Skip to content

Chapter 32

Chapter 32

Zuriarmu Book One Complete Hausa Novels 1,196 words 0 views Progress saved
Download Book

canza izuwa wando da riga aranta tace zaku ci ubanku yau Wata sharbebiyar waya ta dauko kitchen ta fice ta dauko oil tazo dede bakin kofar fita palon ta zuba oil din ta koma ta zuba a bakin upstair. ... Sukuwa sai surfa d'umi suke basu ma lura da abinda takeyi ba se kawai jin saukar bulala a jikinsu sukayi.. Tashi sukayi da niyyar kai mata hari tayi wani super juyi ta sake lalabta musu da iya k'arfinta da sauri Halima tayi hanyar stair dan dauko itama mabugi sai ihunta kawai sukaji ta fad'i kasatana fadin wayo k'afata ta karye. Manane ko dama kamar jira take ta dunga zulamata bulalar bataji bata gani kamar wanda wani ya aikota .. Halima ko ihu take tana fadin Hajjo kizo ki taimakeni man ko sai ta kasheni.. budar bakinta tace haba inzo a gama da ni ai wly nayi nan Taje kofar fita palon aiko itama tayi slip ta zube nan Manane ko mizatayi inba dariya ba da sasarfa ta iso wurin tafara dukanta itama sai ihu take Suna tsaka da haka Rid ya turo kofar palon Ganin abun da Manane keyi ne yasa ya daka mata tsawa.. amman tayi kunnan uwar shegu da shi ta cigaba da abun da takeyi Fizge wayar yayi yace bakyaji ana miki magana ne.. tace ni kaba bulala ta ..anki abayar d'in Nan fa ta rufe ido ta dunga massifa saukar bulalar da tajine yasa tayi shiru ta bude ido kafin tayi wata2 yasake zabgamata guda ai ko tace kafa minaci ban baki ba... Ta kofar baya tabi ta gudu se gidan Mom Shima mizaiyi inba bintaba ya kuwa rufa mata baya..... Ku biyo mu danjin yanda zata kaya.... *Kuyi hakuri da jin mu shiru kwana biyu muna buzy ne...* Love you all 😍❀😘 Fasma&AΓ―cha [11/2 02:07πŸ’“πŸ’žπŸ‘ͺπŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦πŸ‘¨β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *Zuri'ar* *mu* ( *Notre* *Famille* ) πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦πŸ’•πŸ’ž Story&written by πŸ‡³πŸ‡ͺ ~AΓ―cha~ and ~Fasma~ πŸ‡³πŸ‡ͺ _Dedicated_ _by_ _Ramatou_ *Wannan page din nakune fans na Zuri'ar mu ...muna godiya da irin so da kaunar da kuke nuna muna da wanda muka sani da wanda ma bamu sani ba..Allah ya bar kauna ya kara donkon zumunci...love you all irin totaly din nan* 😍😘❀ 135__140 ```Manzon Allah (SAW) ya ce:''Lallai Allah ta'ala ya haramta wa wuta cin naman wanda ya fad'i ''La'ilaha illallahou''don Allah'' Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi..``` Gidan Mom ta shiga da gudu tana fad'in wayyo Allah zai kasheni.. Momy , Mom da Haidar ne a falon da sauri suka mike suna cewa waye zai kashekin? Duk hankalin su ya tashi.. Kafin tayi wani kwakkwaran motsi ta sanar musu Rid ya fad'o d'akin kamar wani mayun wacin zaki sai huci yake ya dunfaro zai damk'eta da sauri ta zille ta koma bayan Haidar... su Momy na mishi magana amman yayi kunen uwar shegu da su burinshi kawai ya damk'eta da sauri Haidar ya fizge bulalar yana fad'in miye ya sameka wai ..a na maka magana kawani yi banza da mutane Wata harara ya gallamasa yace to ku miye ruwanku a ciki idan ma kasheta nayi.. ba matata ba ce ba .... Mom tayi saurin cewa la la la la... zancen kisa ma be taso ba Ke zo nan maza ma kki fice d'aki.. kamar jira take da sauri ta kama hanyar har tuntub'e take ..... d'aga murya yayi yace walahi in ki shiga d'akin nan kada ki kuskura ki dawomun gida inba haka ba se na b'abb'alaki........ Cak ta tsaya ta kasa gaba ta kasa baya ...se Wani kukan daya sake kubce mata ..... ganin haka ya sa Mom fad'in ka kwantar da hankalin ka baza ma ta sake komawa ba bare ka kashemin ita... Fuuu ya fice daga gidann.yana fad'in da ya fiye mata.. Manane kuwa palon ta dawo taci gaba da rera kukanta... su Mom se rarrashinta suke ..da kyar ta tsagayta tace nifa Momy ba kukan dukan da yayi min ne nake ba illa kukann...se kuma tayi shiru.... Momy tace yi magana mana ..... Share hawayenta tayi tace ina bukak'atar meeting din gaggawa na *Zuri'ar mu*.... Mamaki kwance a fuskokin su ..suke kallonta........ta fice d'aki tana sharar kwalla Tun lokacin Haider ya fara kira yana sanar musu biyar 5 na yamma akwai meeting gidan Papy.......... Duk wanda ya sanarma se yayi mamaki ..dan haka kafin biyar din ma kowa ya iso.. Zazaune suke ansaka manane tsakiya kowa yana jiran jin abunda yasa ta buk'aci meeting.. nan fa Manane ta fara zayyana musu duka abunda taji ta kuma sani.tun waccan lokacin da kuma abunda ya faru d'azu.. gaba daya palon ya dauki Salati aka fara dikkira suna salamce wa....kowa yayi mamakin wanna abu.....nan fa kowa yafara fadin albarkacin bakin shi palon ya hargitse da hayaniya.. .. Papy yayi gyaran murya se kowa yayi shiru dan jin abunda d'an tsofo ze fad'a... Yace duk ku kwantar da hankalin ku da yardar Allah ze rabu dasu da karfin addu'a dana Alqur'ani me girma .. Ya ce ai bamuga ta zama ba .. Nan fa ya yanke shawara tun gobe za'a fara yimishi rukya kamar yanda addini ya koyar tare da wani malami na Medical Islamic Herbe .. Mom ta ce amman fa Manane bazata koma gidan bah har sai Rid ya medo hankalinshi. Ya dawo normal dan tana tsoron ya illata mata y'a.. Babu wanda ya musa mata Se gab da sallar magarib taron ya tashi kowa yawatse cike da jimamin wanna al'amari..da kuma shirin goben . . Bayan sun dawo gida direct d'aki Manane ta shige jiki ba kwari watso ruwa tayi tare da d'auro Alwala tayi sallah magrib sannan ta shiga jero nafil fili bayan ta kare tabi lafiyar gado tana saka ta na war warewa ..har aka kira isha'i tayi ta koma ta kwanta dan bata jin zata ma iya komawa gidan papy yin diner.. Karar wayar ta ne ya medota da ga duniyar tunanin da ta tafi da har baza ta d'aga ba amma ganin name din Sambaby se ta d'aga tana fadin Hello sam ykk#? Bayan sun d'an gaisa. Sam tace yana ji muryarki wani iri? Kuma ya akayi baki dawo school ba ....?Allah yasoki bema kar..bata gama fad'a ba taji Manane ta fashe da wani irin marayen kuka... Gaba d'aya hankalinta yafara tashi jitake kamar tayi fuffuke tazo ..dole ta fara rarrashi.. Ita kuma Manane tuna sambaby nada cike yasata yin shiru sanan ta bata labarin duk abinda taji da kuma gani ..da kuma shawarar dasu papy suka yanke Salati tayi tace aie nasan dama za a rina RUWa BAYa tsami banza... Nan ta shiga yi mata nasiha tace yanzu hakuri zakiyi tunda da dey su Umma sun san komi kuma ki k'ara kai kukan ki ga Allah. Ki rage baccin dare ..ki zanki rayashi da nafil fili da addu'a insha Allahu za'a dace a haka tayi ta fad'a mata kallamai masu sanyaya rai da bata karfin guiwa(Allah sarki Manane kinyi sa'ar kawa ta kirki muma Allah kabamu irinsu ka kuma kare mu da irun kawaye kamar su Halima...ameen) : Sun jima suna hira sanan sukayi sallama. Bari mu le'ko 'bangaren su Halima .... A fusace ya shigo gidan yana huci amman har ga Allah a ranshi bai san dan mi yayi wa Manane haka ba kay gaba daya ma be san dalilin da

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41