa wannan hafsar a matsayin yaruwata. nima naji na amince kuma ina musu iyakacin karfina "ko bada sanin maminka ba . Amman idan kaga cikin dajin da hafsa ta kai mamika sai kaji tsoro sau biyu ana zuwa daita da police "Amman bata gane wajen . ance akwai aikin sihiri ciki "shiyasa takasa ganewa addu'a kawai za'a cigaba dayi . Dady ya kalli Abdullah da yayi tagumi kmr an masa mutuwa yace Abdullah kayi wa "maminka addu'a kaji . Abdullah ya daga kai dady yace daman nayi mamakin randa ka min bayanin sakin da tasa kayiwa yarinyar nan . duk da nasa bata son yarinyar Amman nasan tana shakkar abinda,zai sa naji ba dadi. byn tafiyar ku Germany fa mun zauna daita sosai akan haka a karshe ta nuna min ta hakura da komai "har na matsa mata tasa muku albarka kuma nasanta nasan halinta idan tace tayi hakuri akan abu to da gaske take "shiyasa da'aka tashin yin abun aka biyo ta hannuta daman kuma ita tun filazal akwai rashin son abun a ranta shine komai ya dada kwabewa Allah dai ya shirya mana . Cikin sanyi jiki Abdullah yace Ameen dady yace sai maganar tafiyarka Denmark komai ya kammala Abdullah ya dago suka hada Ido da dady ,. dady yace aiki zaiyi yawa sosai byn tafiyar ka musamman game da zance da na gamaka yanzu "hankalina gabadaya ya tafi ne kan neman natsuwar maminka . saboda akalla itace mai rike da gida Abdullah yace haka ne " dady yace bbu komai inshallahu komai zai warware. Cikin sanyi jiki Abdullah yace Allah yasa. dady yace Ameen shiyasa maganar wancan result din yarinyar nan Aisha da Dr sagir ya baka na Adana su har zuwa lokacin da zata dawo daidai. sai maganar interview da za'a sabbabin ma'aikata" ina son ka fara da alhj aminu waliyin Aisha ranar Monday dan nafi son kayi masa da kanka "inyaso sauran koda baka samu damar yi musu ba" har tashinka yazo shikenan . Daga part din dady na mami ya wuce ya dade a gurinta yana kallon yanayin rayuwar maminsa" shi da kansa ya zabarwa kansa tafiyar nan Amman gashi tazo masa a lokacin da bai so . Baya son ya tafi yabar maminsa cikin wannan halin ya fison ya tsaya kusa da dady ayi komai a idonsa. sai dare sannan ya iya barin part dinta . Koda dawo gida yayi duk abinda ya zama na al'adarsa ya zauna shr "Ita kanta Aisha ta fuskanci akwai matsala a tattare dashi dan har suka zo kwanciya. duk sai taji ta damu ta kasa hakuri dan haka ta dame shi da tambaya ahankali ya juyo ya zuba mata rikitattun idanunshi masu kashe mata jiki tarinka jin wani irin ajikinta" still bai dauke idanunshi daga gareta ba yacigaba da kallonta. gabadaya ba abinda ya shafi bangarenta bane dan haka ba yadda za'a yi ya sanar mata" kawai ya janyota ya hadata da kirjinsa yana shafa kasan cikinta zuwa mararta yana jiyo tudunsa a jikinsa. MMN SUDAIS CE [3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗 ZUCIYAR MASOYI 💖💖💖 💗💗💗💗💗 AISHA A BAGUDO Page 73-74 Abdullah ya dauki ya'yansa ya gane dukansu"maza ne "ya musu addu'a sosai doctor yace saboda yanayin jikinsu dole a sasu a kwalba musamman saboda halin da mahaifiyarsu take ciki a halin yanzu" Amman banda haka da dumin jikinta kadai zai kara musu kwari. Har kusan la'asar Aisha bata farfado ba har ta Wuce kaidar yadda ake tsammanin alokaci. koda babanta ya sauka ya isketa tamkar matacciya. sai dai addu'a kawai ya dinga mata . A can ma dady murna ba gida kadai ya tsaya ba har ma'aikata anji manager Abdullah ya samu karuwar tagwaye. musamman dady yasa aka dinga sauke alqur'ani mai girma a gidan ,akan Allah ya farko da mahaifiyar yaran . Dady shi ke kara karfafawa Abdullah zuciya ta waya ba kowa Allah yake bawa baiwa irin wacce yayi masa ba. shi dai yayi ta addu'a" haka Abdullah ya rinka yi ga murna ya'ya yasamu ga tashin hankali rashin farkowar uwarsu" har zuwa washegari ranar 'wanda shi kansa ruwan dake aiki a jikinsa ya kusan kafewa, saboda tarin zullumi da fargaba. mlm abu ma shi ke dan tausarsa wani lokaci . Gashi duka bbys din nasa suna kwalba bare ya rungume abunsa yaragewa kansa tension koyasamu wani abin yacigaba da aiki ajikinsa. ga Aisha duk na,urori sun kewayeta itama bbu halin yaje kusa daita ya dan ji duminta jikinta. komai ya tsaya cak a tare dashi sai dai ko numfashi. can ma innarta duk abinda take Aisha na ranta . Gabadaya hankalinta a tashe yake kuma ya tattara ne akan halin da diyarta take ciki. dan su ko zance haihuwar basu ji ba har zuwa wannan lokacin. usman kuwa kasa zama gidan yayi ya shiga dakinsa ya kwashi sabbabin takalmansa da siyo kwanan nan ya kai ya siyar" kudin ya sai kosai da waina yayi sadaka dasu" akan Allah yasa ya Kuma ganin ya'yarsa a rayuwarsa . "zuwan da,akayi aka tafi da baba abu shi yafi komai tada musu hankali dan inna cewa tayi mlm abu kawai ya tafi kawai bazata iya zuwa ba . sai a ranar laraba" kwana uku kennan da haihuwar ,da sanyi asuba Abdullah yashigo asibitin tunda ba'a kwana musamman da yake bangaren haihuwa ne duk da yake dakin ita kadai ce" yana shigowa jiki a sanyaye ya zauna kan kujerar dake kusa da gadonta ya zuba mata idanunshi shi kadai yasan yadda yake jinsa a halin yanzu" tsawo lokacin yana zaune yana kallonta ya runtse idanunshi tsantsar kaunarta ce da tausayinta suka hade masa alokaci daya .yasa hannu ya zaro hanky daga bayan aljihun wandonsa ya goge hawayen daya zubo masa ,ahankali ya zaro hannuta dake hade da injin din jikin na'ura ya hada da nasa ya kifa kansa a jikin gadon yana murza hannun sannu sannu " Allah kadai yasan daidai Amman likitoci cewa suke zata farfado, yake fada a ransa. Sai ya dan ji kmr ta motsa hannu daya rike dashi ,yayi shr yana son ya sake ji" can yaji kmr atishawa agigice ya dago kai da sauri a sanda take sake yi wani" a agigice Abdullah ya saki hannu da sauri. har

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46