Skip to content

Chapter 30

Chapter 30

Zuriarmu Book One Complete Hausa Novels 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

Docteur Rid muna tayaku jimami kuma yana barar ada'arku. Munabawa masoyan Salma hakuri na kasheta da mukayi dan akwai abunda muka hango muku nan gaba. On vous aime tous and thanks for your support ana mugun tare Muna neman afuwar ku na rashin jimmu kwana biyu da kukayiπŸ™πŸ™πŸ™ .😘❀😍 Fasma & AΓ―cha [5/2 22:30]πŸ’“πŸ’žπŸ‘ͺπŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦πŸ‘¨β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *Zuri'ar* *mu* ( *Notre* *Famille* ) πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦πŸ’•πŸ’ž Story&written by πŸ‡³πŸ‡ͺ ~AΓ―cha~ and ~Fasma~ πŸ‡³πŸ‡ͺ *Wannan page d'in nakune yan Zuri'armu Novel Fans* nous vous aimons tous irin sosai din nan😍❀😘 _Dedicated_ _by_ _Ramatou_ 125__130 ```Manzon Allah (SAW) ya ce:''Duk wanda ba ya tausayin mutane to shi ma Allah ba zai yi masa rahama ba'' Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi``` Bayan awa guda ya farfad'o daga suman da yayi amma har lokacin ciwon kan bai barshi ba se ma abunda ya k'aru dan haka ya tatara kayan shi yakoma gida .... Direct dakinshi yashige ya kwanta dan wani irin mugun headache yake damunshi yana juye2 har wani b'arawon bacci ya kwasheshi cike da mafarkai barkatai marasa digi... Suna tsaka da lecture gabanta yayi wani irin mummunan fad'uwa wanda sai da ta dafe kirjinta tana fadin innalilahi .... tundaga lokacin cours d'in ya fita ranta ''et elle n'a qu'une seule envie c'est de retourner at home.'' Ana basu break ta dawo gida kwatsam taci karo da motarshi a farfajiyar gidan a ranta tace lafiya yaya ya dawo a wannan lokacin? Da sassarfa ta karasa ciki a dakinshi ta ganshi yayi ruf da ciki yana bacci sai bata tayar dashi ba kuma bata kawo komi a ranta ba kawai tashiga kitchen ta d'ora musu lunch.... har time d'in komawarta school yayi amma bai tashiba abun ya bata mamaki sai ta nufi d'akin dan tayar da shi dan tana tammahanin ko sallah azahar beyi ba . Kafarshi ta d'an bubuga tace yaya tashi mana bacci ya isa haka har fa....... Katse ta yayi dawata tsawa da ta gigitar da ita yace uban wa yabaki izinin shigo min d'aki har da zaki tayar da ni ina bacci idon nan nashi jajur seda ta tsorata taja da baya har b'ari take bakinta na karkarwa tace loka..cin..sallah..ne fa y...... Kanta gama ya d'auketa da wani wawan mari sai da ta zube kasa yace kin fini sanin lokacin sallah yayi ko da ke kike sakani nayi ne sha3 kawai b'ace da gani kafin na tashi na tattakaki... Yakoma yaci gaba da baccin shi Sum sum ta tashi ta fice .. dakinta takoma ta kwanta tana kuka kasa2 gami da dafe wurin marin dan har sawun yatsun shi sun fito. A ranta tace mike damun yaya yau?mike faruwa dani? Ko gidan Papy basu tafi ba dan shi gogan tun biyar na yamma da ya fita bai dawo gidan ba har yanzu dayake goma na dare ita kuwa Manane shatin din hannunshi ne ya hanata zuwa dan bata son tambayoyi Koda Momy ta kirayeta se tace ee batajin dadin jikinta ne shiyasa. Two days later Yau ma kamar kullum da marmarin dambu Manane ta tashi dayake suna cikin holiday dan haka se tashiga kitchen dambun shinkafa tayi wanda yasha nik'ekken nama rago da d'an jajab'ar vinaigrette d'inshi yasha yajin nanπŸ˜‹ ta jere musu nasu a dining table dan ita tun a kitchen ta ci nata because yanzu batacin a dining saboda irin wulakanci da cin zarafin da Rid ke mata inhar tare zasu ci.. Bayan wasu yan mintina shi da Halima suna tsaka da ci suna hira yayi wata dariya abunka ga dambu sai kawai ya sarke shi tun yana tari ahankali har ya sauko da kan kujerar dining din yafara amai .kamar ze amayar da hanjin cikin shi.... Dede lokacin Manane ta sauko daukan juice a frige da glass a hannunta gani halin da yake cike da sauri ta iso gabanshi ganin yana amai ga Halima da ko aka bata kowa ba dan cigaba ma tayi da cin dambunta. Dafa shi tayi tace sannun yaya ... Hankad'a ta yayi seda ta fad'i glass d'in hannunta ya fashe ya yanketa a hannu jini ya fara zuba.. Tashi yayi cike da masifa idanun nan jajur duk su fito waje yace kada ki tab'ani shegiya mayya zaki kasheni. Cike da takaici tace yo ni mi nayima ne? Nufota yafarayi yace dan ubanki waya dafa dambun inba keba gashinan ya shakeni yana famar kasheni muguwa kawai.. A dede lokacin taji Halima ta sheke da wata karuwar dariya har tana fad'uwa k'asa tana rike ciki dan k'eta.. A fusace tace ga mayya can me kama da jab'a kusan ka.... Kuma ka tabatar da cewa in ni mayya ce kaima maye ne dan daga tsatso daya muka fito ehe.. Kuma daga yau ku rubuta ku aje bazan sake taimaka in dafa muku abinci ba sai day waccar banzar me kan angulun idan har ta iya ta dafa ..... Ganin yana zare belt d'inshi... ee kowa tace k'afa mi naci ban baki ba ta kuwa tattare sket ta arta da gudu dakinta ta danna wa kofar key. Biyota yayi ganin ta rufe k'ofar yasa ya fara dukan k'ofar da iya k'arfin shi yace wly Manane ki bude kofar nan dan idan na shigo jikin ki zai gaya miki. Bakinta bai mutu ba tana daga d'akin tace wly bazan bude ba angaya maka ni baiwar kace da zan bari ka dakeni ne...? Yajima nan tsaye daga baya ya ficewarshi ganin batada niyyar budewa. Box tad'oko tayi treatment din hannunta tana kuka marar sauti tace wannan masifar da mitayi kama?kwata2 ya Rid ya canza gashi yanzu ko gidan papy yin diner ma ya dena zuwa ....gidan su Umma ma baya zuwa yanzu ..hannu ta d'aga tana rok'on Allah ya kawo musu saukin abun nan... A bangaren Halima kuwa sosai taji dad'in ganin abunda Rid yayi wa Manane har da taka rawa tayi tace kadan ma kika gani ai ni wly ko na malakar beyi tasiri akan shibaaikin aljanin nan ma ya isheni.....sosai taji dadin scΓ¨ne d'in nan... ,(Allah ya k'ara shiryar damu..ameen) *** ** ** bari mu lek'o bangaren su Umma ... Sosai suke kula da khalifa bama kar Yesmine da Muhsana ba irin riritashi da suke kamar kwai shi ma kuma yaron har ya gane su dan kuwa ko muryarsu yaji to fa ya fara duben2 nemansu inkuwa ya gansu se sun daukeshi inba hakaba se yasaka musu kuka har se sun dauke shi..ko school zasu tafi se da dubara...... A b'a'garen Haider kuwa ya fara zuwa clinique dan ganin irin kulawar da khalifa ke samu gashi kuma yanzu Rid se yaga dama yake zuwa dan haka duka responsability clinique din ya dawo hannunshi..duk da shi kanshi yaga irin sauyawar da Rid yayi... ** ** * Kwanci tashi ba wuya lokaci nata tafiya su Manane na aji na biyu a shool of midwifery. ..sambaby na dauke da d'an karamin cikinta.... Halima kuwa har tagama karatunta result kawai suke jira... Su Yesmin kuwa suna ss2 sun k'ara girma dan yanzu shekarun su goma sha biyar....shakuwarta kuwa tsakaninta da khalifa se abunda ya k'aru..sosai.take bashi kulawa.... Doc Rid kuwa duk yabi ya lalace har wani baki na wuya yayi dan Halima juyashi take son ranta ga kuma shiga tsakanin shi da aljani yayi da Zuri'ar tashi kwata 2 ya yanke duk wata mu'amalarshi

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41