Skip to content

Chapter 9

Chapter 9

Zuriarmu Book One Complete Hausa Novels 1,388 words 0 views Progress saved
Download Book

yake kaiwa kowa koda ya shiga bureau d'in Doc A.Razak jikin shi yayi sanyi bayan sun gaisa ya mika mishi katin ya amsa yana karantawa da sauri ya d'ago kanshi yace wata Maimunar?? Manane.. sede kayi hakuri Allah yaya ma matarka bace ,๐Ÿ˜ณya Mike tsaye yana fad'in what?? !se kuma yakoma ya zauna yana fad'in kalmar INNA LILLAHI WA INNA ILAYHI RAJIOUNE yana ta maimaita wa har ya samu nutsuwa (haka ya kamata duk Musulmin kirki yayi idan musiba ta sameshi bawai yayi ta kuru ruwa da koke2 ba)yace Allah ya sanya alheiri ya kuma basu zaman lfy , yace Ameen2 kaima Allah ya baka wacce ta fita ,ameen nagode,yayi fice warshi(wayoo A. Razak mun tausaya maka muma๐Ÿ˜ž) Yau takama ranar jeudi (alhamis) kuma yaune akayi kamun amariya duda batayi kwaliya ba amman tayi kyau dan gyaran jikin da ake mata ya anshe ta ,wani tissu(matรฉriel) ne ta saka wandan Mom ce ta bada d'umkin riga da jupe(sket)ne se d'an mayafi data yafa sede fa idanunta sunyi jazir daga gani tasha kukanta ,shiko Doc Rid ko lek'o su beyi ba duda yasan al'adar *Zuri'ar* tasu dole ango ya halarci wurin kamun ,Mom tacika jiran shigawarshi kawai take dan duka wayoyinshi a Kashe suke ,beshigo ba se bayan magriba e kuwa Mom ta fad'a shi da fad'a ta inda ta shiga bata nan take Fita ba ,yayi ta bata hakuri daga baya kuma se ta fara mishi Nasiha kan biyyaya da rike zumunci ... Washe garin ranar bayan antashi daga sallar jumma'a ,dubunan jama'a ne suka sheda daurin auren *Ridwane Abdul Wahid Elh Fayรงal * Maimouna Mamandu Elh Fayรงal daurin auren daya tara manya2 mutanen garin dama matasa dan *Zuri'ar*tasu tayi suna cikin garin saboda had'in kansu ,mutuncin su kai dama abubuwa da yawa. Bayan daurin auren aka rankaya gidan Elh Fayรงal dan akwai walimar da za ayi.., Daga b'engaren Manane kuwa koda taji ana ta rangad'a gud'a se ta fashe da wani sabon kuka ,sambaby nata ta lallab'a ta tare da bata hakuri.. Se after magrib aka fara shirye2n zuwa paty ,da dafari yaso k'in zuwa amman daya tuno fad'an Mom na jiya se ya shirya ,iyata had'e fuska ,itama ana ta b'engaren k'in shirya wa tayi seda Umma ta bud'e mata wuta tana mata fad'a kamar zata doketa sannan ta csiga tayi wanka ta sa kaya ta zauna tasake dasa wani sabon kuka( hum har ruwan idonki ya k'are aurene de an Riga da an d'aura ๐Ÿ˜๐Ÿ˜›)Mom da Momy suka shigo sakamakon kiran da sambaby tayi musu dan fir tak'i a mata kwalliya,tsaka suka Sakata Momy ta fara mata nasiha me ratsa jiki daga baya Mom ma ta d'aura nata nahihar ,dan danan ta sauko har dasu dariya sakamakon wata rad'a da Mom tayi mata a kunne duk irin son jin gulmata amman banji mitace mata ba (shakuwar nan taku tana birgeni kamar ba sirikarta ba ...kodan *Zuri'ar*tasu cikin son junan su suka taso?muma de Allah ka bamu sirika irin wannan๐Ÿ™ˆ ameen) .Safara ta shigo ta bata wasu kaya tace wannan zaki sa ta amsa koda tasa su, habawa Samira da sauren y'an uwa ba abunda suke fad'i se tsarki ya tabbata ga Ubangiji Allah da ya hallice wannan kyakyawar hallitar dan wani tsaddenden farin lรจche ne tas dumkin dogawar Riga akamata sannan aka mata wani irin d'auri dankwali kamar gwagwaro da Jan yadi me silb'i, aka c'encad'a mata kwaliya sannan tasa Jan takalmi me tsini ga kuma yar karamar jaka ta hannu itama ja form d'inta 8(Coca-Cola Kenan)ta fito duk da yanzu ne suka fara ida futowa,dan haka seta yafa mayafi fari shima me ratsin ja ,duda ba dariya take ba amman ina ko makiyi ya kalleta se ya kuma kallo sannan ya yaba (koku kanku ku hango min farar mace cikin wanan chigar).. Dayake daga gurin patyn gidanta za akaita dan haka bayan an shiryata se aka kaita gidan Elh Faiรงal duka mutan *Zuri'ar*tasu sun hallara harshi uban gayyar (Rid),ya Adam ya Budรฉ taron da addu'a , sannan Elh Fayรงal yayi Bismillah ya fara ma *Zuri'ar*nasiha da kan zaman takewar aure da hakk'okin miji akan matarshi da kuma na mata akan mijinta yaci gaba da cewa ita mace ABOKIYAR RAYUWA ce mai rauni ce, ka fita hankali, ka fita karfi, ka kuma fita hangen nesa, kenan ya kamata ka dauke ta a matsayin abokiyar ka wacce zaka tallafa mata ka agaza mata, da kuma yin hakuri da ita a in da ta gaza, domin ita tamkar kashin hakarkari take. Kamar yanda yazo a cikin Muslim: ูˆ ููŠ ุฑูˆุงูŠุฉู ู„ู…ุณู„ู… ุนูŽู†ู’ ุฃูŽุจููŠ ู‡ูุฑูŽูŠู’ุฑูŽุฉูŽ ู‚ูŽุงู„ูŽ: ู‚ูŽุงู„ูŽ ุฑูŽุณููˆู„ู ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ู ุตูŽู„ู‘ูŽู‰ ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ู ุนูŽู„ูŽูŠู’ู‡ู ูˆูŽุณูŽู„ู‘ูŽู…ูŽ: (( ุฅูู†ู‘ูŽ ุงู„ู’ู…ูŽุฑู’ุฃูŽุฉูŽ ุฎูู„ูู‚ูŽุชู’ ู…ูู†ู’ ุถูู„ูŽุนู ู„ูŽู†ู’ ุชูŽุณู’ุชูŽู‚ููŠู…ูŽ ู„ูŽูƒูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุทูŽุฑููŠู‚ูŽุฉูุŒ ููŽุฅูู†ู’ ุงุณู’ุชูŽู…ู’ุชูŽุนู’ุชูŽ ุจูู‡ูŽุง ุงุณู’ุชูŽู…ู’ุชูŽุนู’ุชูŽ ุจูู‡ูŽุง ูˆูŽุจูู‡ูŽุง ุนููˆูŽุฌูŒุŒ ูˆูŽุฅูู†ู’ ุฐูŽู‡ูŽุจู’ุชูŽ ุชูู‚ููŠู…ูู‡ูŽุง ูƒูŽุณูŽุฑู’ุชูŽู‡ูŽุง ูˆูŽูƒูŽุณู’ุฑูู‡ูŽุง ุทูŽู„ูŽุงู‚ูู‡ูŽุง )) Manzon Allah (SAW) yace: "Lallai mace An halicce ta ne daga kashin hakarkarin (Adam) ba ta iya daidaituwa gare ka a hanya, idan zaka ji dadin ta, to ka ji dadin da ita a karkace, idan ka ta fi don mikar da ita, to za ka karya ta, kuma karyewan ta shine Sakinta". [Muslim]. Kenan sai an yi hakuri da juna, sai ana yi ana kawar da kai, saboda shi rayuwar aure dukkan sa hakuri ne, kuma Duk wanda zayyi aure haka zaka ji ana yawan ambata masa cewa kayi hakuri, se fa kunyi hakuri da juna a rinka yiwa juna uzuri, sannan ku rinka kyautata zamantakewar ku . Domin Manzon Allah (SAW) yace : ุนู† ุนุงุฆุดุฉ ู‚ุงู„ุช: ู‚ุงู„ ุฑุณูˆู„ ุงู„ู„ู‡ ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู… ุฎูŠุฑูƒู… ุฎูŠุฑูƒู… ู„ุฃู‡ู„ู‡ุŒ ูˆ ุงู†ุง ุฎูŠุฑ ู„ุฃู‡ู„ูŠ. [ุฑูˆุง ุงู„ุชุฑู…ุฐูŠ] Mafi alkhairin ku shine wanda yafi alkhairi ga iyalin sa, sai yace ni nafi ku alkhairi ga iyalaina." [Tirmiziy]. ุนูŽู†ู’ ุฃูŽุจููŠ ู‡ูุฑูŽูŠู’ุฑูŽุฉูŽ ุฑูŽุถููŠูŽ ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ู ุนูŽู†ู’ู‡ู ู‚ูŽุงู„ูŽ: ู‚ูŽุงู„ูŽ ุฑูŽุณููˆู„ู ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ู ุตูŽู„ู‘ูŽู‰ ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ู ุนูŽู„ูŽูŠู’ู‡ู ูˆูŽุณูŽู„ู‘ูŽู…ูŽ: (( ุงุณู’ุชูŽูˆู’ุตููˆุง ุจูุงู„ู†ู‘ูุณูŽุงุกูุŒ ููŽุฅูู†ู‘ูŽ ุงู„ู’ู…ูŽุฑู’ุฃูŽุฉูŽ ุฎูู„ูู‚ูŽุชู’ ู…ูู†ู’ ุถูู„ูŽุนูุŒ ูˆูŽุฅูู†ู‘ูŽ ุฃูŽุนู’ูˆูŽุฌูŽ ุดูŽูŠู’ุกู ูููŠ ุงู„ุถู‘ูู„ูŽุนู ุฃูŽุนู’ู„ูŽุงู‡ูุŒ ููŽุฅูู†ู’ ุฐูŽู‡ูŽุจู’ุชูŽ ุชูู‚ููŠู…ูู‡ู ูƒูŽุณูŽุฑู’ุชูŽู‡ูุŒ ูˆูŽุฅูู†ู’ ุชูŽุฑูŽูƒู’ุชูŽู‡ู ู„ูŽู…ู’ ูŠูŽุฒูŽู„ู’ ุฃูŽุนู’ูˆูŽุฌูŽุŒ ููŽุงุณู’ุชูŽูˆู’ุตููˆุง ุจูุงู„ู†ู‘ูุณูŽุงุกู )) [ุงู„ุจุฎุงุฑูŠ]. A wani hadisin kuma yace: "... Ku kyautata zama da matan aure, saboda lallai ita mace an halicce ta ne daga kashin hakarkari, Kuma lallai abin da ya fi karkata daga hakarkari shine kashin samansa (hakarkari), idan ka tafi domin ka mike dashi zaka karya shi, idan kuma ka barshi ba zai gushe ba yana a karkace, to ina muku wasiyya da kyautatawa ga matan aure." [Bukhari]. Kyautatawa yana sawa aboki ya so abokin sa, yaron gida yaso shugaban sa, kuma uba yaso dansa, haka nan ma kyautatawa yana sa mace ta so mijin ta. Elh yaci gaba da fad'in Duk namijin da ke son ya zauna lafiya da iyalan sa dole ne ya sauke hakkin iyalin sa kuma ya koyi kyautata musu. Saboda kyautatawa yana sanya soyayya a tsakanin mutane. Haka nan sai ka ga mutane suna son ka don kyautatawar ka, to ita ma haka iyalinka zata so ka kuma ta rinqa alfahari da kai. Haka de yaci gaba da nasiha bayan ya gama Dad,Abba,Dady suma sukayi tasu nasihar tare da Jan kunne , ita de Manane babu abunda take se kuka,shima Rid jikin shi du' Yayi sanyi,akayi addua'a tare da fatan alkhairi ga ma'auratan sannan aka fara shiryen2 tafiya patyn dan 21h za a fara..cikin iyayen Mom da Momy ne kawai suka halarci patyn.. Koda

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41