Skip to content

Chapter 22

Chapter 22

Zuciyar Masoyi Book Two Complete Hausa Novels 1,169 words 0 views Progress saved
Download Book

kanta Aishar data zo daidai gurin da Abdullah yake a boye sai da taji jikinta yayi alamun wani abu dan itama hakance takasance daita . Amman bayanta kawai ta dan juya sannan sukayi gaba itada Aunty Maryam shi kuwa Dr sagir bayansa kawai ya juya musu . Ganin irin karbar da akayi musu yasa har suka baro gurin fuskarta a sake take Sosai . Har aunty Maryam tarinka tsokanarta tace A'a kaga masu cikin fari ana murna dan ance zaki haifi da Kato . Aisha tasa dariya tace kai aunty" har suka sake wuce wa su Abdullah na gun ya zubawa bayanta ido shigewar da tayi tana murmushi kawai Abdullah yaji gabadaya hankalinsa tashi . garama yabita koma me zai faru gara ya faru wato ita rashinsa bai dameta ba ta sake abunta tana walwala har ya fito zai rufa musu baya da sauri Dr sagir ya fizgo hannushi yaja shi ciki sosai yace haba friend ka natsu mana. zafa ka bata mana shiri idan ta ganka me yuwa baza kuma yarda ta dawo ba . Abdullah ya tsaya kawai yana kallon Dr sagir hade da sakin naunauyen hadiyar zuciya sanda salis yakaraso da sauri ya tsaya yana duban Abdullah hade jin wani irin tausayinsa . Agurguje ranar laraba aunty ta rakota " sai da ta bari ta tafi wajen awo sannan ta juya ta tafi gurin aikinta saboda aikin safe gareta. duk wani gwaje gwaje da akewa mai ciki sai da aka wa Aisha. sannan sis din tace ta dawo jibi da yamma ta karbi sakamakon da kuma ragowar magunguna a saboda jibi aiki yamma ne daita. Aisha tayi godiya sosai tana shirin sallama daita aka turo kiran sister din tayi shr zaune a gurin tana tunane tunanen dan sister din tace tadaka ne da tuni ta tafi . sister din ce ta sake shigowa tace kiyi hakuri fa na barki ke kadai Aisha ta mike tana ce mata ita zata tafi Amman sis din taki dole suka fito tare daidai lokacin shi kuma Abdullah yashigo asibiti shi da salis a bakar Jeep ya hangi zasu shiga mota itada sister kwata kwata yau aikin office ya hanashi ya dan fito gashi har zata tafi da sauri ya nemi Dr sagir a waya ya sanar dashi ta gama za'a kaita gida Dr sagir yace yayi hakuri shi dai kawai yakaraso office dinsa. Ranar jumma'a kuwa bata shigo asibiti ba sai byn uku saboda cunkoson abin hawa . ta gaban Abdullah ta wuce yana zaune cikin mota ya sauke glass din motar ita kadai ce tazo shigarta ta yau ta dada tayar masa da hankali tamkar tasan abinda zai kasance a yau. sai da ya tabbatar takarasa gurin sister sannan shi kuma ya juya motarsa ya fita zuwa gidansu wajen babanta tana isa wajen ta tambaye wata dan Allah sister zahra fa? . Wacce ta tambaya ta hada da wani ya nuna mata wani office tashiga ta tarar daita tana ganinta "ta fara dariya tace yanzu nake zancenki a Raina" ina tunanin zuwanki saboda nima bana son na wuce 4 anan " Aisha takarasa wajenta fuskarta dauke da murmushi suka gaisa sister zahra tasoma dan janta da hira kadan kadan kan zance haihuwa . sannan tace ina son dan kammala wani aiki ne sai mu tafi tare na biya gidan doctor na baki sauran magungunanki da result din ma yana can daga nan na sauke ki a gida . . Aisha tace ba komai illa ta kalli agogon lokacin sallah ma tayi ta fada a ranta . sannan ta dan kalli sister zahra tace mata ko zan iya yin sallah. sister tace har lokacin yayi nima banyi ba ko kibari muna zuwa can mukayi sallah sai mu fito dan yanzu toilet din ma sai an zagaya can baya Aisha ta amsa . Tana nan har takarasa aikin suka fito tare . A gidan Dr sagir suna shiga matarsa ce ta taresu a falo gidan. sister zahra ce ke tambayar ko doctor yana ciki ta amsa mata da yafita Amman duk inda yake yanzu yana kan hanya tunda yasan da zuwanku tunda har ya sanar min . Sister tanemi da suna son suyi sallah. ita sister din ce ta fara shiga tayi sannan da ta fito Aisha ta shiga ta lura da irin kallon da matar ke mata har jikinta ya dinga bata to ko ta taba saninta ne ? A daki tayi sallah dan sister zahra ta rigada tafito tana karasowa falo Dr sagir yayi mata magana suka fito waje har Abdullah Dr sagir yayi mata godiya sosai yace zata iya tafiya abunta tayi shr Amman sai satar kallon Abdullah take ta dai . ta amsa kawai har zatayi magana sai kuma ta fasa tayi murmushi tayi gaba. tare suka dawo falon da Abdullah Dr sagir ya kalleshi yace Abdullah me yanmmata kennan kai farin jinin naka akansu yakare ne Abdullah ya kalli Dr sagir yace dan malam ban son iskanci kabarni da rikicen dake gabana Dr sagir yayi murmushi yace a to ni ina ruwa ita fa wannan sister din kai take so . Abdullah yadan zungure shi yace hankali da bayanka dai Dr sagir yadan waiga kadan daidai lokacin da Aisha ke shigo falon ya juyo yace wuuuuuu... Ana kukan targade .... Abdullah yace kawai kana neman karasani. sukayi dariya a tare . tsoro frigice ne taji sun kamata alokaci guda sosai tasoma rikicewa har gabanta ya dinga faduwa saboda ganin su datayi tsaye suna dariya . Ahankali tace gaskiya sun shammace ta dayawa . duk a dabarbarce take Amman tayi yunkurin dakewa ta dan zauna a kujerar da tun zuwansu anan ta zauna tana dan dube dube. su dukkansu ,zama sukayi Abdullah ya zauna kujerar dake kallon nata ya zuba mata ido "kyan da ta kara ya wuce yadda ya dinga kiyastawa ,. komai ya canza a tare da ita har Yar kiba tayi me yiwuwa ko dan albarkar cikinsu ne yasa takara kyau . Aisha kuwa tarasa a wani hali take ciki abinda ya kara tsorata sai yanzu ta lura da hoton dake jikin bango da kyau Dr sagir ne da matarsa sai dansu dan kimanin shekara biyu alokaci ma yana gidan kakaninsa . Aisha ta dauke kanta karda dai rai na mata wayo za'a yi ta fada a ranta . Dr sagir ne ya fara magana bayan matarsa ta ajiye musu abinci da lemon" yace madam kinyi shiru friend fa ke yazo ya bawa hakuri kuma ayi sulhu da juna . Sai alokaci ta dan kalleshi Amman Sam taki amincewa idannuta ya hadu da na Abdullah tace da gaske ne dai abinda ta, zata. ta sake kallonsu a yadda suke bbu yadda za'a yi ta iya tsallakesu ta shige batare da Abdullah yayi wani abu ba. ita ko da matar Dr sagir za'a barta tasan baza ta koina ba. kawai kallon Dr sagir take yana ta magana a ranta tace idan ba zasu barta ta tafi ba kuwa sai dai tayi ta zama anan Abdullah kuwa ko daga hannunsa baya iyayi. duk wani halin da tashiga a yanzu yariga ya gane shi. yana ji tamkar ya karasa ya tausasa mata halin da tashiga da kansa. Dr sagir ya lura dashi sai ya dan share sannan ya

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46