Skip to content

Chapter 27

Chapter 27

Zuciyar Masoyi Book Two Complete Hausa Novels 1,173 words 0 views Progress saved
Download Book

sama sama numfashinta yake saboda tsabar tsoro da take ji a yadda taji tana tambayar ta tace ai...sha... daga can bangaren mami ta maimaita sunan tace daman dake ya tafi . abinda Aisha taji alokacin hatta abinda ke cikinta sai da ya motsa dif taji an kashe wayar hade jan tsaki mai tsawo. taji jikinta ya dau zafi da maganar karshe da mami tayi "ahankali ta ajiye wayar har yanzu kirjinta yana bugawa da sauri "cikinta na juyi tamkar ana yamutsa bbyn ciki. Ahankali ta mike da kyar ta shiga dayan dakin dake nan falo ta kwanta tana jan numfashi sama sama abinka game tsohon ciki . koda Abdullah ya fito wanka yana goge kansa da karamin towel bai ganta ba ahankali ya tsaya yana kalle kalle daga can ya kwala mata kira ya nufi inda ya jiyo ta dan amsa masa da kyar. yana tura kofar ya ganta kwance tayi lamo akan gado . ya sauke numfashi ya karasa ya zauna kusa daita sannan ya lalubo tafin hannuta yace ya kika zo nan kika kwanta da kyar tace nan yafi min kusa. kuma bacci nake ji ya kwaikayi yadda tayi magana yana shafota. ta rufe idanunta batace komai ba yace ko nazo muyi baccin tare. ta girgiza kai so nake na dan huta yayi murmushi yace ba kya son nazo na dameki na gane ai ya sake yin murmushi ya mike idan kin tashi ina falo ya sumbaci lip's dinta yayi waje . Fitarsa tayi tamkar wacce aka kara mata wani abu akan yadda take ji' har kusan awa guda tana nan kwance ciwo take ji a kasan mararta sosai kmr zata mutu "can ta mike da sauri ta shige toilet din dake manne a cikin "dakin tana shiga ta duba ba sai taga jini ke biyo kafarta ba. gabanta ya sake wani irin faduwa akan na da yaushe rabon da taga hakan tun suna American sau biyu Abdullah yana shigowa tana ban daki data ji ciwon ya fara damunta kawai sai tasa kuka" tana nan ciki bathroom taki fitowa har Abdullah ya hau buga kofar da karfi sannan ta rarrafa ta bude yana ganinta haka ya shiga tambayar ta a rikice ta nuna masa kafarta ya kalla ganin jini da yayi ya kara tayar masa da hankali . a gigice ya kamota yana kara dubawa yace kinga ni ko Aisha kinga ni ko shiyasa nace muje asibiti duk yabi ya agigice gashi nan kina shirin jamin asara saboda bakya sona Amman ba komai " da sauri ya gyara mata jiki shima jikinsa na rawa ya sa kaya ya fita daita . Allah sarki ciwo kmr jira yake akai inda magani yake "cikin lokacin kadan Aisha ta fara fita haiyacinta.. gashi babban abinda ya hana ma a rufu sosai akanta "saboda basu da kati ma kwata kwata wanda ta taba zuwa ma a Nigeria duk har shi ya hadawa dady da takardun . cikin ikon Allah har wayewar garin asuba Aisha bbu wani sauki sai na ubangiji . Allah ya taimaka saboda matsayin aikin daya kawo Abdullah din aka basu card din ganin likita Aisha na kwance da kyar take magana Abdullah dake kusa daita hannushi makale da nata ya sake matsowa daf daita "ahankali take sake magana "da kyar ya gane abinda take fada' Amman yaki kulata. Dan tun safiyar ranar ta dame shi da maganar ita dai a maidaita gida taga iyayenta" kada ta mutu ko Kuma ya kawo mata su ta gansu" kar ta tafi bata gansu ba" maganar tana neman takarasa kasheshi . dan sau biyu da suka yi waya da dady yagaya masa halin da ake ciki da abinda take cewa sai gashi dady ya sake bugowa . yace gara yasa akawo mata iyayenta dan idan bata gansu ba wani abu ya faru daita daga baya sai yaji ba dadi . To har dare lahadi magana ma sai ta gagari Aisha" sai idanuwa datake wulwullawa. Abdullah ma ya kasa tsaye ya kasa zaune ballanantana magana . sai dai kallon kallo ciwon a duka jikinsu su biyu yake "abinda doctor ya gaya masa da suka isa office cewar Aisha ta Sami wata razana ce ko wani abin tsoro da ya frigitata. ko ta dauki wani abu mai nauyi wanda hakan yasa shi kansa abinda ke cikin ya juye zaune.. shi ke tokare mata numfashi Amman suna kokarin ganin ya koma yadda yake . Da yammacin ranar abun ya bawa Abdullah tsoro sosai jikinsa ya dinga rawa ganin Aisha numfashi ma sai da aka sa mata oxygen saboda kan yaron ya sake yowa saman kirjinta" yana yiwa dady waya Amman shima kirjinsa ya rike gam. dole ya amince dady ya sakowa Aisha iyayenta a jirgi ta gansu "yayi addu'a har bai san irin wacce yake kamawa ba Allah shi ya bashi Aisha kuma yana tare dashi . idan ya dauketa ba yadda zaiyi wanda a lokacin ko shi kansa Aisha bata ganewa . doctor yace dole a cire abinda ke cikin tunda ta riga ta galabaita. ko "dan " ya koma yadda yake ma bazata iya haihuwa da kanta ba . Tunda Abdullah yaji iya nan bai kuma gane abinda doctor yake cewa ba, ya dai zubawa bakinsa ido yaga yana ta motsi har sanda yata bashi yace be a patient .. please. Abdullah ya dan girgiza masa kai sannan da kyar yace to doctor ai cikin bai isa haihuwa ba. doctor yace eh dama koda ya rayu sai dai yazo a bakwaini da kyar dasa bakin babban ogansu Abdullah sannan yasa hannu akan za'a yi aikin. dan gabadaya yagama fita haiyacinsa sai zare idanu yake Amman bakinsa bai bar ambaton sunan Allah ba . Yana kallo aka shiga daita dakin yin operation ko a samu ko a rasa . One hour batayi ba aka fitar mata da identical twince din ta masu matukar kama da juna . komai nasu iri daya hatta mahaifa guda daya ce shiyasa ba fahimci biyu ne a cikin ba . Sun sha wahala kmr mamansu dan daya ya zaune kan daya sai a sannan Abdullah ya dan samu kwarin jiki yana tambayar uwar dan shi ta matarsa yake yasan ko ya rasa bby "muddin suna tare zata sake haifo masa wasu. idan kuma ya rasata wa zai kama. doctor yace ana sa ran farfadowarta itama .. dan har lokacin batasan inda rayuwarta take ba .. MMN SUDAIS CE [3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗 *ZUCIYAR* *MASOYI* 💖💖💖 💗💗💗💗💗 *AISHA* *A* *BAGUDO* Page. 70 A take tashin hankalin wancan lokacin shi ya dawo mata a yanzu. ya juyo daita suna kallon juna yadda ta ganshi taji bazata iya tafiya ta barshi, jikinsa a matse yake sosai, idanunshi gabadaya sun canza kala sun gama kankancewa da kyar yake iya budesu. ta rufe idanunta ahankali ta koma ta zauna . Abdullah ya janyota gabadaya ta fado jikinsa cikin zafi zafi yasoma romancing din da jikinta bakinsa yake kokarin kaiwa cikin kunenta ta kamewa tasoma mutsu mutsun kwace kunneta dan tasan abinda yake shirin yi.. matseta yayi sosai ya zura harshensa ciki kunneta yana tsotsa cikin iyawa da kwarewa take taji tsigar jikinta gabadaya sun mike yrrrrrrrrrrrrr . jikinta ya dauki rawa ahankali yake mata rada acikin kunneta. kin amince min Aisha wlh a

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46