Skip to content

Chapter 38

Chapter 38

Zuciyar Masoyi Book Two Complete Hausa Novels 1,151 words 0 views Progress saved
Download Book

ashirin ba'a dauka ba "dan haka hankali a tashe ya baro office yana zuwa yashigo ya tarar da takarda sun tafi gurinsu minal yaje can da daddare ya dauko su . Ahankali Ya kamo lip's dinshi na kasa yana cizawa ya runtse idanunsa laifinta ya sake ka ruwa "gashi tasa direver ya kai su alhalin tasan koina zasu je yafi son shi ya tuka su da kansa ". ,bai wai dan wani abu ba shi dai kawai yafi ganewa hakan " . kai tsaye gidan nasu ya nufa ya samu tana saman su teema mami tana ciki dan haka ya shiga ya dan ga mami kadan har take mamakin ganinsa a lokacin office" ya nuna mata bbu komai. ya fito falo yayi waya saman su teema ita ce ta dauka daga baya sai gata ta sauko ta sameshi a falon mami "ta matso kadan kusa dashi ta zauna idanunta gabadaya sun canza kala saboda kuka. ya kalleta sosai fuska a hade har taji ziciyarta na wani irin harbawa". yace kinzo kigayawa mami abinda yake faruwa ne ko ? Ta kalleshi a tsorace saboda yadda yayi maganar ta haka ya gane bata fada din ba ". yace idan har kika kuskura kika gaya mata zaki karawa kanki wani abin ne na daban kawai , ya tashi ya Mike yayi gaba abinsa . . Taji kmr ta jawosa jikinta ta rungume taba shi hakuri . ita bazata iya da rigimarsa ba .. Affan ya biyoshi ya dauke shi yayi gaba dashi "Aisha ta zubawa bayansa ido har sanda ta daina ganinsa sannan ta sauke idanunta taji hawaye na zubo mata. tana jin motse shigowa nan da nan ta hau goge hawayen. . mami takaraso falo . Yadda mami ta ganta ta kara shan jinin jikinta tasan akwai abinda yake faruwa a tsakaninsu. daman tunda ta ganta sannan taga Abdullah din yazo yanzu tasan akwai wani abu . batace mata komai ba sai da ta bari har zuwa dare sanda yazo tafiya dasu sannan take tambayar sa Tasa aka kirawo Aisha samanta, tana zaune kanta a sukunye. Ahankali muryasa a sanyaye yace wai kin ganta nan mami saboda tana da ciki shine duk tabi ta tashi hankalinta tasa damuwa a ranta . Mami ta kalleta da kyau tana fara'a sosai. tayi Yar dariya farinciki tace to menene na damuwa ?. ta sake yin dariya tace na san dai matsalar ba zai wuce khalifa ba . "ni idan an dada kwana biyu a kawo min shi "tunda yana tafiyarsa yana cin abincinsa " ita ko Aisha gabadaya nauyi da kunya mami sun hanata dagowa.. mami ta kira sunanta ta kasa dagowa tace ki saki ranki kinji . Aisha ta girgiza kai gabanta na faduwa. tace shi kije abunki. ta Mike tamkar kazar kwai ya fashewa a ciki ,. Tana fita mami ta sake yin murmushi tana kallonsa tace kai ai masu karamin ciki lallabasu akeyi wani cikin haka yake idan yana karami sai yatasa mace bacin rai, komai aka dan mata sai tasa kuka . Abdullah yayi murmushi kawai ina ganin yau ku kwana anan part dinka gobe ma idan zaka fita kabarsu dan naga tana sakewa a cikinsu teema . ya amsa kawai ya tashi ya fita mami ta bishi da ido tana murmushi uhmmmm wai Abdullanta ne ke shirin haihu ta hudu ,ta girgiza kai kawai yaran yanzu kennan. Gidansu ya koma ya kwaso abubuwansu masu mahimmanci ya dawo nan part dinsa har karfe goma bata zo ba yayi waya teema tace masa ta kwanta yace ta taso ta . Tashigo rungume da khalifa da teema ta rakota dashi . kallo daya yayi mata ya gane ta fara bacci . ya sake bata rai sosai wato ma ta manta dashi taje ta kwanta abunta . byn tasan shi ba zai iya bacci ba sai daita .. yazo ya zauna kawai akan gadon da take zaune " ya tsareta da idanunshi tsawo lokacin yana kallonta kafin daga baya ya kira sunanta kai tsaye Aisha ....ba ummu affan ba " me zan miki ki soni ne? Ta dago tsumammu idannuta tana kallonsa dasu shima ita yake kallo duba kigani ummu affan wai cikina kike son zubarwa ? Ta sake kalloshi ,ahankali tace ni bada wata manufa na fada hakan ba. ya kamo hannuta har bed room dinsa ya fiddo makullin wata karamar loka ta karfe . ya bude sannan ya fito da wasu takardu da file file daga ciki ya dinga zubawa a gabanta "yace duba ki Gani na mallaki abinda koni kaina basan adadinsu ba. a dalilin yaran nan su affan dady ya mallaka mana abubuwa masu tarin yawan gaske . Ko share dinsa na company da muka bude a Denmark gabadaya ya barwa khalifa . a yanzu kuma muna shiriye shiriyen bude wani company a England wanda kuma ana saran ni zan zama manager company. Muryasa raunane yace to Aisha idan ban tara ya'ya ba a yanzu me zanyi da duka wannan dukiyar ?wani abin ma ba zai lissafu ba . Amman duka ya'yanmu uku dake har kin fara gajiya dani "anyway nasan dama tun can nine bakya so shine ya kawo haka ". Amman babu komai ta sake kalleshi idanunta cike da kwalla ta rasa ya zatawa Abdullah ,. yasan sarai tana mutuwar son shi"yanzu Amman motsi kadan yace bata sonsa "kawai ta kallesa tace dan Allah kayi hakuri ni ba abinda nake nufi ba kennan". ni tausayin khalifa nake ji bai yi wani girma ba shiyasa na fadi haka Kawai yaji tausayinta ya mamaye zuciyarsa sosai ita Sam bata iya fada ba ya kawar da fuskarsa . ta sake cewa kayi hakuri dan Allah ban san hakan zai bata maka rai ba , . da ban fada ba Amman kayi hakuri . Kawai ta Mike taza koma wajen khalifa. da sauri ya rikota jin ya ta bata yasa takarasa rushewa" tashiga kuka Sosai. ita yaya za tayi da rayuwata ga khalifa bai yi wani wayo sosai ba,. ga ciki ga Abdullah shi kansa" . gashi tun jiya da yau Abdullah yana fushi daita sai fada yake mata daga Yar magana . ya juyo daita suna facing juna sannan ya rungumeta tsam tsam ajikinsa yadda take kukan ya dinga shiga jikinsa ,. ahankali yace kiyi hakuri banason Kukan . da kyar ya rararsheta tayi shr" . sannan ya sausauta mata rungumar yana kallonta yace kiyi hakuri nasan kema tun dazu ranki a bace yake" . kuma nasan daman saboda khalifa yasa kika fadi haka". to Amman ya zanyi maganar taki ce ba dadi a rai ". kuma na miki haka ne saboda wata rana kada kije ki zubar min da ciki bansani ba . Aisha ta hadiye wani abu da taji a tsaya mata a wuyanta tun safe ya sake rungumota sosai ajinsa . yana hura mata iskar bakinshi kiyi hakuri ,kin hakura tayi shr taki magana yayi murmushi ya sake matso daita jikinsa sosai. har suna jiyo bugun zuciyoyinsu ya hada goshinsa da nata yace kika sani ma ko Yar bby zaki haifa mana me kama dake . ta dan yi murmushi shima murmushi yayi Allah kinga sai ki haifa mana mai sunan mami dan naga mami murna take da cikin nan sosai. sai ki ta koya mata yanga irin

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46