Skip to content

Chapter 25

Chapter 25

Zuciyar Masoyi Book Two Complete Hausa Novels 1,178 words 0 views Progress saved
Download Book

idanunshi ya dade Zaune a falo bai shigo bedroom din ba . tana so tayi wanka saboda kayan jikinta sun dameta "Amman takasa tashi" anan kan gado ta kwanta tana jin ba dadi aranta" shr shr bata ji motsen shigowarsa ba sai har bacci yayi gaba daita. da safe karfe takwas sai gashi har yayi wanka ya shirya cikin kananan kaya sai kamshi yake zubawa " ya hawo har kan gadon da take. Ahankali ta mike zaune tana kallon yanayinsa . ya zuba mata ido tana so ta gaishe shi Amman tsoro yasa "ta kasa magana "Ko har yanzu yana fushi daita? ya gane nufin ta dan haka ya lalubo tafin hannuta ya matse cikin nasa" yayi murmushi kadan yace gud morning my dear "yaya bby jiya laifi abbansa ya shafe shi ko ? Ta dago kai tana kallonsa yace humm ya dan langwabar da kansa yana murmushi" itama kawai sai tsinci kanta da mayar masa tayi murmushi hade da sunkuyar da kanta. ita duk tunanin abinda tayi masa jiya ya hanata sukuni "sai gashi shi har ya manta ahankali yakira sunanta yace Aisha a jiya nayi tunanin tunda dai har da gaske baki sona baki son zama dani.... .dan haka take taji gabanta yayi wani irin faduwa jikinta ya dauki rawa " har yana jin yadda jikinta ke shaking" Amman share yacigaba da magana yace har gashi ya janyo a jiya mun dan samu matsala dake shine na yanke yi miki abinda zai kwantar miki da hankali zan mayar da ke gurinsu inna har sai kin hakura da laifin da na yi miki" acan zakiyi komai da kike so , kuma shi kansa bbymu sai yafi samun natsuwa " ahankali ta sauke numfashi tana runtse idanunta "dan ba . abinda tayi zato bane. can hankalinki a kwance yake to yanzu kuma da safen nan munyi waya da dady yace kiyi hakuri "zai dawo yau zaizo da kansa ya baki hakuri. kada ki tafi ta dago tsumammu idannuta ta zuba masa a tsorace take kallonsa tana girgiza masa kai cikin frigice da nadama take kallonsa kmr zata sa masa kuka "cikin tsanyi murya tace haba Ab..dul..lah me yasa kake min irin haka ni " sai kuma tayi shr ganin yadda ya tsareta da manya idanunshi still hannunsu na cikin juna" yana mammatsa mata yatsunta "ahankali tace ya zaka gayawa dady zai yi magana" ta fara girgiza masa kai" ta fara hawaye tace Abdullah yanzu dan dan wannan abinda ya faru shine zaka gaya masa ya sake riko hannuta Sosai yace ke kike kallon haka Amman tafiyarki ba karamin abu bane wajena. bbu yadda zanyi ne shiyasa kawai nayi tunanin na mayar dake din "saboda abin ne " ke neman yafi karfina yazanyi da Raina laifina na neman ya jamin maseefar " da zata shafi dana . Tacigaba da kuka cikin rawar murya tace ni .. Abdullah idan za munyi duk abinda za muyi ,muyi mugama "Amman mu daina sa dady a ciki kawai yana zamansa zamu sako shi" ransa yazo yana baci . ni dan Allah kayi hakuri kace masa na hakura . ya sake dubanta sosai ta bashi sha'awa takara kima sosai a idonsa wannan ya nuna cewa tana girmama mahaifinsa "yaji dadi har cikin ransa" ya langwabar da murya yace to shikenan kiyi shiru ki daina kukan tunda kince kin hakura "tayi shiru kmr Jira take yace oya goge hawayen banson ganin su" da sauri tashiga goge fuskarta da bayan hannuta" yasa hannu shima yana kara goge mata" sannan ta kalleshi tace kace yau dady zai dawo , mu kuma fa ? Yace mu ma muna nan part dinmu " ki kwantar da hankalinki kowa part dinsa daban fa, ahankali ya dogota ya mikar daita tsaye" ya kamo hannuta suka shige har ainihin dakinta da dady yasa aka kara saboda ita ,wanda faiza ta lafta kaya ciki" suka shiga ya zaunar daita kan gado yace kinga dakinki ta dinga kallo tana mamaki irin yadda aka tsara dakin hatta kayan shafe duka gasu nan zube akan mirrow "dady yace ya mallaka wa mata komai na dakin tunda da kudinsa aka siya "sai kayan lefen yasa a kwashe yace a zube su a wani guri "zuwa wani lokacin duk zai rabar dasu ( hummmm nace idan da masu so sumin magana oooo😜😜lolz ) Ta juyo tana kallonsa ya dan daga kafadarsa yace idan bai miki ba sai a canza" takasa magana ya mike yana cewa dady zai dawo yau idan bai dawo yau ba "may be sai gobe su dawo tare dasu mami" gabanta ya shiga faduwa ta kira sunansa ya dawo ya tsugunna gabanta yana kallonta cikin murya mai kusa da kuka tace gara mu koma can gidan "ya dubeta sosai yana dan nazarinta ya gano abinda take tsoro yace any way duk inda kike so" na amince in dai muna tare. kishirya yanzu muyi breakfast sai mu koma can gidan, yasa hannu ya dago habarta yana kallon kwayar idanunta yace gabadaya kwayar idanunki cike suke da tsoro Allah yasa kar wannan tsoro ya taba lafiyar bbyna . Ya koma lip's dinta ya dan tsotsa yana lumlumshe ido yaushe rabon daya ji taushin su "ahankali ya juya ya barta" tana kallon ikon Allah bata tashi a gurin ba sai gashi ya sake shigowa rungume da wasu kaya da jaka ya zube kayan akan bed tsarabar ki na tun tafiyata Denmark kafin muyi aure" na siyo miki sanda na dawo kuma ban samu ganinki ba "sai byn aurenmu ta zuba masa idanunta tana kallonsa sai yanzu ta lura da irin ramar da yayi ya kula da irin kallonsa datake ya dan kashe mata idonsa daya da sauri ta dauke idonta yayi murmushi yace ina jiranki sannan ya fita . Har suka shiga falon wancan gidan nasu na ainihin aurensu tana lura da yadda yake binta da mayen kallo duk ta tsargu ta damu. Abdullah yakamo hannuta ya janyota jikinsa atsakiyar falo suka zube kan kujera yana sha cikinta yace kinyi kyau sosai Aisha komai kikasa sai ya dace da jikinki ". ta zame jikinta ta zauna sosai akan kujera ya dawo ya tsugunna gabanta ya kara zuba mata ido sosai har sai da ta kalleshi "ta dan haharesa kadan yace Aisha ina son zuwa wani guri ta yamutsa fuska ya lura da hakan bazan dade ba " fitar da zanyi ta kamani dole ne shiyasa Amman dan Allah ki kular min da kanki komai akwai na bukata tun jiya akayi clear din komai . To Abdullah bai dawo gida ba sai byn magriba duk ranta dagule a bace yasameta ko magana ta kasa yi "saboda barinta yayi ita kadai "har yasa tarinka tunanin da sake sake abubuwa da dama a kansa "har tana ganin wautarta na saurin amincewa da zama dashi "saboda ruwa kawai zai sake mayar daita . A kallon fuskarta da yayi ya gane ya karasa da sauri dan kar ya sake karawa kansa laifi. dan haka yashiga lallabata hade da rararshinta yadda zata huce Amman taki sauraronsa har lokacin bacci yayi. Yana falo yana kallonta har ta fito daga wanka cikin kayanta da tabarsu anan" ciki ta zabo night gown lemon Green mai shegen kyau ta saka sabuwce "a ledarta ta bare"ta tana tsaye tana gyara gashin

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46