Chapter 5
Chapter 5
kodan kyansa kadai zan'iya aure shi , gashi namijin duniya tana magana tana girgiza jiki . Ke matsa can wawiya banza ana maganar masu nauyi kina magana wani kyau. ai idan bbu kudi ai ko shi kansa kyan baya wani tasiri ,. faiza tace ai wlh dan dare yayi ne da yanzu zan tafi tunda kince ( boka dan ina da Kare) yace wuyarta a raba su ,idan aka rabasu komai zai daidaita . Mama hafsa Tace haka yace Kuma bakisani ba har uwar ma a yadda ta nuna min sai yadda nace . , dan haka banason abin yawuce wata daya ke Kuma kina shiga sai ki san yadda zaki mallaki dukiyar kinsa gidajen wannan ubanku nasa a market na siyar . kinga sai amaida masa batare da ya ankare ba . sannan takara rage sauti sosai tace duk cikinku kece nake ganin zaki biyo ni, kinsa Allah banki ace wannan kanjamammen uban naku ya mutu ba nima in koma in aure uban Abdullah. tunda an yarda da halacci haka ,faiza tace kai mama babanmu Kuma tace shifa. to meyake tsinana muku ,shege mutun sai dan banzan son abin duniya tsiya. mai kan goruba kawai faiza ta saki wata uwar dariya har da rike ciki ,. mama hafsa tace ai wallahi bari kiga mugama da naki . ko yaya naga waje fadawa zanyi mutaru ayi ta damawa damu. faiza sake kecewa da wata dariyar tace kinga munkasa mun tsare kennan mun hana gaba mun hana baya komai yadawo hannunmu tabawa uwar hannu duka tafa .. . Mama hafsa Tace uhmmmm ana magana ma shiyasa nake sonki dan nasan duk abinda na tsara bakya kii.. sai dai kinsan Allah ina tsoron alhj ishaq har cikin Raina. faiza tace dady ko tace shifa ,kina ganin ko irin dan wasan nan na dagin mata bai so. bayan gaisawa ba yarda wani abu ya gilma. Amman nasan ta yadda zanyi ai duk wani taurinkai akwai maganinsa . Faiza ta Mike tace bari kiga mama naje nasoma shirina tun yanzu kinsa da zazafi ake buga karfe . mama hafsa tayi murmushi tabi diyartata da kallo tana rayawa a ranta ai ba zaki sha dadin ke kadai ba. har dani za'a. yadda nayi sintiri a gidajen bokaye da makabartu ne zan zauna sai kin mikomin ahankali ta Mike itama . Duniya gabadaya ta cukede ta tsayawa Abdullah waje daya ,. yarasa wacce irin rayuwa mahaifinsa take son yayi byn taraba shi da tsanyin idanunshi . Tun yana kuka da idonshi har yadawo yin kukan zuci .. Gabadaya wayoyinsa ma a kulle suke komai ya tsaya cak rabonsa da zuwa office tun ranar da dady yabar kasar. ya gwammaci yacigaba da zama a mataccensa har ran da za'a kaishi kabari da dai ya fida koina , kwanansa uku duk wata al'ada ta rayuwarsa ya barta inka dauke sallah . Ko magana bayason yi idan mami ta turo yazo haka zai zauna a gabanta bai fahimtar komai, ko fada take har tagama bai jin abinda tace ,. shi a lokacin ko mami yankashi zatayi bazai damu ba . Dr sagir ne yake buga kofar part din Abdullah da karfi gaske, yana kiran sunanshi Abdullah Abdullah jin muryarce yasa Abdullah ya zubawa kofar ido yana jin Yadda kirjin ke radadi da ciwo mara misaltuwa. jin an cigaba da bugun kofar ne yasa ya Mike da kyar ya bude yana budewa yayo gaba abinsa. Dr sagir yashigo yana furta kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun..ganin yanayin abokin nasa .. friend meyye haka kana da lfy kuwa five days kana cikin daki a kulle. ko ma'aikatanka , ka hana su , shigowa su gyara maka guri, Abdullah dubi yadda kadawo ya zauna agabansa yana nuna shi da yatsa . salis ma yace ko shi kaki yarda ka Gani why.. Abdullah yayi kwanciyarsa akan kujera bai ce komai ba domin zuciyarsa ke wani dokawa yasa hannunsa duka ya dafe kirjinsa dashi . cikin mamaki Dr sagir yake kara kallon koina sannan yace ina matar gidan take. ina Aisha nace, sunanta dayaji ne yasa ya dan ya kalleshi ,Dr sagir ya sake maimaitawa Abdullah tambayar , Abdullah ya dubishi yace na saketa da sauri Dr sagir yace what . Abdullah ya amsa da kansa alamun haka ne. why ar you talking rubbish Dr sagir ya fada a fusace ,. Abdullah ya dan yi murmushin takaici ya sake kollonshi , Dr sagir ya sake dafashi cikin sanyi murya yace my friend meyake damunka ne na nemi wayar ka bansamu ba ,na dauka ko baka kasar ne jiya naje office ance baka zuwa, . anjima zan wuce sokoto shine nabiyo nayi checking din ka . ance baka ganin kowa salis nasamu sannan nashigo friend meyasa Meka haka kasan abunda kafada min kuwa. Abdullah ya dan Mike zaune ya kalleshi ido jajur murya a raunane yace Dr sagir lafiya ta kalau . da gaske na rubu da mamata, mami ce ta zabi haka ,dan haka na saketa. Dr tunda na auri Aisha duk abinda zai sani farinciki shi take min to yanzu bata nan mun rabu me zai sani farinciki kuma ? kawai ya koma ya kwanta yana sakin numfashi sama sama tamkar mai cutar asma. ya rufe idanunshi gam yana tuno Aisharsa bai sake yin magana ba sai wasu zafafan hawaye dake gefen idanunshi can kuma jikinsa ya dauki kirma ya kamo lip's dinshi gabadaya ya tura abaki ya datse da hakoranshi wannan lokacin yazo masa da abubuwa munana masu wuyar mantawa ko awani hali Aisharsa take ..a kasan rashi yace killama tana can cikin jin dadinta tunda daman ba sonshi take ba shi kadai yake shan wahala akanta mamina maye yasa ...meyasa kikawa Abdullanki haka baki san bazan iya rayuwa ba muddin kika rabani da ruhina ,. Aisha zuciyata ita bugun zuciyata sosai jikinsa ke rawa yayinda idanunshi ke runtse ahankali fizgo numfashi yana sake dafe zuciyar..... MMN SUDAIS CE [3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗 ZUCIYAR MASOYI 💖💖💖 💗💗💗💗💗 AISHA A BAGUDO Page 47-48 Dr sagir ya zuba masa ido watau har yanzu dai rikicin mami na nan kennan na rashin son auren Abdullah da Aisha. a ganinsa zuwa yanzu ya dace ace mami ta barwa Allah komai . ya jima, yana jinjina al'amarin sannan ya numfasa yace Abdullah a hanya nake yanzu. bbu wani hanzari da zan iya Amman karaba kanka da wannan kadaicin . ,kada ka mutu a cikin daki kai kadai. Ganin yadda jikin Abdullah har yanzu rawa yake kmr mazari yasa Dr sagir yin hanzarin Mikewa ya ja hannunsa zuwa bedroom ya kwantar dashi kan gado sannan ya dubo wayoyinsa duka ya kunnansu da duk wata na'urar dake dakin. sannan ya koma waje yayi kiran salis yace a shigo a gyra koina. ya koma kusa da Abdullah wanda yake kwance yana numfashi ahankali, yace da sati guda zanyi a sokoto Amman ya zama dole na rage kwanakin su koma hudu zuwa biyar saboda yadda na sameka Amman dan Allah ka tashi yanzu kayi duk abinda kasaba Aisha...sai kuma yayi shr yakasa magana ya dan dafe kai shi yarasa ma wani abu zaiyi akan lamarin ,ya girgiza kai yana duban agogonsa yace dole ne in dawo da wuri saboda kai Amman zan neme ka dana isa. Abdullah ya dan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46