Skip to content

Chapter 19

Chapter 19

Zuciyar Masoyi Book Two Complete Hausa Novels 1,165 words 0 views Progress saved
Download Book

maganin ya wuce jiya zuwa yau da rana. ban ji abinda faizar tace mata ba. Sai dai naji sun canza magana . dady yace na dauka labe kika tsaya yi musu yace dan bbu kyau musamman ma idan iyaye ne. tace A'A wlh yace to shikenan kuyi hakuri duk zan san abin yi in Allah yaso . komai zai gyaru kinji . Ta amsa ta tashi tana fita . dady ya rike gefen hakarkarinsa ya Kuma dafe kirjinsa. ya mike da kyar ya shiga bedroom dinsa ya zauna a gefen gado ya jawo durowa yana dudduba magungunansa . ya sha wani bai iya kai hannushi ya dauko ba dan haka ya hakura ya kwanta dan ya dan huta ya dafe kirjinsa sosai da yake bugawa . Abdullah kuwa yana fitowa daga part din dady salis ya tareshi "ga Dr sagir yazo yana nemansa "da hanzari ya karasa inda yake gabadaya ya rike hannuwan Dr sagir yana dariya. Wow Abdullah yi dariya cike da farinciki yau ranarka ce 😃😃😃😃😃😃😃😃😃😃😃😃😃 MMN SUDAIS CE [3/12, 3:02 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗 ZUCIYAR MASOYI 💖💖💖 💗💗💗💗💗 AISHA A BAGUDO Page 65 Gabadaya ya rike hannuwan Dr sagir yana dariya. yace doctor na taba gaya maka nayi mafarkin ni da Aisha muna tsakiyar macizai sun kewayemu" har wani me kyalli a cikinsu ya howa kaina ya sauka ya koma jikin Aisha daga nan na farka. sau uku ana gaya min wadannan macizan dana Gani ya'ya ne.. gashi nafara jin kamshin cikin sananin farinciki yace doctor doctor doctor Aisha ciki gareta tunda muka rabu ban sani ba. Dr sagir ya kalleshi da kyau yace friend waya gaya maka hakan? yace dady bai je min daurin auren faiza ba. sai yaje min bikon Aisha ya tarar ashe tana dauke da cikina . Gabadaya shima Dr sagir hannuwansa ya jawo suka rungume juna suna murna. Abdullah yace doctor kaima kana farinciki ko? Dr sagir ya kasa magana sai dai yarinka girgiza masa kai . sai da suka saki juna sannan Dr sagir ya sake miko hannu yace congrat... Abdullah yace thank you doctor muje nayi sallar isha'i ka rakani gurinta yanzu zanje "bazan bari na kwana ban ganta ba Dr sagir ya sake kallon. Sai Abdullah ya idar da sallah ne Dr sagir yace friend ka bari zuwa gobe mana ,sai aje da manya Abdullah yace in mutu kennan. Dr sagir yasa dariya yace baza ka mutu ba baban bby . Abdullah ya mike ai maganar manya takare nima yanzu babba ne tunda zan zama uba. Suka yi dariya ,Abdullah na kokarin fitowa Dr sagir yace are you serious friend zuwa zakayi . ko ka manta sakin Aisha kayi Abdullah ya dago da sauri ya kalleshi Dr sagir ya amsa masa da haka ne ,"sannan ya Kuma cewa tsawon watanni kun rabu ka barta da ciki baka nemeta ba sannan yanzu kaje mata karfe tara na dare nasan abune mawuyaci ta kalleka. idan da manya aciki sai a hadu a sulhunta. a sake sabon aure jikin Abdullah ya danyi sanyi Dr sagir yace wlh gara ka kwana yau kana addu'a Allah yasa ba tayi fushi da kai mai tsanani ba . ,kaga gobe sai ka lallaba kuje da dady ma zaifi. Har Dr sagir ya bar shi zuciyarsa natayi masa wasi wasi 'sau Tari idan wani abu na farinciki zai same shi sai garin ya daure masa" daga baya ya tsinke masa da alkhari. tsawon watanni da yayi cikin ukubar rashinta har zuwa yau din . daya zamanto inda zaije ya huta ma ya rasa a karshe gashi ya juye masa alkhari "zai zama uba nan da dan wani lokacin . dan haka yasan koyaje da kyar in zai ji ko yaga wani abu na bacin zuciya . dan haka ya murza sitiyarin motar sa shi kadai dan salis yariga yatashi daga aiki. Amman har yashiga lungun gidansu shi kadai a kafa "ya tuna da wani ido zai kalli mlm abu" sai yau yake zuwa garesu cak yaja ya tsaya ya kasa karasawa . gara zuwa da dadinsa zai fi har ya juya yaji yakasa tafiya ,nan yasamu jikin bango ya rabe" yana hango kofar gidan . yana tuna akwai kadararsa a ciki "yana nan tsaye har yayyenta guda biyu suka zo suka shige gidan . sannan ya hakura ya tafi duk da bai ganta ba Amman zuciyarsa ta masa dadi . Yau ko ba komai zaiyi kwanan farinciki . bayan yayi sallolin da ba zai iya kayyadewa ba . Karfe shida wayar dady ta sameshi yana jiransa Abdullah yaisa cikin bedroom dinsa ya sameshi har zuwa lokacin yana kan abun sallar sa . ,cikin farinciki kmr yadda yaga dady ya karasa ya gaisheshi "dady ya karasa jan carbi sannan ya amsa "ya nuna masa nan kusa dashi da hannushi. Abdullah ya matso ya zauna inda ya nuna masa cikin fara'a dady yace Abdullah Amman kayiwa Allah godeya da zai azurtaka da zuria ko Abdullah ya girgiza kai yana murmushi shima dadin dariya yayi . yace a to dan nima tun jiya nake godiya ga Allah zai kara mu zuria a cikin gidana . Abdullah baice komai ba illa murmushi daya sake. dady ya numfasa yace abinda yasa na nemeka tun yanzu nasan zakayi mamaki akan wannan Batun kuma ne yuwa zakaji wani bakon abu. wanda ba mamaki bazai maka dadi ba . kada ka taba sanya damuwa ko shakku a game da abinda ke jikin yarinyar nan Aisha . ni dai na amince tabbas cikin dake jikinta na cikin gidan ne. tun rabuwarku akwai wanda nayi waya na dora akan lamarin, to har likitan daya dubata na kwana uku da rabuwarku sai daya yayi min. bayanin adadin kwanakin cikin dake tare daita a jiya. dan haka komai maminka zata ce maka ka saurareta ne kawai ka amsa mata . Amman kar ka bari maganar ta tayi tasiri agunka . Abdullah ya daga kai dady yace Allah yayi muku albarka Amin Abdullah yakasa tashi daga gurin, dady ya fahimci yana son wani abu ne" yace uhm ina jinka da kyar Abdullah yace dady ita Aisha fa . Dady ya kalleshi ya sake murmushi yace wannan Kuma ai ya rage tsakaninku ni tunda ma naji zance cikin "ban kara dora komai akai ba . saboda har yanzu Aisha tana nan matsayin matarka . tunda saki daya ne akayi dan haka ko a yanzu kace ka mayar da ita ta mayu. tunda batayi Idda ba to auren ya mayu" Abdullah ya dinga yi masa kallon da gaske ?dady yacigaba abu daya ne nasan za'a samu yan tangarda wajen komarwata ko daga gun iyayenta ko ita kanta yarinyar . wannan ne abinda nake son komawa na samesu sai dai tsakanin yau da gobe ina gida bana son fita koina ,saboda akwai abinda zan Jira Amman ko a yau na samu yadda nake so zan iya zuwa na sake nemansu naji yadda za'a yi dan gaskiya dai a musu ba daidai ba . Abdullah ya dan yi murmushi jin dadi yace thank you my dad sannan ya tashi ya fita . Dady ya bishi da kallo shima yana murmushi fitowar Abdullah kuwa ya fadi ya mayar da Aisha yafi sau dari a fili da cikin zuciyarsa. Bayan kmr awa uku dady ya sake

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46