Skip to content

Chapter 31

Chapter 31

Zuciyar Masoyi Book Two Complete Hausa Novels 1,176 words 0 views Progress saved
Download Book

yake kallonta dan har wani tsoro tsoro taji yana shigarta , ahankali ya sauke numfashi hade lumshe idanunshi murya a dashe yace Eh da dai bata san tare muka taho ba" saboda lokacin da muka zo din bata dan jin dadin jikintata ne" Amman yanzu ai tasani tun da gashi taji zuwansu affan. ya dago habarta ya hada goshinta da nasa yace bata zo taga jikinki ba ko ? Kiyi hakuri nasan zata zo ne su teema kuma exam sukeyi suna gamawa zasu zo tayi shr bata ce komai ba . Yana kallon kwayar idanunta dake sake hargitsa masa tunani. ahankali ya sake cewa kiyi hakuri fa. ta girgiza kai ni ba haka nake nufi ba "yace ko ma me kike nufi dai nabaki hakuri kizo muyi baccinmu . kinga yara har sunyi ya kai bakinsa ya tsotse lip's dinta " sannan ya mikar daita tsaye hade da mannata da gefen jikinshi yana sake duban yanayin ta . Lokacin da su teema suka zo Denmark alokaci Adnan bashi da wata ishashiyar lafiya" gashi duk abinda daya yayi to sai shima dayan yayi" ko kuka ne ko fitsari da kashi dan haka affan din ma ba wata cikakkiyar lafiya ce dashi ba . koda yaushe suna asibiti karo na farko kennan da teema ta taba ganin Aisha . cikin lokacin kadan suka shaku da juna sosai abunka da jinin daya. duk da teena ta girmi mata Amman tana bata girmanta na matar yayanta su. affan kuwa yi suke kmr zasu hadiye su musamman minal idan tana renansu sai abun ya birgeka. hakan kuwa nayiwa Abdullah dadi kafin tahowarsu har hotuna sukayi da yaran dan ma rashin lafiyar da sukeyi yasa suka dan rage wani abu . satin su uku suka baro Denmark alokaci su affan sun kusa wata biyu. tafiyarsu teema yasa komai ya sake cakudewa Aisha domin jikin Adnan ya sake yin tsanani haka shima affan din yana rashin lafiyar sai dai bai sosai ba. dady ma ya zo byn tafiyar su teema ya duba su. Abdullah kwance akan doguwar kujerar dake falo idanunshi a runtse kmr mai bacci yace a ransa kowa yazo yaga abinda ya haifa ya duba jikin Aisharsa' Amman banda mami , fushin mami ba a kansa da Aisha kadai ya tsaya ba" gashi har yaran da basu san komai ba ya shafa. ya sake runtse idanunshi sosai yana jin wani irin a ransa. Rashin lafiyar Adnan tasa har Aisha ta fara fitar da rai dasu " dan sau Tari idan taji shr sai ta dinga taba kirjinsu taji ko suna numfashi . Duk da akwai masu kula dasu sosai Amman ita da Abdullah basa barin yaran a gurin ma'aikata ko bacci bata barinsu suyi ga yawan kuka kuma Adnan ne yake farawa sai affan ya kama shima' a tsakanin wannan lokacin Aisha ta rame sosai ga rashin lafiyar yaran da rikicinsu ga rigimar uban gayya Abdullah " dan tunda yaga ta samu sauki ya hanata sakat" wani lokacin tayi ta kuka a daki ko idan su affan sunayi kuka itama sai zauna gabansu tana taya su , gashi lokacin Abdullah bawani zaman gidan yakeyi ba yana gurin aikinsa. Haka ta dinga rayuwa wani lokacin har gara su affan din ma akan babansu" dan su da zaran sun Sami bacci shikenan . shi kuwa idan tana rokonsac ya kyaleta sai yace dan bata son shi ne shiyasa bata damu da hakan ba "shiyasa kawai taga gara ita ta hakura masa yayi duk yadda yake so daita , ta tuna zamansu a boarding ta taba jin wasu kawayeta suna labarin wai daman shi balaraben mutun akwai shi da son yawan jima'i ,duk da shi Abdullah ruwa biyu ne Amman bai bar komai daya danganci hakan. kuma ta amince da haka sai da su affan suka samu cikakken wata biyar da haihuwa sannan Adnan ya fara samun sauki shi kuwa dama affan ta Adnan ce ta shafeshi tuni ya warwaare. Sannan taji an fara , zance komawarsu gida nan da wata uku nan gaba. ta kagu taje taga su innarta sosai har yanzu inna bata san su affan ba take fada a ranta watansu biyar suka zama tamkar basu ba dan har an fara zaunar dasu a kekuna sai gashi Adnan ma ya riga affan iya zama wai har yana kamo abu yace zai mike. ita kanta Aisha a wannan lokacin ta dan samu sauki abubuwa saboda Abdullah idan ya shiririce a tare dasu affan sai su kwashe lokacin mai yawa suna tare "wani lokacin sai dai tazo ta tarar affan ya kwanta a kan hannusa Adnan kuma a saman cikinsa "duk sunyi bacci sai dai ta dan gyarasu itama ta samu inda zata kwanta anan kusa dasu. Ahankali take gane tsansar kamannin su da ubansu hatta dimple din kumatunsu musamman affan da idan ana masa wasa yana dariya sak Abdullah " na Adnan ne bai fito ba Sosai. mai yiwuwa dan shi bai cika yin dariya sosai bane . Watanni su bakwai lokacin kuma su Abdullah watan su tara kennan a Denmark aka fara musu shirin komawa gida' Aisha tana cikin murna da doki dan bata taba dadewa haka a rayuwarta batare da taga danginta ba. kawai Abdullah yazo yace ma Ankara sati uku akan tafiyarsu gida saboda za'a kayatar da bikin company daya zo dominsa, kuma shi ake son zai yanka igiya sai party da za'a shiryawa su affan. saboda shine dama tun farko yaki ganin basu da isheshin lafiya. Aisha tayi kmr ta basa masa ihu dan takaici ta kasa magana . to yadda ta raina abun har tana korafi . sai dai abun yabata mamaki matuka dan an shirya abin sosai ya kuma kayatar har ya birgeta . anyi bikin bude company, Abdullah ya yanke igiyar shiga byn ya karbi kyaututtuka akalla masu mahimmanci dan nuna kwazon aiki" adviser da sauransu har da tsaftar kayan hada aiki" shi kansa abin yazo masa a bazata" inda a jawabinsu har suna neman ya dawo garin da zama ya rike company. Aisha najin haka sai hankalinta ya tashi addu'a kawai take kar Allah yasa ya amince da haka ta fada a ranta . Kwana biyu tsakani aka shirya parting su affan. alokaci Sun shiga watanni su na takwas kennan Adnan yana tafiya har da dan gudunsa affan kuwa bai iya ba sosai sai idan yaga dan'uwan yana tafiya shima sai ya rinka kokarin Mikewa yana farawa daya biyu zai fadi yana kuka shi kuma Adnan yana ganin haka duk abinda yake zai bari shima ya taho ya kama shi yana kuka . a haka suke birge mutane da shiga rai ranar da'aka shirya musu party su na haihuwa kusan kowa yayi hotuna dasu, yaran sunyi kyau sosai da sosai kowa yana Sonya dauke su idan ka kalli Aisha kmr karbosu tayi "dan ba alamun ko daya da nuna ko ta taba haihuwa bare ace ita ta haife dukansu. har hoton family sunyi ita da yaran da babansu an bawa yaran kyaututtuka har Aisha ta dinga tsorata da abun ,sutura gasu can a gida Amman wanda suka samu a gurin har yafi na gida. dan akwai kayan da zasu kai akalla shekaru sha biyu kafin su soma sawa. kuma komai iri daya wasu kuma kudi a envelop dollars

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46