Chapter 33
Chapter 33
yasa yakejin dangin nashi na bashi wani irin haushi da takaici kamar ya kashe su(mu ko muka ce Rid bawon Allah ba laifin ka bane na aljaniπΉ dan k'undalo ne da wanan shegiyar matar ka mai kan angulu inji Manane baπ) Dede stair ya hango Halima a zaune tayi dirshan ko motsi bata iya yi ballΓ© ta tashi . Ko kallo bata isheshi ba ya fice d'akinshi wanka yayo yabi lafiyar gado dan yanzu baya ba sallah ma mahin manci Kay Halima kin cuci bawan Allah nan mutumin da baya wasa da addini amman yanzu ko sallah baya cikawa Kai mata muji tsoran Allah mu dinga tuna da akwai ranar da zamu tsaya gaba ubangijin mu kuma ze tambayye mu duk abunda muka aikata ..ranar da baki baze yi magana ba sede gab'ob'i.. Allah ya k'ara kare mu daga sharrin masu sharrin..ya kuma K'ara shiryar damu..ameen(juste un tout petit rappel) Ganin ba shi da alamun taimaka mata yasa tayi k'okarin hawa stair d'in da rarafe a ranta fad'i take dole ma na koma wurin Boka ya had'on na mallaka... Kawarta ta ma tayi fice warta dan ita bata ji wani rauni ba se dukan datasha..ta sawa Halima Allah ya isa yafi cikin kwando.... Washe gari dede wajejen karfe goma na safe su Papy suka sallamo gidan Rid Sunyi sallama amma shiru ba'a amsa musu ba abun bai basu mamaki ba dan Mom ta rigayi da ta fad'a musu irin cin mutuncin da sukayi mata kwanakin baya.. direct palo Papy ya huce ganin bakowa yasashi fara kwallawa Ridwan kira wanda shi kuma yana baccin shi abunshi hankali kwance.... Halima kuwa tun safe ta fice hospital daga can ma gidan su zata fice.... cikin bacci yaji kaman ana kiran sunan shi firgit ya farka ran nan a b'ace fuskar nan a murtike ya nufi palon cike da masifa yake cewa way waye yake damun mutane da sa ssafen nan .. Ganin wanda yayi ne yasakashi jan wani mahaukacin tsaki ya Juya da sauri zai koma.. sai kawai papy yayi mishi wata gigitacciyar tsawa wanda sai da tasa jikin shi b'ari dan tunda ya taso bai taba ganin baccin ran Papy irin nayau Jiki a sanyaye ya tsaya yana musu kalon raini .. amma aranshi yana san basu hakuri kawa ji yayi bakinshi yayi nauyi kamar kullum.. Komo ka zauna ma mutane Papy yace(uhmm tsofo mai ran karfe ba) Yana gunguni ya dawo ya zauna ba dan yaso ba.... To fans ku biyo mu dan jin yanda zata kaya mune naku har kullum ... Fasma&AΓ―cha [14/2 06:26]πππͺπ¨βπ©βπ§βπ¦π¨βπ§βπ¦ *Zuri'ar* *mu* ( *Notre* *Famille* ) π¨βπ©βπ§π¨βπ©βπ§βπ§π©βπ§βπ¦ππ Story&written by π³πͺ ~AΓ―cha~ and ~Fasma~ π³πͺ _Dedicated_ _by_ _Ramatou_ 140__145 ```Manzon Allah (SAW) ya ce:''ka sanya idonka a wurin sujadarka'' Dailami ne ya rawaito shi ``` Badan yaso ba ya zauna..se hararen Papy yake. Ganin su ya Adam Sun shigo ya tashi zum'bur yayi tseye ya nufi hanyar rooms dinshi. Da zafin nama Adam da Haider suka kamoshi, Malamin me suna malam Zaneidu yace ku zaunar dashi a tsakiyar falon.. shikam se faman tirge2 yake. Da karfi tsiya suka zaunar dashi, ruwan addu'a papy ya shafa masa da farko wanda ya sanyashi daina tirge2 dayake, nan aka fara masa rukiyya .... Tin yana ihu harya fara fad'in ku dena bana so, amma duk da hakan basu dena ba sukaci gaba. Bayan wani dan lokaci yace ku tsaya zamuyi magana, malamin be tsayar da karatun dayake ba.. Sosai Ridwane yake ihu yace ku tsaya zamu fita kuna konamu, se a lokaci suka tsayar da karatun, malamin yace muna sauraranka fad'i muna yanda a kayi ka shigeshi ? Kamar bazeyi magana ba sekuma yafara magana dagaji kasan ba maganar Rid bace yace " ni sunana dan kundalo ..Boka gobe da nisa ya turoni danna rabashi,nashiga tsaninshi da *Zuria 'ar* sa, ganin yafi karfina bazan iya shiga jikin shiba yasa na tattaro yarana kimanin su ishirin,yanzu haka dayawa daga cikinsu sun mutu wasu kuma kun karera yamun su.." Malamin yace yanzu zaku fita ?.... Ya kyale beyi magana ba Ya sake cewa Zaku fita ko bazaku fita ba ? Namma shuru Ganin haka yasa yaci gaba da karatu. Ganin suna kokarin kasheshi ne yasa yace kuyi hakuri zan fita kuna konani. Zaku kasheni.. Ya tsayar da karatun yace naji zan kyaleka ka fita Amma da sharadin kayi alkawali bazaka sake komo waba koda an turoka ,kuma bazaka sake shiga jikin musulmi gaba daya. Yace na dauka, na amince. Wata atishawa ce yayi seya fadi summame nan wurin ,papy yace Alhamdulillahi....su Adam suka daukeshi zuwa dakinshi. Kafin su dawo malamin ya bada wasu maganinnika kamasu zam-zam,habbatus sau da..dade sauransu..wasu na yasha wasu kuma yayi wanka...da yardar Allah duk wani sihiri na jikin shi ze karye ... Allah de yasa mu dace..ameen Se wajejen karfe daya na rana ya farka da salati a bakinshi, ya jima nan zaune bisa gadon nan wasu abubuwan da suka faru suke zuwan mishi, kawai seya fashe da kuka,tuna irin abunda ya dinga yima *Zuri' ar* tashi... Jin Kukanshi yasa su ya Adam shiga dakin.. da gudu, ya rukum kumesu yana wani irin kuka me cin rai. Cike da jin dadin d'an uwansu ya samu lfy suka Kamoshi zuwa nan falon inda yaga duka mazan **Zuri'ar* wato su Abba ..etc , da gudu yaje gaban papy ya rumgumeshi yana kuka yana neman gafara, nan ya dinga rarafawa yana neman su yafe masa daya bayan daya. ... papy yayi mishi nasiha sanan yace ya rike addu 'a domin itace garkuwar mumuni. . Kiran sallah da akayi ne yasasu tashi, shikuwa d'aki ya koma ya watso ruwa tare da d'auro alwala ya bisu masjid.. Bayan sun gama ya biyo Abba dan yasan ko karan hauka ya cijeshi bazeje gidan Mom ba shi kade.. Lokacin daya shigo tana waya, tana ganinshi ta saki wayar ta fadi kasa ta mike tsaye tace Son kaine ko kuma idanuna ne kemin gizo ??? Da gudu kamar karamin yayo ya shige jikinta yace Umma nine nanfa ya dinga neman gafarata... Sanin bayin kanshi bane yasa tace bakomi Allah ya kara karewa kuma tayi mishi nasiya akan rike addu'a da kuma karatun Alqur 'ani me girma. Se lokacin ta kare mishi kalo duk ya rame yayi wani baki,,, bata yi wata2 ba ta kamoshi zuwa dining, sosai kuwa yaci abincin. Daganan ma gidan Momy ya fice itama ya bata hakuri, nan ya gamu da Haider ya rokeshi kan ya tayashi ba Mom hakuri .. Koda suka shigo tana falo tana kalon TV, kallo daya ta musu taci gaba da kallonta Bayan su zauna sun gaisheta a daddakile ta amsa ,shurune ya biyo baya.. Ridwane yace Mom dan..... , hannu ta d'aga masa tace dakata karka ma soma ? Nanfa ya tsure se da Haider ya shiga bata hakuri ta d'an fara sakin fuska, Kusa da ita ya dawo ya dnaura kanshi da hannushi bisa cinyarta ya shiga reramata kuka yana bata hakuri tare da neman ta yafe masa. Har cikin ranta taji dadi ta kuma gidewa Allah,ta d'aura hannunta saman kanshi tana mishi nasiha tare da addu 'a Allah ya kara karewa daga sharrin masu sharri. Dama tsakanin d'a da uwa se Allah Suna tsaka da haka Manane ta shigo, ganin Rid yasa tayi turus sekuma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41