Skip to content

Chapter 11

Chapter 11

Zuciyar Masoyi Book Two Complete Hausa Novels 1,150 words 0 views Progress saved
Download Book

jikin naki Abba yace baki da lfy . Aisha ta dan langwabar da kai tace to da sauki kennan sister . daga can suka dan yi shiru sakina tace a she sister kun rabu da Abdullah kuma ? duk son da yake miki Aisha tayi shr bata kalleta ba ta sake cewa me ya faru ne har haka da zafi har ya kai gayin saki . Aisha ta kalleta tayi murmushi takaici tace haka Allah yaso zaman ne iya haka. sakina tace haka ne Amma ba haka aka so ba. abin ma har da abin alajabi wai sister ciki gareki ? .. Aisha ta sake yin murmushi itama sakina dariya tayi . tace koda yake ke ai kin haye kin cigaban arayuwarki . tunda da wani zai samu irin taki . ai da yayi tsalle da kukan murna "Aisha ta dan dago ta kalleta tana mamakinta . eh mana sister dubi yadda kika zama ke kinganki kuwa . kinga kyau da kika kara . sai dai Yar rama . itama ina ga ta rashin lfy ce. na farko kennan kin auri miji mai kyau gashi zaki haihuwa da shi dan Abdullah ko daga nesa mutun ya hange shi . dole ya tabbatar da kyaunsa . kinga kuwa ina tabbatar miki danki ko "ya" zasu yo kama dashi . Aisha ta kalleta sosai ita fa haka take kullum a na cikin magana daita yanzu nan zata subuce wani gurin tamkar Yar fari . haka ta fada a ranta ahankali tace sister ke abinda Dame ki kennan ni ban Dame ki ba ko sister? Haka ranar da za'a tafi dani ma guduwa kikayi kika barni sai yau na sake ganinki . gashi yanzu kinzo, komai ma ciwo yake min Amman kina maganar wani abu na daban can . sakina tayi saurin rike hannuta dukka tace sorry sister ayi min afuwa . MMN SUDAIS CE [3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗 ZUCIYAR MASOYI 💖💖💖 💗💗💗💗💗 AISHA A BAGUDO Page 56-57 Da farko Kamar bazatayi laulayi ba, Amman kwanaki kadan laulayi yazo ya sata a gaba ko ruwa tasha baya zama acikinta. gashi duk nisan abu idan ta kafa ranta shi zata dole taci dan idan bata ci ba sai taji duk cutar duniya kanta ta dawo ,. kuma har dare bazata iya cin komai ba idan ba shi din ta samu ba wani lokaci har kuka take yi . Gashi duk kinta da tunanin Abdullah sai da maraicinsa ya taba ta. duk ta rame ta dashe tayi fari fat. idan ta fara kakarin amai kuwa tamkar hanjinta zai fito. magana ma wani lokacin da kyar take iya yin sa . da kafar ta ma tafiya take dan yawancin duk unguwar an san da a yanzu tana gidan maganganu kuma iri iri bbu wanda baya tar dasu. Ita sai daga bayan nan taji bayan tafiyar su da Abdullah. dadinsa ya dauki nauyin hidimar makarantarsu yaya yusif da duk abinda zasu bukata. akwai mutun na musamman da aka daura akan haka . a yanzu haka akarkashin I M sidi magaji yaya Ali ya tafi NDA Kaduna ,. sai gidanjenta wanda aka mallaka mata cikin sadakinta wanda tun bata dade da dawowa gida ba, da mlm abu yamata maganarsu . Amman tace ita wlh gabadaya tabar musu Amman suna nan a rufe har yanzu ba abinda akayi dasu . takardun ma suna gun alhaji aminu . motoci kuwa ko yau suke so za'a kawo musu daga company dan haka duk wannan a idanun mutane suke har yau surutai ake a gari ballanantana da yanzu aka ga tana gida . Aunty Maryam tazo da yammacin wata lahadi suna gaisawa da inna daga kitchen inna ta fito sai da ta samu gurin zama sannan take mata bayanin . yawan zuwan da Doctor nan yake yi. inna yayi shr tana sauraronta hade da kallonta aunty Maryam. cikin tuhunna inna tace nifa abin har tsoro yake bani kullum ne sai yazo wai yazo dubiya ai ina jin kalla yazo gidan nan ya kai kusan sau talatin. Mlm ma da kansa abin ya dame shi . Aunty Maryam ta dan langwabar da kai tace to inna yaya zanyi. na rasa yadda zanyiwa doctor "can ma idan kinga yadda yake yi min sai kiyi mamaki "tun bana bi ta kansa har na hakura. shi inna wai ita yake so da aure har cikin dake jikinta . inna tayi murmushi kawai dan ita har yanzu ranta Abdullah take so da diyarta ,aunty tace baki ga abinda abun ya zame masa kmr wani ibada yazo kullum ya tambayi lfyr ta a gurina kafin ya fara aiki. ,har na rasa yadda zanyi da nacinsa . inna tace haba nasan za ai haka abin yayi yawa fa da idan zaizo fa ke baki ga abinda yake tahowa dashi ba . daga baya da muka fara fahimtar haka aka daina karba, aunty Maryam tace wlh ni kaina basan ya za a bullo abin ba ,. gashi da bin diddigi maseefa ni fa kawai zuwa ya yi yace min wai kuna gaishe ni . ban san ya'akayi yasan gidan nan ba .. Inna tace a to rayuwa kuma iri iri kowa da irin tasa Amman shi yana daukar abu tamkar yanzu ne ,. dan wani lokacin idan yazo ma bai ga kowa a kofar gida ba . sai yafi awa bai tafi ba aunty Maryam tace ai shi bai ki da cikin a daura musu aure ba ko ayau ,inna ta rike baki. Aisha na daga daki tana jiyo su ita dama ta dade da gane hakan . tun a ranar zuwansa na farko da inna ta matsa ta je tsoro wai yazo ganin jikinta. yana mata yan tambayoyi akan jikin Amman ta fahimci sarai me yake nufi . ta Kare masa kallo tsab ,bai da laifi sai dai Abdullah dinta ya fishi komai nisa ba kusa ba ,shi Abdullah ma dazakaga jikinsa tamkar na bby sabon haihuwa sabo tsabar kyau gashi gentle man . Amman shi wannan sai tsari da iya magana kmr wani lauya. haka ta karaci kallonsa ta bar shi nan tsaye . daga ranar ko magunguna ya aiko tasha na masu ciki bata sha sai dai tayi wasi dasu dan ita basu take so ba tafin so ta jita karkashin Abdullah dinta ta lumshe idanu sakamakon yadda tarinka jinsa yana yawo ajinin jikinta . Aunty Maryam ce ta shigo ta katse mata tunani . ta zuba mata ido tace kai Aisha haka kika kara zama dubi idanki fa . Ta riko hannuta tana dubuwa . tace har kin fi da dashewa fa duba kmr mara jini a jiki. inna takaraso da kunun tsamiya data dama mata tace nima dai kallon haka nake mata aunty tace wlh ma haka ne inna ai sai muce tare kawai an jima in yaso da safe muje asibiti a dubata. cikin muryar kuka tace ni aunty ki barni kawai ba inda zan je wani dube dube . Aunty Maryam tace ji ikon Allah kina cuta kina cewa a barki . kinsan ma ko ba haka ba yana da kyau ki dinga zuwa asibiti saboda abinda ke jikinki . Aisha ta bata rai tayi sosai tace nifa bazani ko ina ba a barni. har aunty Maryam tayi fushi daita. Washegari

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46