Chapter 43
Chapter 43
hakuri na taba ce miki akwai soyayyar wani namiji daban a Raina Byn mijin dana aura. to sister ba kowa bane wannan mutun face mijinki Abdullah uban ya'yanki bbu yadda,zanyi da zuciyarta dana hanata son Abdullah, a tun farkon ganina dashi. Yayinda shi alokaci a makance yake akan kaunarki baya ganin kowa sai ke .. Nace miki wanda nake so sunan sa Muhammad ba karya na gaya miki sai dan sanin dana yi Abdullah ishaq Muhammad ne cikakken sunansa . sister Ba yadda zanyi da son mijinki dan yaci karfin jikina . har su mama suna ganin ko wani abu ne a kaina. ganin duk kannena anyi musu aure ni kuwa mazan ma korarsu nake yi .Amman ni kadai nasan abinda ke damuna nakan hargetse a duk lokacin dana ganshi shine dalilin dayasa ko ranar da za'a kaiki gidansa na gudu dan bazan iya bude idanuna na ganshi na baro ku tare ba shi . yasa washegari ma na tattara na bar garin gabadaya . dan nasan zaki nemeni. ba yadda zanyi Abdullah dake yafi yadacewa bani ba , . tsakanina dake son Allah mukewa juna shi yasa na hakura da sonsa a Raina har gashi ina bayyana miki a wasika ta dan me yiwa baza mu kuma ganawa ba kiyi hakuri kiyi hakuri zan tafi da kaunar mijinki a Raina wanda bbu wanda yasan da haka . na tsorata matuka da lafazinki akan mijinki ran nan da kika zo lokacin bikina. nasan kema kina sonsa sosai yanzu. ga hotunansa nan. dana karba agun abokinsa tun lokacin bikinku . faruk ya taba Gani sau daya har kumayi rikici Sosai dashi daga baya ya gane mijin kawata ne . nagode sosai sister da kaunar da muka nunawa juna . Taki a koda yaushe sakina aminu. Ita kanta takardar sai da ta jike saboda ruwan hawaye, kuka Sosai Aisha takeyi ta zube a gurin tace ki dawo sister dan Allah ki auri Abdullah na yardar miki dama tun muna school komai namu daya ne . ki dawo mu auri miji daya meyasa baki fada min ba sai da kika tafi . Tanan dukurshe rike da takardar taci kuka idanunta sukayi luhu luhu suka yi jawur dasu. Abdullah yashigo gurin a tsorace tunda ya shigo bai ji motsin taba ahankalinsa yake atashe. a firgice yakaraso inda take fuskarsa cike da tsoro da mamaki ya tsugunna gabanta. yana tmyrta ta Mika masa takardar tana kallon yanayinsa. yana gama karantawa ya runtse idanunsa sannan ya numfasa yace kiyi hakuri Allah yajikan sakina . Ta kalleshi fuskarta a tuhume dashi tace Abdullah kasan sister na sonka dama ? ya zuba mata rikitattun idanunshi sannan yace nima bansani ba. kuma lokacin da yawa bazan iya tunowa ba. ni bamma fahimta ba Amman kiyi hakuri kiyi mata addu'a Allah ya hadata da wanda yafini a aljanna. Ya riko tafin hannuta cikin nasa yana murzawa kada kisa damuwa a ranki kiyi ta mata addu'a nima zan dinga tayaki . batace komai ba banda hawaye dake silalowa akan fuskarta yasa hannuwansa duka ya tallabo fuskarta yasa harshensa yana salar hawayen dake silalowa akan fuskarta. ya danyi murmushi yana kallon kwayar idanunta . yace kinga wannan me sunan dady irin halin dadi sak yake saki tun yanzu na fahimci shine koda yaushe cikin walwala kike Amman muddin kika sa damuwa aranki yanzu nan zaki daina yasa hannu yana shafo cikinta yace tashi muje yau duk bamu gaisa da bbyna ba. yana kara kunnenshi a tsaitin cikin. Ta dan tureshi zata Mike ya dinga mata dariya yace hakuri zakiyi kowa da irinn tasa jarabawar. yanzu na dada sanin cewa ni Kuma sai ta Allah akan sonki. Amman ina godiya da yasa ke din kika zamo matata . Duk yadda taso ta manta da mutuwar sakina abun ya cutura ta dinga tuna rayuwarsu a boarding sai ta tuna yadda sakina ke yawan zuzuta kyan Abdullah ,ta tuna yadda take mutuwar sonsu affan da nuna musu kulawa sosai da sosai waton saboda sun yo kama da Abdullah kwabo da kwabo ne . Wannan haihuwar anyi abinda baa tabayi ba saboda bby mace ta haifa . party kala kala sai ga innarta har kasar da take aure Abdullah yasa aka dauko mata ita har da aunty Maryam. karo na farko da inna ta taba ganin inda diyarta take zaune ga ya'yanta abin sha'awa khalifa ne kawai bashi da hasken sauran yaran. Amman duk kamaninsu daya sai a lokacin Abdullah ya kara Gane tsantsar kamamani dadinsa da inna kamarsu daya da kuma matarsa bambancin kadan ne taso Abdullah yasa mata sunan sakina sai dai kafin tayi wani hanzari taga har yayi mata huduba da sunan mami wato (hajarul aswad) aka dinga kiranta da aswad a daren ranar inna har hawayen farinciki tayi . ganin inda diyarta take rayuwa . gashi mijinta yana kaunarta fiye da yadda take tsammani . aswad tayo uwarta sak sai dai ita tafi mamanta haske sosai Abdullah yana mutuwar son yarinyar tamkar bai taba haihuwa ba sai akanta. sai ya lalace a gurinta ya bata lokacin mai tsawo yana mata wasa Aisha na kallonsa tana kara jin kaunar mijinta . yana son ya'yan da ta haifa masa ta kara amincewa aswad a tsaye take a ransa . dan wata rana sai kaga ya zubawa yarinyar ido , idanunshi suyi jawur yayi shr yace kai ta son yarinya ba lallai bane kuma idan wani ya aura ya kular maka daita . ya rufe idanunshi ya daga kansa sama Aisha ta kalleshi har yabata tausayi . mami ce ta samu Abdullah akan minal tace ita dai idan an yaye aswad a barmata ita . tana son yarinyar sosai shi kansa Abdullah ya gane hakan. dan duk mai son ya'yansa shima akan zuciyarsa yake. ya dade yana jinjina abin a ransa shima . ita kadai ce garesa mace ko fushi yayi yana ganinta zai huci . ya kasa cewa mami komai mami ta gane hakan ta nuna masa minal din ce ta dade tana mata naci ta rokar mata yarinyar a gurinsa. da har taki sai kuma taji tausayinta. tana son yara gashi ita Allah bai bata ba ..ta nemi a raba auran har Abdullah shima cewa yayi A'a gashi shima mijin adalilin haka bakaga yadda yake ji da minal din ba. ko yaya ta motsa yana kusa daita yana lallabata kuma sai abinda take so gashi dukiyar shima kmr watso masa ake. dole Abdullah ya amsa tunda shima ba rawa yayiwa Allah ya bashi ba. ,dan haka ya samu ummu affan da maganar ya dade yana fahimtar daita a karshe har ya nuna mata Allah ne ya kiyaye hade da taimakon minal lokacin da aka tisiyeshi sai ya saketa. da tuni saki uku ya rabuta " dan haka mama hafsa taso . minal ce ta dinga shawartarsa daya rubuta daya "Aisha ta amince da minal tasan zata kula da aswad tamkar yadda zatayi koma fiye da hakan. tunda ita kadai ce a gabanta tasan kuma yarinyar zata ji dadi kmr a gidan ubanta dan haka ta amince ta hakura . Ana gobe za'a cireta a no-no kuwa minal a gidan ta kwana washegari tun karfe goma suka shirya komai itama aswad tana ta murna zasu tafi unguwar tunda ta saba daita. ummu affan tana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46