Chapter 13
Chapter 13
itama tace kaga dakata doctor abin fa bai zama na daga harshe ba. Aisha dai ba yarinya bace" ba kuma igiyar kowa akanta "dan haka tana da right din da duk inda taga zai fiyye mata dadi dole taje . Dr salim ya dubeta yana dan murmushi idansa har neman fidda kwalla suke dan tsabar bakinciki. cikin Yar kwausashiyar murya yace sister Maryam kina daya daga cikin masu neman salwantarmin da rayuwa kennan . tunda har kina goyon bayan barin Aisha garin nan. saboda an san ko ban ganta ba idan naje kofar gidan na tsaya ina jin duminta a jikina tunda nasan tana cikin gidan. shine dan bakin ciki kika sa hannu akabar garin daita saboda ki kuntatamin ko . wata kawar aunty Maryam da suke zaune tare "tace haba doctor duk me yakawo wannan ko menene ma yana da kyau abi" abun cikin sauki mana. ya dube kawar aunty Maryam ya watsa mata wani mugun kallo wanda yasa tayi tsit da bakinta . Yace ai dukkanku dakikai ne shiyasa baza ku gane kan abun ba. Amman muddin ina da karfina da lafiyata da hankalina bazan yarda na kasa magance abinda zai cutar da rayuwata ba '. ya ja tsarki mai tsawo sanann ya juya kan aunty yace nakan kyale abubuwa da dama su wuce ni koda zasu dame ni bazan nema ba, saboda ban cika son na samu matsala a rayuwata ba. nakan share koma menene bana bari yakai zuciyata. dan bana son ya dameni Amman tunda naga Aisha sau daya na tabbatarwa kaina tawa ce . ni kadai wani ne kawai yarigani yamin shigar sauri . a yanzu kuma ya barmin ita tadawo gareni sannan kuma sai na bari wani yasake min shigar sauri. ke kinsa impossible Aisha ta shafi komai na rayuwata . dan haka zan iya damun kowa na tashi hankalin kowa akanta . ciki kuma har da wanda bai sona daita . kmr ke ba ya nuna aunty Maryam da yatsansa. dan haka sai ki kiyaye ni wlh bai tsaya jiran wani abu ba yayi gaba abinsa. Aunty Maryam ta zuba masa ido . Wanda idanta har rawa rawa yake saboda takaici da ganin ikon Allah na Dr salim. Sai da taga wucewa tace to ba sai kayi duk abinda zakayi ba. ka tashi hankalin duka duniya ma, kagani kai ma idan bata hade da kai ba. banza kawai . kawarta ce ta dafa kafadarta . tace kai haba ya isa haka mana wai duk mai me ya kawo haka ne? Aunty Maryam ta numfasa tashiga yi mata bayani tace kinji wani ikon Allah kuma. shine bai sani ba dan ko a lisafin Aisha bai ciki. Da zai zo ya damu mutane iface iface. Ta sake mai da hankalinta sosai kan kawarta tace dan tana yawon tunanin tsohon mijinta ne shiyasa aka tafi daita ka'oje. shine zai zo ya dinga wa mutane bala'i ko an taba so da karfin dole ne" oho" tace ai tunda aka dawo dashi asibiti nan" nake masa kallon irin yan kaidan nan . ga girman kan maseefa da fadin rai . Shiyasa rananan fa har ina mamaki da yazo har inda muke zaune "daku aka gaisa" ya wuce ashe ke da biyu yasa yayi haka. Aunty tace biyun ma. Idan mai yuwu wa ne ba . ai ni wallahi har cikin Raina nafi kaunar Aisha takoma gidan Abdullah. dan idan akayi auren da irin wayan nan. Akwai matsala dan wannan irinsu duk randa zafin zuciyarsu ya tashi har ita Aisha zai yiwa duk son da zai mata . Ita kam Aisha tana can ka'oje tana fama da laulayin karamin cikinta ita ko sunansa ma . bata sani ba ballanantana ko me sunan shi taji ta dan tunoshi. ta rame ta koma kmr baita ba shiya dan cikin nata ya fito a wata uku zai yashiga na hudu. sannan tafara samun saukin laulayi "da yawan amai duk ya ragu kuma tana iya cin abinci duk da tasamu . sai dai har yanzu akwai kwadayi iri iri musamman na yaji . A washegari ranar ne su usman sukaje ka'oje dubata" shida aliyu da yazo hutu daga Kaduna suka tarar inna tayi mata kwadon zogale tana ci usman yana tare daita yayinda aliyu kuma ya tafi zariya kala kala gunsu iya. sai inna dake can tana dora abinci rana usman ya dinga kallonta bbu laifi tayi kyau Gani sosai kmr ba sati uku da suka wuce tazo ba. yana kallonta shi da inna haka ya sata a gaba tamkar ya dawo da cutar jikinsa haka yake ji . ya zubawa abinda take ci ido yace wai ko yajin bakya ji zafin sa . sai karawa kike yi idan yajin yayi yawa bazaki gane dadin abu ba. Ta dan kalleshi kadan tace kaine dai baka san dadin ba. ai duka wani dadin duniya anan yakare. usman yayi dariya sosai har inna ta karaso tana tambayarsa ita ma tashiga dariya tace kaga duk randa wannan baturen zai zo ganin dansa sai yayo min buhun barkono . Aisha ta bata fuska inna tayi shigewarta daki tana kara cigaba da dariya. usman ya tashi ya dibo mata ruwa a randa yazo ajiye mata kusa da kwano "usman ya dubeta sosai ahankali yashiga gaya mata irin borin haukan da Dr salim ya dinga yi musu saboda ta tahowarta . saboda balain naci daya dinga yi musu a waje yana aike har sai da yaya Ali yace wa baba wlh idan bai tafi ba kuma bai daina zuwa ba . zaiyi masa duka ko yasa ayi masa usman ya dan yi dariya yace kinsan kuma zai aikata bare yanzu da yake soja .. Usman yayi dan shiru ko zata ce wani abu Amman Shir batayi magana ba. sannan ya dan sake yin murmushi kadan yace Amman wlh yaya Aisha ni nafi sonki da yaya Abdullah dan kunfi dacewa da juna . haka koda mukayi zance da innnarmu tace tafi sonki da Abdullah koba komai danta ne . kuma tasan bashi da wani laifi akan rabuwarku . dan tasan sharrin maminsa. wai wata killa tsanar da tamata ne. ta shafeki in gaya miki innarmu har da kuka tayi a jiya daza Muzo . Sai alokaci Aisha ta dago da sauri ta kalleshi har ta katseshi shima yana kallonta duk abinda daya zata ko itama daman tafinson haka ne. sai dai ,tana gama kallonsa yaji tace innarmu mantawa tayi tace zata dakamin yajin tafarnuwa kuzomin dashi . Usman yasanta sarai kadan daga cikin halinta kawai yayi murmushi yace me yiwa ko sai zata zo . Idan ka kalli rayuwarta a ka'oje baza ka taba tsammanin ta taba zuwa ko da airport ba . bare taga jirgin da zai fita daita waje . Yadda ta karbi rayuwar kauye itace zata sanyaka ka fadi haka abinda ta kaddara daman rayuwa tana iya canzawa na wani lokacin" abinka ga mai ciki , kuma tana samun abinda take so nan da nan ta murje kyau. kyaunta ya fara dawowa har ma yaso yafi na da .... MMN SUDAIS CE [3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: πππππ ZUCIYAR MASOYI πππ πππππ AISHA A BAGUDO Inna lillahi wainna ilaihi rajiunπππππππ Ina Mika ta'aziyyar gaisuwata ga yar'uwa faiza anfa marubuciyar danfashi ,akaro na biyu Allah ya jikan gwaggonki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46