Skip to content

Chapter 10

Chapter 10

Zuciyar Masoyi Book Two Complete Hausa Novels 1,151 words 0 views Progress saved
Download Book

Amman yau an wayi gari saboda wasu can masu kama kaman dagin ta raba danta da abinda ya kwalafawa rai . ta batar masa da duk wata walwalarsa yake fada a ransa. ba Abdullah din kadai ba hatta shi kansa abin kullum dashi yake kwana a ranshi . gashi koda acikin hira taki yi masa zance idan sunyi waya . shima Kuma ya dau alkawari ba zai fara sanar mata yasan da maganar ba. Har ya kwashi mintina talatin da rabuwa da dady a waya. Amman bai san cikakken tunanin da yake yi ba. abubuwa uku sun taro sun cakude masa cikin kwakwaluwarsa. Kuma duka atare suke tafiya ko wanne yana bukatar ayi solving dinsa. Aisharsa auren faiza matsalar ma'aikata. ya rike kansa da karfi dan kada ya tarwatse. da kyar ya iya tuna dady yace ya dinga ya waita addu'a idan irin haka takasance dashi . addu'ar yayi tayi har ya kara da sallah raka'a biyu a haka ya samu sausauci a zuciyarsa . ko abincin daren ranar bai ci ba. domin shi kansa abinci ma ba kalar raayinsa bane . dan a Yan kwanakin mami gabadaya ta fita batun tattalinsa da abinda zai ci rawar jikinta akan faiza da mama hafsa kawai yakare . Ko a washegari daya shiga gaisheta kafin fitar sa office . karara mami ta nuna masa ita fa yanzu so take ya dauki duk abinda mama hafsa take bukata da mahimmanci tamkar ibadarsa data zame mata dole. ya kalli mami kmr ya zubda kwalla dan takaici abinda tace. Amman sai yace bbu komai duk yadda kike so haka za'ayi . a hakan ya baro part dinta daidai zai fita falon ne suka kusan cin karo da faiza da sauri ya tunkudeta tun kafin takai ga jikinsa. tayi taga taga zata fadi sannan ta rike bango ganin zai bar wajen ne yasa tayi saurin Sha gabansa ta tare shi wai tana son magana dashi kallon da yayi mata . sai da taji shi har cikin hantarta . nan tabi shi da ido har suka fice shi da salis . Abdullah ya zagayowa mutanen su ta bayan gida ya kamo su ta inda baza suyi tsammaninsa ba. mutun shida dama ake zargi sai gashi an kuma samu n mutun biyu a kasa. takwas kennan abin mamaki sosai ragowar biyun din duk abokan dady ne na kud kud wanda yake ji dasu . ragowar Kuma manya ma'aikatan company ne . Bai tsaya ji komai ba yasa aka kame su aka kullesu har da abokan dady . Kuma fur yaki yarda da duk wani ban hakurin da'ake bashi . da'aka dame sa da magana ma yasa aka buga kara kotu . To can ne ma ya kori ma'aikatan na har abada.. Sannan yabi didigi kowacce kadara dake garesu anan cikin company . a karshe dama yasan ba komai ne zai dawo ba. Amman cikin dari an samu kusan kashi tamanin da wani abu . Teema ce tayi nouking kofar part din Abdullah ya bude . tashigo da jug a hannuta ta same waje ta zauna sannan ta tsiyaya masa fresh miki ta bashi ya karba. ita kanta teema yaga duk ta canza masa komai cikin tsanyi jiki take yinsa . sai daya shanye . sannan tace bros dama naxo ince maka ni zan rika kawo maka abinci da zaka ci. da kaina zan dinga girka maka ina kawo maka saboda a gaskiya ban yarda da zaman su mama hafsa da faiza acikin gidan ba . dan akwai wasu abubuwa da nake ganewa idanuna . gashi Sam mami mai da hankali balle ta taka musu birki. Abdullah bai ce komai ba sai dai ya amsa mata da kai. itama tana gama fadar haka ta Mike har ta kusan kaiwa kofa sai Kuma ta juyo tace bros duk wanda zai kawo maka wani abinci byn ni ka barshi kawai . ta juya shi daman baya iya cin duk abinci da,ake kawo masa . saboda ba irin test din da yake so bane. kwata kwata sai dai masu gyaran wajen su fita dashi . Ya kalli agogo tara ta dade da wucewa yayi murmushin gefen baki Aisha tasan lokacin da yake bukatar fresh milk a dan zaman da suka yi tare. bata taba bata lokacin bare ta manta. a yanzu kuwa tunda maminsa ke shareshi wata rana salis ke siyo masa a waje ya Sha ya ci takeway ya kwanta . Yayi shiru yana tuna yau kusan kwana talatin da shida da tafiyar dady iya kwanakin rabuwarsu da matarsa kennan . ya Mike jiki a sanyaye ya shige ciki ya kwanta akan royal bed dinshi. ji yayi gabadaya kwanakin ma kmr bayin su akeyi ba . ya fada aransa a kalla yanzu za'a kuma ninka kwanakin sau biyu kafin yaji wani bayani daga gareta. gashi su mami tamkar zasu sa ya gudu daga garin haka yake ji kansa. Akan maganar auren faiza shi kam yace dasu suyi komai ba sai an nemeshi ba. tunda da auren suke so ayi . Amman shi kansa yasan yanzu ba wani auren da zai dauke shi da daraja byn na Aisha sanda ya aure ta bata son shi ,shi kansa ya san da haka . bata damu dashi kuma ba bata son wani abu nasa ba, Amman dan zaman da sukayi suka tare shiga ran juna ko bacci bata iyayi sai dashi. nan take jikinsa ya sauya yarikece ita kawai yake kishirwa a halin yanzu, . Gabadaya idanunshi sun gama canza kala sunyi jawur . ya jawo pillow ya kankame ajikinsa yana shafa ahankali Amman bai daina jinta a sansar jikinsa ba . barin da ya tuna yadda ta ringa rikita shi adaren da zasu rabu , Ko tasan zasu rabu ne yasa ta rinka masa abubuwa masu cracking brain . ya Mike tsam ya shige bathroom . ya sakarwa kansa ruwa ya dade tsaye ruwa na zuba kansa . sannan ya fito Amman yana sake kwanciya sake jin ta biyosa ta manne akirjinsa ,. Jikinsa ya dauki rawa ya runtse idanunshi ya kankame jikinsa waje daya yana surutai iri iri . adaren dai yayi wanka ya kai sau goma . dan ya samu saukin sha'awarta har aka fara kiraye kirayen sallah bai runtsa ba haka yakaraci haukansa shi kadai a adakin. har sanda aka kira assalatu ya kara tabbatarwa kansa lallai so bala'in ne . bai gane hakan ba a tun farko sai a yanzu Basu da lecture yau Amman tun jiya da babanta ya sanar daita zance Aisha take tunanin can zata wuni. dan haka tayi shirinta tamkar wacce zata je makaranta ta fice Abba ya gaya mata zance ne domin ko su mamanta bai bari sun sani ba . Tana shiga gidan daita ta fara cin karo . ta fito daga bandaki da buta . suka sawa juna dariya Aisha har da dan kwallarta na murna .. Sakina taja hannuta zasu shiga rufar inna . Aisha tace shiga inna tana ciki ku gaisa tukun . ni ina nan tana fitowa suka shige tsohon dakinta dake kusa da na inna wanda byn barinta gidan ya zama na usman. Amman a yanzu ma duk da kayansa yana ciki anan din take kwana . Sakina ta dubeta da kyau cikin sanyi jiki tace sister ya

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46