Skip to content

Chapter 15

Chapter 15

Zuciyar Masoyi Book Two Complete Hausa Novels 1,166 words 0 views Progress saved
Download Book

sauka ta fara raba goro sannan taje Kano kwananta daya ta dawo. tasa mami ta aika da duk wasu kayan aure can sokoto haka kuwa akayi hatta makota sai da mama tasa akayi musu fenti . saboda yan daurin auren idan an zo aga layin da gaske . takama iri iri take diyarta zata aure mai kudin wuce sa'a. tace wanda duk taga dama shi za ta taka. ta kwana lfy saboda naira ta zauna alokaci kuma da gaske ta zauna din Faiza ta dawo kasar Amman sai da sukayi sati biyar da kwanaki ai kuwa tasha tsinuwa da zagi iri iri agun mama hafsa. dan ko goro ma da aka rarrabawa mutane . Sai da aka tambayar faiza . Ita ko aka dinga cewar amarya ana can kasar waje yo siyayya aure. Faiza ta kara sati uku akan yadda sukayi da mama hafsa saboda tana son a gyara mata jiki. dan haka hatta inji daye fata da gyaran jiki sai da tashiga. kuma kai tsaye gidan mami ta zarce da suka dawo batayo sokoto ba. a saboda bata son mama hafsa ta dibar mata wasu kaya data siyo. ko tace a bawa ragowar kanneta. Gidan mami gabadaya ya rikice a lokacin . takai ta kawo ko kwana Abdullah baya yi a gidan saboda mami ta karbi Key part dinsa. wai nan faiza zata zauna daman kuma akwai extra rooms wanda dady yasa aka Gina tun aurensa na farko . duk sukayi parking din wasu kaya gefe aka shiga shiryawa faiza dakinta .. dan haka shi kansa Abdullah ya tattara abubuwansa masu mahimmanci ya kulle bed room dinsa. ya koma kwana a wani part din. Dan bai iya zuwa gidansu na aurensa da Aisha . saboda shigarsa yafi komai tuna masa da ita. da komai nata dan hatta kayan data sa a ranar da zasu rabu suna a gefe gado cikin basket ya gansu. ranar da yaje gidan kwaso wasu mahimman files hatta kayan da tayowa yan'uwanta tsaraba suna cikin akwatina duk suna nan yadda suke. ranar daya shiga kasa fitowa lfy yayi dan har zazzabi yaji a jikinsa kafin ya baro gidan . Iyakar rikicewa kuwa gidan alhj ishaq yayi. dan hatta masu gadin gidan sun fahimci haka kowa surutun yake. ita dai mami sai abinda aka tsara shi takeyi . Shi kuwa uban gayya duk abinda mami tace shi zai yi to haka yakeyi. minal kuwa duk fushi take da kowa a gidan atun rabuwar Aisha da dan'uwanta . hatta mami bata kulata sosai sai ya zama dole sai ta yini a part dinsu bata sauko ba sai idan mami ta aika tazo idan tazo ma bbu wani sakin fuska dan ko gaida mm hafsa batayi . Teema kuwa da ita tafi kowa sanin halin mami ita ke jin jiki sosai dan ganin yadda mami ta koma yanzu yasa kullum sai tayi kuka a daki . tana lura daita da duk yanayin da take ciki yanzu babban abinda yafi frigitata mami sai tayi fiyye da kwana uku batayi sallah ba . wannan abu shi yafi komai tada mata hankali dan haka kullum sai tayi ta yiwa mami addu'a Allah ya dawo daita daidai . Dan haka ya zama hatta ma'aikatan gida idan kaga an dan taru to kus kus din abinda ke faruwa a gidan sukeyi Akasa bikin faiza sati biyu masu zuwa haka Abdullah ya shedawa dady ta waya . dady yace bbu komai shi dai yayi ta addu'a Allah yasa hakan yazama alkhari . Kwana biyar ya rage daurin auren Abdullah ya shiga part din mami ya danka mata files din gidajen da motoci kmr yadda tace masa ta karba ta Gani. sannan ta mikawa mama hafsa domin a ranar ta doka samako tun safe a gidan. a dalilin faiza taje sokoto jiya ayayinda Mama hafsa bata nan yasa ta kwaso akwatinan lefe ta kawo part dinta Abdullah inda zata zauna ta kulle. tun ajiya mama hafsa ke bala'i bbu abinda Faiza ta bari ko irin dan mai da zasu rabawa mutane. bare dan abunda ake cirewa na uwa. mirsisi faiza tayi tace komai na kasar waje ne ba irin na rabo bane zata siya na rabon a bawa mutane . To mm hafsa ta nike file din gidaje shida cif da motoci shida sai ta kuma ta canza shawara, dan wani tunani ne yazo mata hakan yana nufin Abdullah baza shi daurin auren ba kennan. gashi tayi niyar ana gama daurin auren zata sa'a kirawoshi idan ya shigo . da akwai wani turare da boka yabata yace ta turarawa Abdullah daya shaki hayakin take zai ji komai ya canza masa hatta uwar da ta haifi shi bai kuma ganin darajata kmr ita .. shiyasa Ita kadai tasan da wannan dan ko faizar bata bari tasani ba. dan haka sai tasa mami ta sake kiransa a waya ya shigo ta Mika masa files din cewa ya ajiye a gunsa ranar daurin auren ya taho dasu. bbu yadda zai yi dole tasa ya karba dan shima har cikin zuciyarsa bai yi niyyar zuwa daurin auren ba . shi yasa yayi hakan yadda yayi mama hafsa Ta kara gane dabarar ta tayi daidai . dan abunda ta zarga haka ne. bashi da niyar zuwa da kuwa ya cuceta yasata asara mai tarin yawa . dan bazan yaro mai dan karan daurin kai wannan har ya zarce uban nasa ta fadi haka akasan ranta . MMN SUDAIS CE [3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’— ZUCIYAR MASOYI πŸ’–πŸ’–πŸ’– πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’— AISHA A BAGUDO Nagode da yadda kuke matukar sona da kaunar novel din nan ,Kuma kuna Raina domin kuwa KAUNACE SILA komai dan kuna cikin kololuwar zuciyar Bagudo. kuna ina πŸ—£πŸ—£πŸ—£πŸ—£πŸ—£yan ZUCIYAR MASOYI FANS ku matso kusa this page belongs to you ol na bakushi free of charge kuyi duk yadda kuke so dashi. na kune, haka ma Bagudo takuce har abada ana mugun tare irin sosai din nan 🀝🀝🀝🀝🀝🀝🀝🀝 Page 61-62 Abdullah yayi shr ya jima zaune a bedroom dinsa ya gane mama hafsa duk yadda yaso ya kauce mata sai ta kure shi. ta wani koma kmr itace ta haife shi . ya rasa yadda zaiyi da rayuwarsa Amman nasan yadda zan bullo musu ya fada aransa. ga dukkanin alamun rashin Aisha yana nema ya zama gaske . shi Kuma ya rike alkwarin byn Aisha bbu wata ya maccen da yake ganin zai kuma kusanta . dan haka ya gano wata tafiya a gabansa a tun safe . ya samu sako ajikin system dinsa cewar company da suke son budewa a South Korea wanda har suka kirasu interview kwanakin baya Denmark. suna bukatar wani wakili daya wanda zai je ya zauna a can har tsawon watanni bakwai zuwa tara ko shekara har sai komai akammala . Dan haka bbu wani bata lokacin ko jin wani abu kawai Abdullah ya wakilta kansa . dan haka ya tura sunansa da komai nasa akan shi zai yi tafiyar . byn dawowar dady kennan" a yadda yake ganin al'amarin sai wani ikon Allah yasake rayuwa da Aisha. jikinsa har ya fara hakura da rashin ta. dan haka ko anyi aurensa da faiza bazai bari su san da zancen tafiyar ba sai dai su shafa Suji shr . kuma muddin yashi tafiya . Ko

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46